RAI DAI 33 CUTYFANTASIA

201 22 2
                                    

Ko musu baiyi ba ya karba yana ta godiya kamar ba shi ne ya bata kudin da tayi amfani da shi wajen siyayyar kayan ba. Wato shi mutum yana son alkhairi komai kankantar alkhairin shikuma komai kuďinsa. Na kissima a raina. Har bakin mota na raka su, Ammi ta tsaya daga zaure muna ďaga musu hannu har sukai nisa sannan muka dawo.

Allah ya rufa mana asiri wannan rana domin domin muna komawa gidan sai ga Baba kamar an jefo shi. Wata nutsuwa da tsoro suka shige mu, ga mamakina wannan karon sai ya sakar mana fuska kamar bashi ba, harda yi mana siyayyar kayan masarufi, Kodan ganin alamar Ammin na shirin haihuwa ne Oho! Wannan abun mamaki na Baba da yawa yake, shi a ciki yake son ďan sa idan ya futo duniya shikenan ya daina yayin sa babu  ruwansa da shi.
Ammi bata taba tambayar sa ina ya kai Modu ba ko kuma yaushe zai dawo, Yakuri tace mata kada ta sake ta tambaye shi, addu'a matuka zata dinga yi a akan Allah ya shirya mata shi, ya tsare mata shi ko a ina yake kuma Allah ya bashi ilmi da karatun da duk duniyar musulmi za tai alfahari da shi. Watarana zai zo da kafarsa ya neme ta ya gatanta ta ya futar da ita daga halin da take ciki. Da taimakon wannan shawarar Ammi ta kwantar da hankalin ta ta samu nutsuwa.

Tun bayan tafiyar Baba Ammi ta soma rashin lafiya a tsaitsaye, duk karfin halinta sai dai ta kwanta komai ni nake yi, don ma Allah ya taimaka anyi hutun makaranta.

Tun dawowar Abdulhakeem sai ya mayar da gidanmu wajen zuwan sa duk weekends, sunyi wani irin sabo da Ammi na ban mamaki, amma banda ni, tunda shi bai cika far'a ba kuma hirar tasu a kullum baya bukata ta, ba sa sanya ni a ciki, sabanin mai babban suna wanda in sukai magana ďaya biyu sai ya jefo sunana ciki, ko yayi mun tambaya. Yawancin hirarrakin na shi ma a kaina ne.
Shikuwa wannan kasa kasa zaka dinga jin suna maganar kamar masu raďa, sannan dukansu nutsuwa suke yi ba dariya ko nishaďi ba, na kan rasa sunan wannan al'amari. Abdul Hakeem kamar hidimar sa kamar ta yayansa, duk lokacin da zai zo hannunsa da ledoji kuma idan zai tafi sai ya ajewa Ammi kuďi. Tun tana faďa har watarana ya kada baki cikin bacin rai  yace

"Yanzu Ammi idan Modu ne yake hidima da ke sai ki bata rai kice ya daina?"

A sanyaye ta girgiza kai!

"Ki ajeni a matsayin Modu, ki dinga kallona kamar shi kuma duk abinda kika bukata ki gaya mun kamar yanda zaki gaya masa; Zan zamo mai biyayya kamar shi"

Bai kara magana ba ya sa kai ya futa cikin ďaurewar fuska. Baki na saki ina kallon wannan ikon Allah, a ina yasan tana da ďa Modu har ma da inda aka kaishi? Wata zuciyar tace

"Wannan kus kus ďin da suke idan ba sirrin juna suke tattaunawa me suke yi?"

Na tabe baki na shiga ďaki domin yanayin daure fuskar shi da rashin shiga sabgata da yake yi ya sanya bana ra'ayin shi. Duk da ina jin dadin yanda yake kyautata Ammi yake girmama ta.

Kwanaki shida bayan wannan lokacin Ammi ta tashi da matsanancin ciwon ciki, ranar asabar ne da safe, ina gabanta ina kuka domin bansan me zan mata ba. Nayi tofi, nayi addu'ar, na samo zuma na bata amma bai lafa ba.
Muna cikin wannan halin yayi sallama ya shigo cikin shigar sa ta kullu yaumun, kakin yan youth service.

A ruďe ya karaso yana cewa "lafiya? Me ya same ta?"

Nidai kuka kawai nake yi, dakyar Ammi ta iya mikewa ta ďauko gyalenta muka tafi asibiti bisa umarnin Abdulhakeem. Cikin karamar motar sa muka tafi ina tallafe da ita a bayan motar tana ta gumi tana kiran sunan Allah!

kujerar ďora marasa lafiya aka gangara da ita emergency suka barmu tsaye cikin tashin hankali.
Durkushe nayi a wajen ina kuka mai tsuma rai,
"Allah kada ka ďau ran Ammina, Allah ita kaďai ta rage mun, Allah bani da kowa sai ita, idan ta mutu bansan ya zanyi da rayuwata ba Allah na tuba Ya Allah ka taimakeni kar na rasa Ammina"

Irin waďananna zantukan da ma waďanda bazan iya tunawa ba na dinga yi ina kuka kamar zautacciya.

"Amina!"

RAI DAIWhere stories live. Discover now