INAAYA 20💖

249 24 5
                                    

INAAYA💖






   Washegari karfe 7 inaaya ta tashi duk yawanci su basu tashi ba fitowa tayi daga dakin ta ta nufa dakin mamii ta tarar ba kowa dakin har an gyara shi Ac kawai ke tashi da kamshin turaren wuta zama tayi a kan  bed din for kusan 10minutes dan tasan mamii na closet definitely har ta tashi zata tafi sai taji an tura kofar closet din mamii ta fito sanye da wani voile blue da golden tasa sarkanta  da dan kunne da bangles na gold sunyi mata kyau ta fito da laffaya golden a hannunta tana ganin diyar ta ta tasakin mata murmushi inaaya tace "mamiii ina kwana, kinganki kuwa yanda kikayi kyau kaman ba ke kika haifa tsohon ya sa'id dinnan" dariya mamii abun ya bata sai tace "lafiya lau inaaya, har kin tashi, yo ai ba sa'id kadai ba sai ace yarana daga aneesah sai twins" pouting inaaya tayi tace "kaii mamii yanzu ni ya zaayi ace ba ki haifeni ba yar karama da ni" murmushi kawai mamii tayi mata sai tace "ke kin girma baki barin shagwaba dama tun jiya ina son nayi maki wani fada amma naga kun shiga busy ko" yar dariya tayi tace "wlh kuwa mamii" sai mamii tace "fatima" tana jin ta kirata da sunan ta ta san serious abu ne ta sha jinin jikinta mamii ta cigaba "kinsan ita a rayuwa kowa da yanda Allah ya tsaro mishi kuma duk abunda kaga Allah yayi maka ko miye ka gode mishi kila shine mafi Alkhairi a rayuwan mutun, ana so a kullum mutun ya zama mai tawakkali da abunda allah yayi ka rungumi kaddara hannu bibbiyu da mai kyau da mara kyau" tunda ta fara kan inaaya na kasa tana sauraronta sai mamii ta cigaba "kuma kinsan cewa mu iyayenki a kullum masu son ki ne kuma baxa mu taba abunda zaya cutar dake ba hope kinsani" kai inaaya ta gyada tace "eh mamii ai nima banida kamar ku amma mamii miye ya faru kike cewa haka" smiling mamii tayi tace "yayi kyau, to saida wani abu zan yi wa diyata fada? Hakanan fada ne from mother to daughter, Allah yayi miki albarka" murmushi inaaya tayi tace "to amin mamii yaushe ne flight din ku" mamii tace "karfe 10 ne shiyasa na shirya da wuri yanzu zamu wuce airport anjima kuma jirgin 4 ne InshaaAllah zuwa 5 dai muna abuja" inaaya tace "toh! Mamii'am Allah ya kiyaye hanya" ta amsa mata da amin sannan inaaya ta tashi ta nufa dakin ta tana zuwa taga duk sun tashi yawancin su har wasu sun fara wanka mimi tace "malama ya dai ina kikaje tunda safe" kallonta inaaya tayi tace "ikon Allah yanzu dan na bar daki sai anyi questioning dina to zance na fita" dariya ta basu kowa na dakin ya fashe da dariya inteesar tace "wayyo Allah cikina! Har naga inaaya na zance" sultaana ma dariya tayi tana cewa "hmm! Big show kenan" aleena dake kwance kan bed tace "lallai yara zakusha mamaki yo bata isa ba ko bata iyawa kuke nufi" haneefa tayi dariya tace "aa wai dai kawai dai" sukayi dariya ita kuwa inaaya daurewa tayi bata sake ce musu komai ba.karfe 1:00pm aka daura auren sameer sulaiman abubakar geidam da nabilah mujahid sidi akan sadaki dubu dari sosai sameer yake murna yana farin ciki bayan an gama suka je gidan su amaryan da abokanshi da cousins dinshi maza akayi hotuna karfe 3 bayan reception aka fara shirin tafiya airport saboda 4 ne jirgin, amarya tasha kuka sosai da za a tafi da ita tasaka wani alkyabba peach kawayenta su 10 da iyaye 10 da sisters dinta sukayi mata rakiya.





           Duk a gidan baffah suka wuni yau saboda wani dan kaman mothers day amaren sun sha lace kowa da irin nata da irin bridal veils dinnan masu kyau ga kida na tashi dj ya saki sauti gidan ya cika ya cika sosai daga waje har ciki saboda duk harda su mommy da Ammi da dangin iyayen su aleena da ummi suka zo anci ansha sosai anyi hotuna zuwa yamma duk mutane sun rage sosai. Karfe 5:40 su mamii suka sauka garin abuja daga kano da amaryar sameer nabila da kawayenta da iyaye da yan uwa gidan abbah aka nufa da ita inda mahaifiyar ango take da yan tarban amarya saida aka kaita wurin mama sannan sai gab da magrib aka kaita part din su naseer da aka gyare don ajiye amarya saboda anan zata zauna for the time being bayan biki zasu koma kano inda yake aiki da gidanshi a can.




