Chapter 39

749 78 4
                                    

             Don't forget to follow me on insta@Mimsqueen
Also don't forget to subscribe our YouTube channel @Hasken Alkairi Tv Naila Voice will soon be with you soon Insha Allahu Thanks all 👏
        

               Dedicated To 80k and all my fans thanks guys👏

🅿️39

Yau garin yayi sanyi sosai banda karar iska da bishiyun dake kadawa bakajin komai 10pm Ne Amma yanayin garin zaka iya cewa 12am tayi.

Zaune nake kan bed din ina faman jin wakokina cikin kwanciyar hankali sosai nake Jin dadin wakar Wizkid din na 'Craving' sosai nake Jin dadin music din wizkid Wanda kusan shida Tiwa Savage suka cika wayar tawa har wani lumshe idona nake.

Tabani tayi a tsorace na kalleta alwala tayo daga toilet tafito cire daya earpiece din nawa nayi da alama magana take mun.

" sis kitashi kiyi Alwala kiyi isha'i mufita falo hira"

Dan tabe fuskata nayi dan Sam ni ba kullum nake iya yin sallar isha'i ba especially da ya Nafy da momy basu nan bancika sallah ba sam yana wuya nayi biyar a rana.

Murmushi naimata ganin yadda ta tsareni da ido " don't worry little sis ke kiyi ni bazan fita hira ba gaskiya kwanciya zanyi".

Murmushi taimun batare da ta musan ina kallo ta tada sallar maida earpiece dina nayi tare da hararta dan nalura a kwana uku da sukai da dawowa gidan yarinyar nason takuramun kamar Aunty nafy.

Lokaci guda naji bana mood naji inason kiran ya Neeb duk da tun randa suka dawo bankara sashi a idona ba kirama hakan tunda yakira bansan na katse ba saboda Nasiba daga baya kusan kullum saina kirasa baya Kira sai ya Nabil da shima naji yayi sanyi Ko calls dina baicika picking ba.

Tuna momyna nayi nan take naji hawaye na zubomun cire earpiece din nayi nakoma nakwanta ina matukar kewarta sosai bansan a dadin lokacin nadana dauka a wannan yanayin ba baccine yafara fisgata idona suka fara rufewa tun ina budesu harna kasa.

Jin karar wangame kofa ne irin da karfin nan yasa na firgita na bude idona yayinda wata iska ke busowa ta kofar karar guguwar harcikin kunnena inda komai na dakin ya soma kadawa inda Fear voice din ya cigaba da kadawa a kunnena sosai jikina rawa yake na matse gu guda.

" Naila! Naila!! Save me please Naila ahhhhhhhhhhhhhh".

Yayi wata irin razananniyar Kara " Naila ina tare dake kirufe idonki kiyi addu'a!"

Voice din matar nan Dana saba ji " Naila!!!"

Nakuma Jin voice din lokacin da nake shirin rufe idona kirjina banda bugawa ba abunda yake yayinda nakai idona kofar inda idona suka ci karo da fuskarshi Wanda komai nashi farine kamar anyi paint yana nufoni rufe idona nayi da sauri na sunkui dakai jikina na rawa.

" Naila!"

Ban dago ba banda sake matse idanuna nake Jin antabani yasa natashi a razane inashirin ihu ya rufe mun baki da hannunsa.

" hey! Come down is just me meya baki tsoro haka inata magana tuntuni"

Gabana ne yafadi tabbas fuskar ziyad nagani anmai white paint haka kuma voice dinshi ne sauka nayi daga gadon nayi hanyar fita inaji yana kirana Amma Sam bantsaya ba a hanyar sauka step naci karo da dadynsu.

NAILA Where stories live. Discover now