XXX

781 84 7
                                    

Kuyi ha'kuri da wannan banida time ne sannan banaso na karya alqawari😊 insha Allah I will try to post more tomorrow

Cikin sauri jabir ya 'karaso tareda d'aukan akwatina d'aya, 'kare min kallo yayi kafin ya Sanya akwatin a mota yace "me ya faru Bilkisu".

Wani azababben ciwon kai nakeji sannan banida niyyar bashi amsa, kalar tausayi nayi domin na sanshi da takura nace "Yaya idan munje gida mayi maganar yanzu dai muyi mu bar wannan wurin".

Bai sake tambayata komai ba har  muka d'au hanya, saidai lokaci lokaci idanunsa na kaina yayin da nawa idon ke titi, ciwon kaina 'karuwa yake saboda tunanin da nakeyi Wanda baida amfani.

Tsayawa naga Yaya yayi ya fita ba tareda yace min komai ba, dawowa yayi da ice cream da cake ya mi'komin su ta window, godiya nayi masa na bud'e ice cream d'in na fara sha, fata nake sanyinsa ya kashemin zafin da nakeji a cikin jikina, dukda ya sanyayamin raina amma zuciyata tana nan yanda take sai ma 'ko'karin kuka da ba fara, meyasa Saleh zai yanke wannan hukuncin a irin wannan lokacin? Meyasa banyi ha'kuri har ya huce ba na takura masa akan ya yarda dani har yardar ta kawo wannan ga'ba? Akan wane dalili ma nake baiwa kaina laifi? Ba laifina bane ya sakeni zuciya ce kawai ta d'ebeshi, idan har inada zuciya ya dace na cire Saleh tun yanzu daga raina.

Bansan lokacin da na shanye ice cream d'in ba, jifa nayi da robar ta window na maida kaina ina kallon waje, har yanzu ganin sakinnan nake kamar 'karamin abu ne, kamar yana zuwa yana cewa nayi ha'kuri ya wuce, gani nake tamkar zai biyoni a baya yace yayi kuskure nayi ha'kuri na koma d'akina Amma nasan duk wannan ba abune Mai faruwa ba, yanda naga fuskar Saleh a yayin da ya furtamin wannan mumkunar kalma bnaso har mutuwa ta na sake ganin wannan yanayin.

Muna isa gida na d'auki 'karamin akwatin na shige na bar Yaya a waje, sallama nayi sai naji tamkar an manne min 'kafafuna a waje, tsoron haduwa nake da mama na fad'a Mata wannan abun, ban sake tabbatat da saki babban Abu bane sai yanzu.

Amsa sallamata mama tayi tareda ambatar sunana, Jan jikina nayi kamar wadda 'kwai ya fashewa aciki na shige kaina a 'kasa, shiru mama tayi ta zubamin ido har na zauna, tun kafin ta tambayeni nace "ya sakeni".

Wasu zafafan hawaye naji sun zubomin Wanda na danne tun farkon faruwar wannan abun, sam ban shirya amsa tambayoyin da nake tunanin zasu fito daga bakin mama ba, nasan abinda zata tambayeni shine me ya faru? Meye dalili? Akan me?......saidai ga mamakina jin mama nayi a gefena tana rarrashina.

Hakan na nufin ya sanyamin nutsuwa amma sai na sake karaya, Kuka nake sosai a kafad'ar mama tana bani ha'kuri, abinda ya kamata mijina yayimin lokacin da aka min sharri amma sai ya goyi bayansu, ta yiwu rabuwata da Saleh shine alkhairi.

Sallamar Yaya naji shima ya shigo ya zauna, abinka da namiji yana zama yace "wai ke meke faruwa ne?"

Cikin sanyin murya mama tace "jeki ki ajiye kayanki a d'aki ki huta".

Tashi nayi ba tareda na kalli Yaya ba na shige d'aki, ajiye jakata nayi da akwatin da naja na kwanta kan gadona, 'karewa d'akin kallo nakeyi fatana wannan d'akin ya sanyamin nutsuwar da nake bu'kata amma Ina...tunanin gidana nake ko nace gidan Saleh, the more nayi tunanin gidan the more yake sake fita a raina, idan na tuna da Saleh kuwa tamkar zuciyata zata fito.