               "Intee! Please kuyi sauri time is going ya khady just called" inaaya ta fada da karfi dan intee ta ji sun gama shirin su na dinner tsab! Anko ne wani fabric navy blue yayi kyau sosai brides world ta fidda masu anko din na sisters ne kawai fitted gown ne dinkin sai wani chiffon da aka sa ta gefe an sake shi yana jan kasa gown din tazauna mata sosai a jiki shape dinta ya fito sosai an daura mata head tie din nata very simple but elegant dan touch up ne a fuskanta amma tayi kyau ba kadan ba da dan clutch a hannunta silver da takalmi dan low heel su ma silver komai nata simple but classy she's the real definition of beauty komai nata MashaaAllah. Su inteesar da mimi da sultaana suka sauko suma duk da anko dinsu sunyi matukar kyau ba kadan  ba a tare sukayi waje suka tarar da ahmad yana jiransu dama sun ta rokinshi akan ya dawo ya kaisu bayan ya kai su aneesah motan suka shiga suka kama hanyan zuwa hall din suna isa suka fito ya khady suka gani wurin kofan hall din inda ake arranging for entrance din aneesah da saleema ne a gaba suma sun sha anko dinsu sunyi kyau sai ya aleena da ya hilal wani bustle gown tasaka grey yayi kyau sosai da silver jewelries angon yasa shadda ash da black hula da takalma sai bayansu friends dinta da abokan ya hilal sun jero sai su inaaya suka jero sai ya ummi itama bustle gown me fabric din milk da maroon  da head dinta maroon angon yasa brown shadda sai kawayenta da abokanan ango a bayansu sai su khady sai ya aleesha itama bustle gown ne fabric din nata cream da purple sai purple head ango yasaka white yadi na maza mai kyau sai baya kawayenta da abokan ango, haka sukayi entrance din nasu yayi kyau har amare suka iso inda aka tanadar masu su zauna friends ma kowa ya zauna kan table din friends aka fara event ansha rawa har couple dance aka kira amare aka saka masu say you won't let go by  james arthur sukayi wani slow dance anci ansha sosai ba kadan ba wurin grand dinner dinnan komi kakeso zaka samu foods,snacks,desserts komai dai da pictures sosai sun gayyaci big h studio yayi covering event din the dinner was grand, fun and enjoyable sunsha rawa sosai. Aliyu tunda yaje wurin dinner din zaune yake wuri daya yasa wani shadda sky blue mai kyau kaman shima angon ne tare da fareed da sauran cousins dinsu suka zo bayan sun dawo daga daurin auren sameer, shiru yake yana ta kallan yanda suke ta rawa cikin rawan ya hango su inaaya inteesar nasaka ta dole tayi rawa idonshi was fixed on her ya kalleta sama har kasa ya dan tabe baki baice komai ba, Sai 12 aka tashi daga wurin event din suka koma gida a gajiye sosai suka gama sallah suka yi shirin bacci sannan suka zauna suna ta fira ana maida yanda akayi sai wurin 2 sukayi niyyan bacci kowa yayi bacci banda amaren da duk sun kasa bacci kwance kawai suke amma ba bacci aleena ta tashi ta shiga toilet ta dauro alwala ta fito ta kabbara sallah tayi nafila 2 raka'ats ta gama tana ta adduan zaman lafiya da kwanciya hankali ummi da aleesha ma suka tashi duk suka dauro alwalan sukayi nafilan nasu sannan suka samu bacci ya dauke su, karfe 3:30am inaaya ta farka saboda duk a takure take baccin duk bata jin dadi ta rasa me yake mata dadi ta tashi zaune ta kwanta har kusan awa daya sannan ta shiga tayo alwala tazo ta kabbara ta dinga salloli har kusan asuba sannan ta bude drawer ta dauko qur'ani ta fara karantawa a hankali har aka yi kiran sallah sai ta rufe ta tashi ta gabatar da sallahn ta sannan ta fara tada yan uwan nata duk sunyi mamakin yanda batayi bacci ba tace masu kanta ke ciwo kawai sannan ta koma ta kwanta bacci ya dauketa wurin 8:00am ta tashi saboda haya niya duk kowa ya tashi taga anty fareeha a dakin tana saka su aleena su tashi suyi wanka su gama shiri ayi masu makeup yanzu lokaci ya kusa 12:00pm ne daurin auren a an noor mosque, jiki a sanyaye duk suka tashi kowacce daka ganta kasan jikinta yayi sanyi don sunsan yau duk za a kai kowacce dakinta haka suka tashi jiki ba kwari mai gyaran jiki tazo tayi masu na karshe sannan duk suka shiga wanka a different bathrooms din gidan.











Hello lovelies❤️ finally nikah day! Hope it ends well.

Please please and please don't forget to
VOTE
COMMENT
FOLLOW AND
SHARE

LOTS OF LOVE❤️🔐

INAAYA💖Where stories live. Discover now