RAI DAI 52 BY CUTYFANTASIA

231 17 0
                                    

Jikinta ne yayi sanyi lakwas! Maganganun babanta sun shige ta sosai, kuma tana matukar son ta sanar da shi abinda yake damunta amma sai taji kamar an ďaďďaure mata harshe ba zata iya furta komai akan abinda tagani ba. A karshe sai kawai ta soma cewa

"Abu babu komai! Kawai dai yanzu Jibril baya zama a gida harkoki sun masa yawa, nikuma kaďaici ya isheni bansan kowa ba a garin, gashi tunda muka koma bai samu zama ya samarwa Modu makaranta ba kullum muna gida. Ina son na dawo nan ko mu koma Kano inda muka fara zama yaran su shiga makaranta nikuma na samu ko teaching ne na soma yi wanda zai debe mun kewa."

Shiru yayi yana kallonta. Ta tabbatar ba abinda yake damunta kenan ba, Yasan akwai abubuwan da suka fi wannan cin ranta. Amma ba zai takura mata ba, ba zai ce lallai sai yaji ba. Zaiyi duk wani kokari wajen ganin ya samar mata kwanciyar hankali da nutsuwa indai yana numfashi.

Wayar Jibril ta kira yace yazo yana nemansa. Ita kuma ta koma cikin gida tare da yaranta matan gidan babu wadda ta dube ta balle ta tambaye ta me ya kawo ta. Dakinta na ýanmatanci ta budè ta karkade ta share ta shiga tayi wanka, Abui da kansa ya sanya personal kukunsa ya dinga shirya mata abinci lafiyayye sau uku a rana. Don haka babu ruwanta da harkokin mutanen gidan balle ga shiga sabgarsu.

Irin hakan da Abui yake mata ne yake rura wutar tsanar ta a zukatan matansa da ýan'uwanta. Babu me mata kallon rahama balle wata magana me daďi ta haďa su.
Washegari Jibril yazo amsa kiran da Abui yayi masa, bata San me suka tattauna ba illa dai Abui ďin yace akwai gidansa da ke Fada street zai sa a gyara mata ta koma.
Jibril bai nuna mata komai ba, sai ma hakuri da ya dinga bata sannan yace ya amince ta soma aikin idan ta samu.
Sai taji hankalinta ya kwanta, cikin sati biyu aka gyara gidan aka shirya shi da furniture masu kyau sabbi qal sannan Jibril ya kwaso mata kayan ta na can Lagos na amfani ta tare ita da yaranta.

Cikin watanni biyu ta sauya ta maida jikinta domin mahaifinta ta aje mata duk wani abun bukata da jindadin rayuwa. Bai taba tambayarta menene bata da shi ba ko me take bukata ba sai dai duk wata za'a ciko mota da kayan masarufi a jide mata, da isassun kudi a envelope. Yara sun shiga makaranta mai tsada, ita kuma ta koma University of Maiduguri ta ďora PHD a maimakon aikin da tace zata fara, da umarnin mahaifinta.

Jibril yana ďaukar watanni uku har huďu baizo ba, babu wata shakuwa tsakaninsa da yaransa, baya yi musu komai kuma bata iya buďe baki tace masa suna da bukatar wani abu ko kuma abu kaza da yake ba daidai bane. Duk abinda zai mata ba zata iya ďaga ido ta kalle shi ba don haka suka fi sakewa idan baya garin.

Ranar wata talatar da ba zata taba mancewa ba suka wayi gari Abui sugar ďinsa yayi kasa sosai! Aka dauke shi zuwa asibiti, Hamra na gefensa tana kuka sosai domin ya daďe bai galabaita idan ciwon ya tashi kamar wannan lokacin ba.

Sai da likitoci sukai kwashe awanni biyu akansa sannan ya samu bacci. Yana bude ido yace wa likitan ya kira masa Hamra.

Likitan ya futo ya Kirata, ta mike jiki a sanyaye ta shiga ďakin ýan gidansu na binta da harara da kallon tsana da hassada.
A kan kujerar gefensa ta zauna tana goge hawayen da suke zubo mata zuciyarta a karye.

"Abui sannu"

Ta fada a raunane.

Cikin karfin hali ya kamo hannunta ya soma yi mata magana a hankali.

"Humaira kiyi hakuri da rayuwa, kici gaba da hakuri da rayuwa, ki rike Allah duk wuya duk runtsi kada kibi ruďin shaidan.....idan kin koma gida, kije library ďina, cikin "safe" ďina akwai wani littafi mai hoton giwa a bangon shi, ki dauka, zakiga cikakken asalin mahaifiyarki da garinsu da komai da ya shafe ta. Watarana nasan zaki neme su Humaira, mukullin safe ďin yana karkashin carpet ďin dakina daga gefen gado.........."

Sai ya soma haki numfashin sa ya dinga sama da kasa. A guje ta futa ta kira likita, nan fa suka sake rufuwa a kansa don ceto rayuwarsa. An kwashe sama da awanni huďu kafin numfashin sa yayi dai dai. Amma sun kori kowa sun ce basa son ayi masa hayaniya.
Ita dai Hamra ta zama bebiya, tana rakube a gefe da yaranta ta rungume su tana kukan tashin hankali da fargabar abinda ciwon Abui yake nufi.

RAI DAIWhere stories live. Discover now