Cire kayana nayi na shiga wanka na dinga sakarwa kaina ruwa har saida na gaji, fitowa nayi nai shafa'i da wutri da rashin nutsuwa ya hanani yi a gidana.....afuwa gidan Saleh, sai yanzu Huda ta fad'omin a Rai, ji nayi Ina matu'kar kewarta.

Duk abubuwannan da suka faru Huda sun fita da ya Usman, al'kawari yayi mata cewar zai kaita ta hau lilo saboda na daketa shine suka fita yau, bansan lokacin da ya dawo ba ban kuma ga alamar Huda ba, alamun dai ya samu labarin abinda ke faruwa ya barta wajen Sultana kar taga halin da muke ciki.

Wayata na d'auko na kira sultana na tambayeta lafiyar Huda, sanarmin tayi Huda nata tambayata, ban sani ba ko tasan abinda ya faru saida naji ta sanarmin zata baiwa Saleh uta ya kawomin, cikin sauri nace "a'a Dan Allah ki baiwa usman ya kawomin ita banason ganin Saleh yanzu".

Shiru tayi sannan tace "kiyi ha'kuri bilkisu komai mai wucewa ne, dukda bansan duk abubuwan da suka faru ba amma bai kamata kiyi yaji ba Zaki basu abinda sukeso ne, gobe za'a kawo miki ita amma Dan Allah kiyi ha'kuri ki dawo,bansan ya zanyi rYuwa a wannan gidan Babu ke ba kinsani kowa ya tsaneni".

Shiru nYi na rasa me zance mata, ha'kura tayi ta katse wayar Nima na d'auki cajata na fita, zuwa yanzu na d'an samu nutsuwa kad'an a yanayina amma cikin raina Babu wani banbanci da lokacin da na baro gidan Saleh....Saleh, synannan ya zama tamkar magani a bakina, duk lokacin da na tuna da sunan sai naji wani d'aci har cikin bakina.

Fita nayi naga mma tana yiwa jabir kashedi kar ya sake ya yiwa Saleh magana ko ya nuna masa wani Abu ya faru,

"Wannan abun tsakanin Mata da miji ne idan ka shiga ka zubar da girmanka ne da darajarka, sannan Kai bakasan me ya faru ba menene amfanin d'aukan hukunci akai? Mu jira muji ta bakinta Amma inaso ka sani, ko me ya faru kar ya ta'ba ala'karka da Saleh musamman ta bangaren kasuwancinku".

Zamana ne ya dakatar da mama ta kalleni tace "ya kikeji yanxu?"

"Dan dama-dama" na fad'a tareda 'ka'kalo murmushi, harga Allah Babu abinda nakeso nayi a yanzu kamar Kuka, sannan inaso na sanarwa mama abinda ya faru Ina Jin tsoron me zata ce?, Kamar Yaya ya karanta tunanina yace "bilki....ki fad'amin me ya faru ne wai? Meyasa Saleh yayi gaggawar sakinki ki nacw gangancin sakinki?"

Har na bud'e baki mama ta katseni tace "jabir ka bar yarinyarnan ta huta tukuna, jeki d'auko abinci kici".

"Banajin yunwa mama".

"Yaushe rabonki da abinci?"

Shiru nayi domin yau tea ne kawai a cikina shima Babu Madara, d'okin zuwa wajen mama ya hanani cin komai sannan bala'i ya hanani lunch, a takaice dai daga tea sai ice cream nasha yau kuma banajin yunwa, numfashi naja nace "nasha ice cream a hanya banajin yunwa".

Tashi mama tayi tace "ice cream ba abinci bane, daga alamunki tun safe baki ci komai ba ni Bari na zubo Miki tuwo Kuma banaso ki sake min musu".

"Mama Dan Allah ki bar tuwonnan bazan iya ci ba, Yaya ya siyamin cake zansha da tea".

Zama tayi ba tare da tace komai ba sai kalle kalle muke, kafin kowa ya tambayeni na fara magana nace "Mama akan wannan kud'in ya sakeni".

Kallona tayi cike da mamaki naci gaba, Basu labari nayi ban cire komai ba a zagin da yayimin, Wanda yan uwansa sukamin da martanin da na maida Masa, lokacin da na Gama har sha'kewa nake saboda kuka, kallonsu nayi idona dishi dishi Amma naga alamun bacin rai a tattare dasu musamman ma Yaya da yake alamin zai iya kashe mutum, dukkanmu munyi shiru sautin kukana kawai ke tashi...

NAYI DACE✔️Where stories live. Discover now