XXXXXVI

1K 88 5
                                    

*alhamdulillah, alhamdulillah , alhamdulillah, Allah Kaine abin godiya, ka dawo mana da fareesa diyar ladingo lafiya, Allah ka sake tsaremu da mugun ji da mugun gani*

*56*

akiya na musu zuwa airport hannuna na cikin na Aliyu.

Kallona yayi ya kalli hanyar tafiyarsa yace "yanzu bazaki tausaya min ba ki taho tare dani? Su Mama kya dawo daga baya ki gansu".

Murmushi nayi nace "a'a na fa dad'e banga gida ba, tunda akayi aurena sau biyu nazo nan, sati biyu dai ai ba yawa ni da naso nayi arba'in?"

"Tabd'i da wallahi sai na biyo ki, watannin da nayi babu ke fa jurewa kawai nakeyi but I really miss you".

'karashe maganar yayi tare da hugging d'ina, banyi hugging d'insa back ba da farko saboda Mum tana kallona, daga baya dai nayi hugging d'insa nace "I'll miss you too".

'ko'karin kissing d'ina yayi na d'auke kaina, iya kunyar da zanji gaban Mum na jita banaso na 'kara wata.

Saida muka ga tashinsu sannan Jabir ya d'aukeni muka koma gida.

A gidan ma bata sauya zani ba, domin Yaya ke min wanka sannan ta wuni tana kula da Abduls, da dare kuma ni da Mama muyi fama domin kukan dare garesu.

Tunda naga sun wuni suna bacci na san yau akwai hirar dare, saboda haka na samu nima nayi baccin rana.
.
12am dai-dai suka farka saidai Basu tashi da rigima ba, 1:30 suka fara kuka gaba d'ayan su, 'ko'karin had'a musu madara na fara saidai gaba d'aya na rikice, yau ne rana ta farko da zan had'a musu madara.

Karanta instructions d'in na fara saidai kukansu gaba d'aya ya gigita ni, ga Mama yau tana wurin mijinta.

Ruwan zafin na zuba bansan lokacin da na cika feeder da shi ba, ragewa nayi yayin da ruwan ya zuba a hannuna da 'kyar na samu na had'a musu madara ba yanda ma ya kamata ba, ina fara Basu suka 'ki sha suka fara sabon kuka, Abdul-malik nayi Abdul-hakim na amsawa, rasa yanda zanyi dasu nayi na saka su a gaba na fara hawaye, daga hawaye sai kuka sosai dama haka raino yake? Meyasa na kasa controlling 'ya'yan da na haifa a cikina? Yanda nake da son yara gani nake zan iya kula da 'yan biyar ma, saidai gashi tun kafin ayi nisa na fara gazawa.

"Wai yaya nake jin kuka ne ko bacci kikeyi?" Zubamin ido tayi ganin na saka yara a gaba ina kuka, matsowa tayi kusa dani tace "Bilkisu lafiya?"

"Mama bansan ya zanyi ba". Kuka sosai ya 'kwacemin tace "to ki basu nono mana".

"Tun 12 nike basu har na gaji, kuma na basu madara sun 'ki sha".

'Daukan madarar Mama tayi ta kalla tace "ruwa yayi yawa ta yaya zasu sha? Saidai a zubar a had'a musu wata".

Abdul-hakim ta d'auka ta goyashi sannan ta nufi toilet ta zubar da madarar, dawowa tayi ta fara had'a musu madara tana min bayanin yanda ake had'awa.

Abdul-malik na d'auka na fara feeding d'insa haka yasa kukan ya ragu, tana jijjiga Abdul-hakim ta gama had'a madarar sannan ta saukeshi ta fara bashi Madara, bayan d'an lokaci ya kar'ba muka samu d'akin yayi shiru.

Goge hawayena nayi tare da sanya ma Abdul-malik feeder shima, bacci suka fara mama ta kalleni tace "yanzu ke bakiji kunyar kuka ba?"

"Mama na rasa ya zanyi ne, tuj 12 nake fama dasu sama da awa kenan fa sannan suna kuka sosai a tare, sun rikita ni gaba d'aya na rasa me zanyi".

D'aura yaron hannunta tayi a kafad'a tace "Raino nutsuwa yake bu'kata Bilkisu, idan kina freaking out bazaki iya komai ba, tsaida hankalinki zakiyi wuri d'aya kar kiyi focusing a kan kukansu, kiyi focusing akan yanda zaki sama wa kanki nutsuwa ki sama musu".

NAYI DACE✔️Where stories live. Discover now