RAI DAI 57 BY CUTYFANTASIA

199 19 0
                                    

Cikin nutsuwa ya soma magana ďaya bayan ďaya kamar yana karanta karatu.

"Ashe daman Amina baki gane wanne irin so nake yi miki ba? Well if you don't let me tell you
"Ina sonki da dukkan gaskiya da amanata, soyayya irin wanda baki bashi da damar iya bayyanawa, I love you with every fiber of my being, I love you to the extend that I feel my life will never have meaning without you! Your love is the only language all the bones and tissues in my body understand. You know what? A tunanina raini ne ga soyayyar da nake miki na zauna ina bayyanawa da fatar baki saboda son ya girmi harshe da kalmomi, Ba wani abu nake so a jikin ki ba, ba wata manufa nake nufi a kanki ba Amina, na fara son ki ne lokacin da baki da abun kallo ko ďaukar hankali, when you were just an innocent kid ďin da bata san ma meye kalmar soyayya ba, wata irin soyayya makauniya, kurma mara limit. Ba son ki nake saboda zan aure ki ki haifa mun ýaýa ba, ina sonki ne don karan kanki ba don amfanin da zaki yi mun ba. I do not care what you lack, ina tabbatar miki da cewa ko ido da kafa da hannaye zaki rasa abinda nake ji a kanki ba zai chanza ba balle wata mahaifa wadda ba zata hana ki gudanar da rayuwar yau da kullum ba. Abinda ya same ki ba nakasa bace, wata alama ce da Allah yake amfani da ita wajen nuna ayar sa, Idan ma wani ya ďauka ke nakasashshiya ce ni Abdulhakeem ban yarda ba, ke idan ma hakane naji na gani ina sonki haka! Kuma wata lalura ko nakasa ba ta da karfin da zata iya rage wani burbushi na kaunar da nake miki, domin banki ko gawar ki na zauna da ita ina kallo ba idan hakan yana iya faruwa. Ba ina gaya miki haka bane don kiji daďi ko na cimma burina a kanki, billahil azeem ni Abdulhakeem babu wani ďan'Adam da ya isa nayi mi shi daďin baki, ina gaya miki ne saboda ki sani tunda na fahimci cewa baki sani ba, bani da sha'awar zama na buďewa mutum sirrin zuciyata ko na fallasa masa halin da nake ciki, har ina rantsuwar cewa ba zan taba yi ba, but I have no option a yanzu than na zauna nayi ta baki labarin irin yanda nake ji a kanki if that will make you believe that the love I have for you is the purest form of love daga yanzu har zuwa lokacin da mai busa kaho zai busa kalmomi na ba zasu kare ba.
Bansan me ya sa kike irin wannan tunanin ba, da zaki san abubuwan da na shiga a kanki a rayuwa, da baki yi mun rashin adalcin tunanin baki dace da ni ba. Ban taba soyayya ba sai a kanki kuma bana raba ďaya biyu ba zan sake ba, ko da kaddara zata hana mun ke bazan sauya sheka ba. Zan iya jure komai, Zan iya hakura da komai tunda na iya hakura da aikina a kanki, zan iya jure duk wahala da wuya da duk wani obstacle a rayuwa but I will never give up on your love! I look forward to having you in my life, the care I promise to give you will put a princess to shame! I will give you all that you deserve, all that you need to be given to feel the most special being on this planet. I promise it's not a sweet mauth or lie, it is the real feeling I have for you.........."

Daga kuka Safa ta koma hawaye ta koma ajiyar zuciya ta koma lumshe idanu kafin wani bacci ya silalo yayi awon gaba da ita ba tare da ta shirya ba..

Murmushi yayi ya tashi ya futa daga ďakin cikin sabuwar soyayyar Safa wadda ya baiwa suna da kaddarar rayuwar sa. A parlour na karshe ya tarar da Mummy Saratu wadda ita tayi mi shi izini shiga cikin ďakin ya samu Safa. Bai iya yi mata sallama ba ya sa kai ya fuce daga ďakin cikin wani irin yanayi.
Mummy Saratu mamakin irin wannan soyayya take yi ta Khalifa kamar bature tana kuma tausaya halin da suka tsinci kansu a ciki shi da Safa. Ta wani fannin tana yi wa Safa farin cikin samun irin wannan managarcin masoyin kamar Khalifa. Ko da yake ta tabbatar cewa Allah ba zai bar rayuwar Safa ta kare a haka ba sai ya bata abinda zai fanshe mata bakin ciki da wahalar da tasha.

Karfe biyar kiran sallar assalatu ya farkar da ita daga nannauyan baccin da tayi, ta tashi zaune kamar anyi mata duka tana haďa gumi a dalilin mafarkin da tayi. Wai tana wani fili a zaune sai kawai ta hango Ammin ta tana tahowa gare ta fuskar ta sai kyalli take yi. Tana zuwa dab da ita tace

"Ki cika mun burina Amina ki auri Abdulhakeem! Kar ki karyamun alkawari"

Tana gama faďin haka ta juya ta tafi, cikin ikon Allah kuma bata samu damar yi mata magana ko motsawa tabi bayanta ba sai ta farka.

RAI DAIWhere stories live. Discover now