RAI DAI 26 BY CUTYFANTASIA

217 26 1
                                    

Ďankasa na zaune yana jiran dawowar Alhaji Jibril amma shiru babu shi ba alamar shi. Sai da ya ga mintina arba'in sun shuďe sannan ya tashi tsaye yana niyyar bin bayansa, sai kuma ga kiran waya yana shigowa.
Komawa yayi ya zauna yana ďaukar wayar don ganin sunan mai kiran, cikin tashin hankali mai kiran ya soma magana

"I'm sorry about this news sir! Guguwar da aka tashi da ita yau tayi sanadin rushewar Ďankasa Estate,ko gida guda ďaya bai tsira ba. Yallabai bamu taba ganin abun mamaki irin na yau ba,........

Kafin ya karasa Ďankasa ya sulale ya faďi kasa yana kokawa da numfashi, bai taba jin abinda ya girgiza shi fiye da wannan asarar ba, toh sai dai mutuwar Yazeed kaďai zai iya haďawa suyi dai dai.
Rukunan gidaje ne guda hamsin aka gina su cikin shekaru goma, kowanne fili lokacin da aka futar da gidajen naira miliyan talatin ne, a yanzu kuwa da aka kammala komai suka zama gida, kowanne kuďinsa naira 112M wato miliyan ďari da goma sha biyu cif.
An gama komai tallar su ake yi a kafafen yaďa labarai, wasu tuni an fara payment ma, wasu kuma ana kan ciniki
Wai wannan ingantaccen nagartaccen ginin da aka yi mai kwari shi iska ta mayar flat a cikin awanni biyu kacal. Wannan wacce irin almara ce?

A guje Alhaji Jibril ya shigo tare da Dr. Elijah, daman futar da yayi Dr Elijan yaje ya nemo a waya suka taho da ambulance don yayi imanin wannan karon ko zuciyar Alhaji Ďankasa bata buga ba toh lallai zata yi raunin da zai daďe bai farfaďo ba.

Haka suka kinkime shi yana wani irin numfashi suka sanya cikin motar agaji, nan da nan likitoci suka saka masa na'urar taimakawa numfashi tare da first aid ďin da ya dace da shi a wannan lokacin. Sannan ta ďauke shi zuwa asibitin kungiya.
.........................................................................

Safa zaune cikin tagumi tayi tsananin zurfi cikin tunanin da take yi, hakika bata taba tunanin cewa wai dagaske zuciyar ta zata ha'ince ta ta yaudare ta ta ďora mata son abinda ba zata samu ba.
ABDULHAKEEM of all people? Me zaiyi da ita? Duk iya soyayyar da yake tunanin yana yi mata idan ma dagaske ne yana son nata ba zaiyi lasting ba, ba zai ďore ba, ba zai mike ba daga lokacin da ya gane wacece ita? Toh meye yayi zafi? Meyasa zata bari ta zurma ramin da babu wanda zai iya futo da ita?
Akwai plans da take yi wa kanta tunda yanzu she has a family, atleast she is not alone, She has a caring brother by her side. So zata yi duk wani abinda ya kamata wanda zai janyo wa Modu da Hibba farin ciki da alkhairi da nasara a rayuwar su. Iyakacin burin nata kenan,bayan yin ibada tukuru da kiyaye dokokin ubangijinta da riko addininta ta samu kusanci da Allah swt.
Amma a kashin kanta ita bata da wani hope ko plan, duk abinda take buri sun ta'allaka ne karkashin abinda ýan'uwanta suke so ba ita kanta ba.
Idan har Allah ya raya ta, su zata rayu cikin yi wa hidima, ta raini ýayansu kamar nata, ta basu kulawa da soyayya, ta taya su fuskantar duk wani kalubale na rayuwa. Ta mutu suna masu alfahari da ita. Iyakacin burin nata kenan.

Amma a wannan halin da take ciki, wani abu mai kama da mashi yana sukar ta cikin zuciya, ya hana ta sukuni ya hana ta walwala da farin ciki, ya hanata sakat, tana jin zoginsa da raďaďi a kowanne minti, tana jin kamar ta futo da zuciyar ta ta, ta jefar da ita kowa ma ya huta. Ba wani abu bane illah soyayyar Abdulhakeem.
Mamaki take ji da tsanar kanta a duk lokacin da kwakwalwarta tayi processing abubuwan da take ji game da Abdulhakeem ta tabbatar mata da amsar cewa soyayya ce. Wata bahaguwar soyayya mara sanin ya kamata da inda zatai muhalli, wata iriyar soyayya mara adalci da tunani. Toh idan ba rashin adalci ba ya za'ai soyayya ta mamaye ta bayan ta san ko ita wacece? Bayan ta san cewa son ba zaiyi mata amfani ko na kwayar zarra ba sai ma illolin da ba zasu lissafu ba.

"WHY?" WHY?? WHY ME?"

Ta fashe da kuka tana buga kanta a jikin gadon da take zaune a kai.
Ta ďauki awanni biyu a haka kafin ta tashi ta shiga toilet tayi wankan da ya gagare ta yi a wannan yinin.

RAI DAIWhere stories live. Discover now