Chapter 1: The Beginning

3.6K 183 6
                                    


Alhamdulillah for bringing us to see this day as Our New story will begin thank you all for following me, comments and Votes.

Don't forget to add this story to your Library so that whenever it's updated you will receive alarm for you to read,
Inafata ba zaku manta cigaba da bada comments da votes dinku ba Nagode yadda muka fara a sa'a Allah yasa muka re a sa'a Ameen.
    

🅿️01

Kwance nake Ina juyi kan gadona dake can sama yayinda idona keta kakkarwa ina mammatse jikina
Wani irin iska nake Ji Wanda Ina iya Jin karar ta sosai a wannan lokacin idona kuwa rufe yake very tight.

A hankali nadan cire blanket din dana rufe jikina har kai na dan bude idannuna
Closing din eye din nawa nakuma da sauri dan gani nake kamar Ina ganin wata mata zaune da white cloth jikinta.

Fara Jin tafiya nayi kamar ana nufo kwanar da nake kwance nan jikina yakara fara kadawa nakara matsewa ga wani irin
Shuuuuuuuuuuu da nake Ji duka a lokaci guda Ji nayi takun kafar ya dauke inda na shiga Jin kukan mage a hankali bayan nasan Sam bamu da kuliya agidan.

Addu'a na soma duk wacce tazo bakina Sam bana iya gane abunda nake fada dan ba karasa wata nake fara wata kona har hada,
Tsawa naji tayi wani irin Kara take wani haske nagani na walkiya tuni naji fitsari na shirin zuwa mun na bude idona sake ganin wannan matar nayi hakan yasa
Na sauko da gudu daga kan gadon Ina ihu sosai,
Da sauri naji anriko ni hakan yasa ihuna ya karu sosai.

"Naila! Naila!! Meye!".

Sam bansan me take fada ba shigowar momy ne da sauri ta kunna light din dakin hakan yasa na iya ganinsu zaunar dani ya Nafy tayi.
" meya faru!"
Momy Tafada tana kallona cire earpiece din dake kunnena tayi Wanda Sam na manta dashi
Tana kallona sunkui dakai nayi inakallon kasa
" Nafy jeki kawo mata ruwa tasha" tashi ya tayi Tana kallonta.

" how many time nace kidaina kwanciya da earpiece infact I have forbidden you didn't I".

Daga kaina nayi na kada duk nagana yin zufa jikina banda rawa ba abunda yake mun,
" kinyi Magrib"
Girgiza kai nayi alamun banyi ba harara ta tayi nayi kasa da kaina,
" isha'i fa!"
Nan ma nodding din kaina nayi kai hannu tayi ganin dundu me shegen zafi.

" kuma momy walh saida nace tayi Sallah infact na kwace memory din bansan yadda akayi ta dauko shi ba".

Tafada tana mika mun ruwan karba nayi nasha na ajiye cup din,
" Go back to sleep we will discuss this tomorrow is late now",
Tashi momy tayi tabarmu agun saida kashe light din tayi dai2 sanda na kuma Jin walkiya.

Tashi nayi da gudu na nufi ya nafy " ke lafiyarki kuwa kiwuce ki kwanta"
Rike ta nayi da karfi " please ya kiyi hakuri mukwana tare"
Murmushi tayi me sauti tare da janyoni "sai tsoro ga rashin Ji oya get in" hawa nayi can karshe shima saida na tabbatar Ina rike da ita kafin na rufe ido cikin ikon Allah naji shaaaaa ruwa ya sauka,
Wani irin dadi naji da ni'ima naja bargon sai bacci.

"Naila! Naila!! Naila!!!"

Kamar a mafarki naji ya nakira na a wannan lokacin bacci na yayi dadi banson abunda zai katse shi,
Jan pillo din nayi natura kaina ciki tare da squeezing face dina saboda tabani ya take
Kara matse eyes dina nayi very tight Ina turo baki.

"Alright darling keep sleeping sai dodon mafarkin ki ya kama ki"

A tsorace na bude idona na tashi tare da ajiyar zuciya nashige toilet sanye take da hijab dinta da alama ta idar da Sallah ne takoma kan dar Duma ta bude Qur'aninta dan haka take akwai addini that why we are so different because ni inason life dayawa.

