💔RAI---DAI💔 six

249 27 6
                                    

Hamma ne ya fara cewa

"ah ah! waye ya tabo mun yarinya? me ya same ta? me ya faru?"

cikin ladabi Godiya ta risina tace

"Wai sai an biya da ita ta kanti. Kuma yallabai Khalifa wancan satin yace a daina biyawa wani wajen in aka ďauko ta daga school"

cikin rarrashi Hamma ya janyo hannun Mena tana ta turjewa tana bori, iyayen da kakkanin kowanne da kalar lallamin da yake yi tana kara botsarewa, sai Abie ya sa hannu a aljihu ya ciro ýan ďari biyar biyar guda shida ya miko mata yana cewa

"gashi tashi kuje maza! tashi Malam Musa ya kai ku kuje ku siyo abinda kike so"

Mena ta tashi tana kuka zata je karbar kuďin taji an saka mata wata uwar tsawa.
sai lokacin ta lura da Khalifa da ke zaune a falon, don tun farko da ta gan shi ba zata yi wannan iskancin ba, baya mata wasa ko kaďan! tunda ya fuskanci soyayyar da iyayen shi da ýan'uwan sa suke gwada mata sai ya futa daga harkar ta, gata babu wanda ba zai mata ba, abu komai tsadar shi zai siya ya kawo mata amma fa ko a jikin shi bata zuwa ta zauna, tana ganin shi zata nutsu don ta san sauran.

"wanne iskanci ne zaki sa mutane a gaba kina musu kuka? are you stupid? oya shut up!"

nan da nan ta kama bakin ta tayi tsit!

"ďauki hijab dinki da jakar ki ki kai ďaki"

sum sum ta ďauki hijabin da jaka ta wuce da sauri ta tafi ďaki ta ajiye.

Sai gata sumi sumi ta dawo tana rabewa a jikin bango!
ya sake balla mata harara yace
"baki iya gaisuwa ba? baki ga kowa ba?"

cikin in'ina ta dinga bin kujerun su Hamma tana gayar da su abun gwanin ban dariya don idan ba Khalifan ba babu wanda ya isa ya soke zuwa kantin nan a zauna lafiya a gidan.

"Khalifa zafa ka saka yarinyar nan ta tsane ka, ka dinga sassauta mata mana, daga sati sai sati take ganin ka amma maganar arziki bata haďaku sai tsawa da hantara. ba haka ake wa yaro ba"

cewar Amma cikin sanyin murya.

Yaya Fatima tace

"Amma! har da kunyan Mena fa yake ji, kinsan na laqanci halin Khalifa duk abinda yake so toh sai ya nunawa duniya kamar kinsa yake yi. in kika ga ya shiga kyarar mutum toh wallahi bala'in son shi yake yi! in ba haka ba, ai kome mutum zaiyi ai ba ya ďaga ido ya kalla balle yayi magana"

suka sa masa dariya.

sai ya tashi tsaye yana duban Abie yace

"Abie lokacin sallah ya kusa bara na watsa ruwa na sauko mu tafi masallaci"

Abie murmushi kawai yayi mishi yana girmama halin shi da yabawa jarumtar da Allah yayi mi shi.

ya wuce ya haye benen da ďakunan su yake Yaya Fatima na tayi masa shakiyan ci suna dariya. Sam bai kulata ba.

wannan kenan.

.........................................................................
Dr. Amina, Ihsan da Hibba na ďaya daga cikin fasinjojin da jirgin Mangal ya kwaso daga garin Lagos zuwa Kaduna a yammacin lahadi. Bayan Emirate airline ya dauko su daga kasar Germany.

Suna futowa suka samu maigidan Ihsan da driver Dr.Amina suna jiran saukar su. babu bata lokaci suka kammala komai suka futo daga airport ďin zuwa gida. Ihsan ta shiga motar mijinta suka tafi gidansu, Dr. Amina ta kama hannun Hibba suka shiga tasu motar Ikechuchukwu ya nufo gida da su.

lokacin da suka isa Safa na kofar gate a tsaye, ta kagu, ta kagu, ta kosa ta ga sanyin idanunta, rabin rayuwar ta kwallin ďiyar ta Hibba.

lokacin da suka futo daga cikin motar kuwa ji tayi kamar ta kame don mamaki, ýar babyn ta ta tayi wani irin fresh kamar ba zaka taba ba sai ka wanke hannu. ta kara haske, tayi tsayi sosai kuma tayi qiba, gashin ta ya sake kwanciya sinkif a kanta, tasha kwalliya cikin skirt da riga pink and silver kamar wata rainon turai. Ingantaccitar lafiya ta wadata a jikinta kamar ba itace wadda suka tafi lage lage da ita ba. wai Hibban ta ce yau ta koma haka.

RAI DAIWhere stories live. Discover now