XXXIV

922 80 7
                                    

Tashi yayi cikin hanzari ya fita, a 'kofa ya tsaya ya runtse idonsa idan ya kaiwa hajiya wannan magana ranshi ne zai 'baci bayaso tace ta san wannan zance saidai bayaso ya gaskata hakan, idan har gwamnati ta biya musu kud'in aiki meyasa suka kar'bi kud'insa? 'ko'karin danne gaskiyar yakeyi a bayan ransa saidai gaskiya a bayyane take 'karara, sai yanzu ya fara komawa hayyacinsa, shin me ya aikata cikin fushi? Me su hajiya suka aikata masa?

Komawa yayi ya kwanta yana sake duba labarin domin ya gaskata, kwanciya yayi kan kujera ya fara tunanin yanda zai tunkari hajiya da wannan bayani, dalili d'aya yake son ji, meyasa suka kar'bi kud'in? Me zasuyi dashi? Da wannan tunanin ya kwanta

*********
*BILKISU*

Banyi tunanin za'a samar min aiki da wuri ba, amma abin mamaki ina zaune sai ga kiran aunty tace na shirya naje gidan ta zata kaini interview na aiki, dama ana bu'katar interview a nursing?

Ina shiryawa ta sake kirana, cikin d'aga murya tace "saura kizo min da jajayen idanu sau na saka a kwantar dake a asbitin na wata hud'u", dariya nayi nace "to aunty" abinda bata sani ba tuni na dena wa mutuwar aurena kuka, dama nasan igiyar aurena bazata zauna ba tun ranar da na saka 'kafafuna a gidan.

Bazan ce Saleh ya fita daga raina ba amma na kaishi can wani wuri a zuciyata, koyaushe yana raina amma bana tunaninsa, bansan ko akwai wanda ya fahimci maganata ba.

Na san halin aunty ko gumi ta gani a fuskata sai ta 'karewa Saleh zagi nima na sami rabona, saboda haka na d'an b'ata lokaci wajen makeup, abinda banyi ba kusan sati biyu kenan.

Powder na shafa na sanya purple d'in jambaki nayi highlighting da  jagira, saida na 'karewa kaina kallo sannan na yafa mayafi, i can't believe it, wai ni ke iddar Saleh ya sakeni, Allah yasa ma ba fara wuri.

Ina zuwa gidanta na sameta tana zaune a palour da jakarta da mayafi a gefe, kallona tayi ta saki murmushi tace "haba ko kefa, har kin fito a mace da kina kwance bakida aiki sai kuka akan wancan me......"

"Dan Allah aunty karki 'karasa ki barshi haka, ni ina mamakin ma yanda kalamannan basu 'kare a bakinki ba duk zaginsa da kikeyi a barshi haka". Na 'kare maganar ina dariya, harara ta tayi cikin wasa tace "da kansa kamar banana". Dariya nayi sosai, har mantawa nakeyi aunty ta kai mahaifiyata saboda yanda take abubuwanta, ta iya tafiya da mutane ko Yaya mutum yayi socializing da aunty sai ya sota, idan akayi hutu gidan cika yake da yara, dukda ban ta'ba ganin mahaifina ido da Ido ba amma idan na kalleta tana tuna min dashi, mama tana yawan fad'amin halinsu d'aya da mahaifina, irin mutanennan ne da basa nuna fushinsu, idan kana tunanin basu haushi saidai ma ranka ya 'baci.

"Tashi muje kar mu makara" tashi nayi muka fita a motarta, baifi tafiyar minti 15 ba sai gamu a asbitin, kallon wurin tayi tace "ya kamata a saya miki mota saboda fita", bance komai ba domin zanso nima na fara tu'ka motar kaina, ina yawan driving ta Saleh musamman zuwa makaranta kuma fita a motarka yafi mutunci musamman a wannan zamani na cudanya da 'katti a abin hawa.

Asbitin nada girma ba laifi sannan ya matu'kar had'uwa, tun daga wajensa har ciki, secretary ta wurin naji ta tambaya wani mutumi nan tace mata yana office, babu wani jira taja hannuna muka zagaye secretary d'in muka wuce, 'kwan'kwasa 'kofa tayi kafin ace mu shiga ta bud'e tareda turani sannan ta shiga.

A fusace mutumin ya juyo zai fara fad'a yana ganinta yanayinsa ya sauya, bansan waye wannan ba amma dai naji yanayin wurin ya canza, "ko kujera baza'a bamu ba Abban shaheed?"

Kallona yayi da alamun kunya sannan yace "kuyi ha'kuri ga wuri ku zauna", d'aura 'kafa d'aya kan d'aya aunty tayi sannan tace "sai naga kana nuna kamar baka san da zuwanmu ba bayan dai kai ka kirani ko har tsufa yasa ka fara mantuwa haka, ko kuma kyakkyawar 'yar tawa ce tayi maka?"

NAYI DACE✔️Where stories live. Discover now