RAI DAI 42 BY CUTYFANTASIA

204 23 1
                                    


Tushen samun cikakken ďa mai nutsuwa da tarbiyya da lafiyar jiki da ta kwakwalwa da zuciya na samo asali ne daga irin kulawar da yaron ya samu a wajen iyayen shi. Yaran da suka taso a gaban uwa da uba waďanda suka fahimci juna suka sauke hakkin da ke kansu suka rungumi ýaýan da soyayya da kulawa sun futa daban da duk wani ďa a duniya. Idan har aka samu akasin da yaro ya taso cikin gidan da iyayen shi basu da kwanciyar hankali da fahimtar juna, kullum suna cikin faďa da zage zage ko kuwa shi uban yana azabtar da uwar, ko kuma uwar bata tsaya ta maida hankali kan tarbiyyar gidanta da ýaýanta ba toh akwai gagarumar matsala.
Rashin jituwar iyaye shi ne mataki na farko da yake lalata tunanin ýaya ya gurbata musu rayuwa su zama emotionally abused, su rasa walwala da farin cikin da yaro mai shekarun su yake bukata.

Sai maudu'i na gaba wanda yafi kowanne ci mun tuwo a kwarya. Ba komai bane illa rashin ýancin da mace take fuskanta a rayuwar aure. Yanda take fuskantar kalubale kala kala da matsi da takura da tsangwama wai saboda ta kare hakkin sunan babanta ko sunan uban ýaýanta ko kuma su ýaýan kansu. Mace ta kan shiga wata irin bakar rayuwa ta abuse kuma a toshe mata baki a hana ta katabus domin kawai kada ya janyo wa iyayen ta ko ýaýanta abun kunya. Ba'a considering halin da zata iya shiga a dalilin wannan abuse.

Anyi wa mata yara kanana babu dadi adadi fyaďe amma ko hukuma taso kwato musu hakkin su sai iyayen su nuna basa so, sai su rufe maganar wai kawai don kada sunan su ya baci. Don kar yarinyar ta rasa me aurenta, don kar duniya ta dinga kallonta a matsayin mara daraja da cikakken ýanci.

Babban abun bakin ciki da takaicin shine su waďanda suke aikata laifukan haka suke cin bulus, ruwa tasha. Suci gaba da rayuwa freely cikin mutane babu tsangwama ko kyara ko wani hukunci mai tsanani, su bar waďanda suka aikatawa laifin cikin kuncin rayuwa da bakin ciki na har abada. A dalilin hakan, yara da yawa suka nakasta, wasu suka samu tabin kwakwalwa, wasu suka yi hannun riga da walwala da jindaďi, duk inda suka yi ana nuna su ana zunďen su. Idan kuwa kaddara ta ratsa suka samu ciki ta wannan hanyar suka haiwu, toh duk wani tofin Allah tsine da Allah wadai akan su zai kare bayan basu san hawa ko sauka ba.
A wannan dalilin ake samun yaran da suke haďiye zuciya ta mutu, wasu su murdèwa jariran da suka haifa wuya su mutu, wasu su bar gida su shiga duniya, wasu su jefar da jariran a masai ko a kan bola. Waďanda kuma basu yi hakan ba sai su faďa sabuwar rayuwar kunci da takaici ta raino a lokacin da ya kamata ace suna aji suna ďaukan karatu. Shikenan rayuwar su ta durkushe farin cikin su ya lalace, an gama nakasta duk wata dama da suke da ita a rayuwa na zama wasu abubuwan alfahari.

Akwai cases kala kala na matan da suke fuskantar physical and emotional abuse daga mazajen su, amma a dalilin tsoron kada su tafi su bar ýaýan su, kada rayuwar yaransu ta lalace, sai suyi shiru suna ta kunsar bakin ciki wanda sau da yawa yake zama ajalin su.

Akwai mata da yawa da mazan su suke barin su da nauyin gida da na yara, su tafi uwa duniya, su zasu yi duk wata fafutuka su nemawa Ýayan ci da sha da sutura amma tukuicin da al'umma zasu yi musu shine su kira musu ýaya da ýaýan mata. "Wannan ďan mace ne, wannan ýar mace ce"
Toh shi su ýaýan matan ba ýaya bane?
Idan mace ta zage damtse tayi ilmi mai zurfi ta kama aiki don ta tallafawa kanta da yaranta sai a dinga yi mata kallon ýar iska ko mai buďaďďen ido, idan sana'a take musamman wanda ta danganci international business toh sunan ta karuwa komai kamun kanta.

Wanne irin rashin adalci ake a wannan rayuwar? Meya sa ake karyawa mata daraja da ýancin da suke da shi bayan mutane ne masu ýanci da daraja musamman a addinin Islama. Meyasa irin haka yake faruwa a arewacin kasar mu? Mecece kuma mafuta?.

Yaya za'ai a shaho kan wannan matsala yara su daina faďawa kangin CHIlD ABUSE? Idan har aka toshe wannan kafar hakika za'a samu rangwamen yaďuwar ýan ta'adda, ýan shaye shaye da ýan bangar siyasa, karuwai da yan damfara da matsalar ALMAJIRANCI a arewacin Nigeria.

RAI DAIWhere stories live. Discover now