Chapter 37: The Young Feelings

839 67 12
                                    

               Boom❗️❗️❗️
  Ayi hakuri na rashin jina kwana biyu abubuwane sai a hankali Allah yasa Mudace Ameen👏

         
     Don't forget to follow me on insta@Mimsqueen
Also don't forget to subscribe our YouTube channel @Hasken Alkairi Tv Naila Voice will soon be with you soon Insha Allahu Thanks all 👏

             Not Edited✍🏽

🅿️37

Zaune nake a babban falo nida momy Amma Sam narasa zantukan da take mun kawai amsata nake Amma a raina tambayar kaina nake meya faru danine ga gabana da yake faduwa.

" haba Amina Kidaina mata zancen abunda bahaka  yake ba maybe is just a dream kawai" Yafada yana mun murmushi.

" Amma ho....."

"Kinga taso muje inganki dan fita zanyi" yakatseta da sauri tashi tayi da sauri suka haye sama cigaba nayi da zama agun ina mamakin zantukan momyn Farid.

Najima zaune ina kallo sosai nafara Jin dadin series din da ake a Zeeworld din sosai nafara Jin wani kamshin turare me kamshi da sanyi yana ratsani nan nafara tunanin inda natabaji tare runtse idanuna sosai.

"Ya Neeb"

Na furta a hankali cikin sanyayyar voice dina Wanda zai iya karanto maka yanayin da nashiga.

"Yes Naila!"

Kirjina ne ya shiga bugawa tare da razana saboda sweet voice dinshi daya doki dodon kunne na waige2 nafara a tsorace batare dana kalla kofar shigowa ba Jin lallausan hannayensa a kafaduna yasa natashi a tsorace na waiga bayan kujerar.

Shine tsayen ya tsareni da kyawawan idannunsa masu matukar razana ni a Koda yaushe kasa furta Koda kalma daya nayi duk da a zuciyata kalamai be makil da tambayoyi.

Murmushinsa me kashe mun jiki yayi dimples dinshi suka lotsa ciki yakara bayyana kyawunsa dan kasa yayi da Kansa ya dago hannayensa nabi da kallo wadanda na nan exactly cikin pocket dinshi inda yasaba zubasu " oh my goshhh am i dreaming!".

" no you are not"

Sam bansan zancen da nake a zuciyata ya fito fili ba sam hakan yakara gudun beating din da heart dina yake a wannan lokacin ji nake kamar nashige jikinsa na rikeshi gam abunda banta ba jiba Yau natsinci kaina dashi.

" Naila! Baby!!......"

Momy ta katse mun duniyar Dana tabka ganin Muneeb da tayi a tsaye batare da ta San ya dawo ba sam Ko zuwan sa gidan.

" A'a Muneeb! Kaine a gidan"

Cike da jin kunya yayi kasa da Kansa ya zagayo ya sunkuya yagaisheta " Ah lallai Yau muna da manyan baki Ashe gidan Yau duk 'yan Hutu ne yanzu suma suka kirani sun iso zanje dauko su a Airport"

" momy harsun karaso"

Nafada ina kallon gefen ya Neeb wata irin harara ya maka mun da sauri na dauke kaina kanshi dan jikina har rawa yake ganinshi.

" eh walh da zamu tare Amma yanzu kinga ga Muneeb bari muje da Farid kawai da dadynku"

Girgiza mata kai nayi " Zanje!"

Nafada Ina sake satar kallonshi wannan karon Sam bai kallo inda nake ba " no kizauna gasu laraba a kitchen kisa a kawo mishi abubuwan da suka dace kinji".

Zaro wayarta tayi takira ya Farid baikai 2mins ba ya shigo falon ganin Muneeb a falon zaune ba karamun razana shi yayi har saida hakan ya nuna tattare dashi.

NAILA Dove le storie prendono vita. Scoprilo ora