Koda na shiga alwala na fara kenan nafara Jin wasu stressful voices Wanda Sam bana gane me ake cewa,
Wasu irin illusion images ne na fara gani sai dai pictures din are not clear hakan yasa ban fahimci abunda nagani ba sam
A hankali nadaina Ji alwala nayi nafito nayi sallolina ina idarwa kamar jira nakoma na kwanta ya nafy nata Kira'a momy ce ta shigo dakin da sallamar ta  ta kalleni tamin alamu da hannu nabiyota.

Dakinta tashiga direct Ina biye da ita " Zauna nan"
Ta nuna mun kan dan center carpet din dake shinfide a tsakar dakin.

" NAILA! NAILa!! NAILA!!!"
Tafada tana kallona kina na kasa duk na amsa ta
" how many times nayi calling sunan ki iye"
" 3 times momy"
Girgiza kai tayi tare da tsura mun ido kamar wacce take nazarin wasu abubuwa,
Dago kaina nayi Jin tayi shiru ganin idonta kaina yasa namaida kaina kasa da sauri.

"Meyasa kike wasa da ibada"
Shiru nayi " kina so Allah ya dunga fushi dake ne"
Girgiza kai nayi " to idan ba haka kikeso ba meyasa ba zaki gyara ba iye"
Girgiza kai nayi " momy kiyi hakuri Insha Allahu bazan karaba"
" Allah yasa yar Auta kije ki duba Qur'ani yayarki tamiki kari kafin ki koma today is Saturday ba school" tashi nayi cike da jin dadi nakoma daki kamar yadda tafada haka nayi.

Banji ma agun ba nakoma gado abuna saboda wani bacci dayake zuwa mun ya nafy bata ce mun komai ba taci gaba da karatun ta.

" Nafy! Naila!! Time na wucewa do you people forget kuna da islamiyya ne" Tafada sanda ta turo kofar dakinmu.

" oh ya Allah what do I do with this girl" Tafada tana nodding head dinta " Naila!!!".

Kamar a mafarki naji ankira sunan nawa a zabure na bude idona na zauna ina looking din dakin side by side.

" hahahahah look at you uwar tsoro tashi kishirya mutafi yau akwai karban hadda" takara she tana mun Dariya already ta shirya momy tabi suka rufe kofar.

Sauka nayi na shiga toilet danyin wanka bayan nagama tarar ruwan nayi a bocket dan Sam bancika son shower ba
Bayan na sirka ne na tube nafara wanka kamar kullum fuskata na fara sama soap din nan na fara Jin wani irin voice.

" Help me! Dan Allah kitaimakeni"

Muryar danaji yasa duk na duburburce na shiga lalluben ruwan ina wanke fuska da sauri2
Still  wannan voice din bai barni ba sam ga wasu abubuwa dana ke Ji Koda na bude idona voice din gaba daya ya dauke,
Duk jikina rawa yake Jan towel dina nayi da sauri Ina shirin arcewa naji like ankama kafafuna.

A hankali na kai eyes dina kan kafafuna dan na kasa Koda kwakwaran motsi wasu irin hannaye nagani kamar skeleton,
Bansan lokacin Dana sandara wani irin ihu ba Wanda duka gidan saida ya amsa
Jin kafata nayi ansake da gudu nafito toilet din na bude kofa nayi falo Ina ihu Ina kiran su momy.

" Naila lafiya kikai shiru",

Abunda yaban mamaki ganina nayi zaune Ina a dinning already cikin shiri nan nakara firgita natashi.

Bude bakina nayi zanyi magana amma Sam naji kamar anrike mun harce " Naila lets go tunda kingama",

Zan yi magana Nan ma momy ta katseni "oya tashi kuje na lura Yau bakison zuwa islamiyya and you have too
" dan ilmin addini shine mutum tashi maza a dawo lafiya",

ba yadda na iya na mike Ina mamakin yaushe na fito har mukai break na shirya am I dreaming or is something wrong with me,
Haka mukaje Islamiyya dake ba nisa a kafa muke zuwa a hanya ya Nafy keta Kara tuna mun haddata amma Sam nakasa fada mata matsala ta sam har muka karasa islamiyya kowa ya nufi ajinsu...........


Don't forget to Votes, share,comments thanks all👌

NAILA Where stories live. Discover now