XXXXXV

1.2K 84 7
                                    

Na gama cire kayana na suna kenan Aliyu ya shigo, hugging d'ina yayi ta baya tare da sha'kar jikina yace " 'kamshin jego na daban ne, ina ma koyaushe zakiyi ta wannan 'kamshin".

Juyowa nayi na kalleshi daga underwear jikina sai bra nace "baka san masu jego 'karni suke ba? Kaima angon 'karni ne kuma ni nafi son 'kamshin jikina lokacin da bana jego".

Hannu na sanya na sa'kalo wuyansa ya matso da fuskarsa dab da tawa, numfashinsa na dukan fuskata yace "ya gajiyar suna?"

'kurawa lips d'insa ido nayi nace "ai na manta da gajiyar ma".

Murmushi yayi ya matso tamkar zai kissing d'ina sannan yace "dole ki manta da gajiya mana tunda kina kallon kyawawan lips d'ina". Ya 'kare maganar yana cizar lips d'insa, ban bashi amsa ba nayi pecking lips d'in nasa kafin yayi kissing d'ina naji gyaran murya.

Juyawa nayi naga twins sun rufe idonsu da hannunsu suna dariya da sauri na sakeshi yace "ku bud'e".

Ido d'aya suka bud'e Nawal tace "bamu ga komai ba".

Zama nayi kan gado ya zauna gefena yace "to meye ma dan kunga komai" ya sanya hannunsa daga bayana ya ri'ko 'kuguna, ture hannunsa nayi ya sake matsowa, 'ko'karin tashi nakeyi domin na fara jiyo muryar Mum da Inna idan suka ganmu a haka ai naji kunya.

Ko a jikinsa ya sake matsowa twins kuwa sun tsaya suna kallon live show, sallamar Mum naji yayin da na tashi ya rikoni, girgiza kai tayi tace "kun saka min babiesa gaba zaku 'bata su ko?, amal nawal kuzo mu tafi".

Jan hannun jariranta tayi ta fita tana murmushi Inna kuwa shigowa tayi ta zabga masa ran'kwashi tace " 'kaniyarka, ba nace kar na sake ganinka a wajen yarinyarnan ba sai tayi arba'in? Shine ko bi'kin bata gama ba ka fara cakumarta ko? Ki barshi ya sake d'irka miki wani cikin kece da wahala".

Turo baki nayi nace "Inna ban fa gayyato shi ba kawai ina shiryawa ya shigo". Mun riga mun saba haka sam Inna ta hana Aliyu zuwa wajena mu d'anyi love d'innan, da zarar yazo zata koreshi tace kar ya d'irka min wani cikin ko kuma ta zauna har ya gaji ya fita.

Ri'ke 'kugu tayi tace "ayyo, wato shiryawa kikeyi shine yana shigowa kika tu'be ko?"

Sum-sum ya fice ya barni a wajen na bishi da kallo, zaka yi bayani ne.

Zama tayi tace "nemi riga ki saka ni kin tsaya kina turo min nono".

Riga ta na zura nace "to Inna meye baki gani ba? Ai yanzu har zana ni zaki iya domin kin kalleni tsaf"

Duka ta kawomin na kauce muka yi dariya sannan tace "Bilkisu sai fa kin kula, Kar kiga ina korar mijinki kiji haushi saboda ke nake yi, namiji fa bashi da saiti a yanzu kika mi'ka masa kai hayewa zaiyi ya barki da wuya, kwainuka idan d'aya ne da sau'ki amma biyu akwai wuya".

"To Inna zan kiyaye amma ai nayi tazarar haihuwa".

Tagumi ta zuba tace " Ni Indo yaran zamani ana nuna muku annabi kuna rintse ido, to ai shikenan Allah ya kyauta, wato kinyi tazarar haihuwa saboda bazaki iya jurewa har kiyi arba'in ba ko? 'ya'yan zamani ina zaku kai zumud'i? Shiyasa mazan zamaninnan ke muku kallon banza".

Sunkuyar da kaina nayi nace "Inna ba haka fa nake nufi ba".

Abdul-malik ne ya fara kuka na d'aukeshi ina d'aukansa Abdul-hakim shima ya fara, suna fara kukan twins suna zo da gudu suna kokawar had'a madara,  amal na mi'kawa yaron hannuna na nufi toilet ina jiyo Inna na musu jaraba, kullum dai
haka akeyi a kwana bakwai d'innan.

'Dokin tafiya ta Kano kawai nake yi, Mum har ta lura da hakan tace "ina ganin kwana uku zuwanmu kano yayi nisa, gobe sai mu tafi".

Bance komai ba amma a ciki ji nake kamar nayi tsalle, ban raina abinda suka yimin ba domin naga iyakacin gata a wannan sunan, saidai ni ba haka na saba ganin hidimar suna ba, babu irin cika gidannan da akeyi ana aikin kayan miya da sauransu, babu haya'kin itace babu masu sabbin riguna da tsofaffin zani sun kama gaban tukunya suna tu'kin tuwo, babu kunun aya da zo'bo na leda, babu plates d'in roba ko irin shige da fice da yara keyi suna a basu abinci babu, komai anyishi silently  cikin gayu, bazaka ta'ba cewa ana suna ba sai kaje inda akayi decoration, ina zaune ake kawomin gaisuwa maimakon na dinga bin mutane ina gaidasu, nayi kewar rayuwar middle class d'in da nakeyi sosai.

NAYI DACE✔️Where stories live. Discover now