INAAYA 23💖

242 28 8
                                    

INAAYA💖










           Karfe 4 har sun shiga jirgi zuwa gombe da kawayen amarya da yan uwan mahaifinta sai anty fareeha, sai feenah, aneesah da saleema sai yan dauka amarya, amarya tasha kuka bayan sun isa gidan baffah sukayi pictures da iyayensu mata wurin karfe  3:20 duk aka saka suka canza kaya wani filtex atamfa suka saka da lafayya ba makeup a fuskokinsu duk sun goge aka kaisu parlour wurin su baffah harda mahaifin aleena da na ummi fada da nasiha akayi masu sosai sannan aka nufa dasu wurin iyayen su mata su ma suka dora da nasu aleena tasha kuka da kyar aka rabota da jikin ammi tasha kuka sosai, haka itama ummi tasha kuka sosai ba kadan ba itama ta rirrike mommy sai aleesha itama haka sun sha kuka har da sisters din nasu su khady duk sunsha kuka baffah da kanshi ya kai aleesha gidanta bayan an tafi da ummi da aleena  a gidan ta da ke karsana east a garin abuja  kawayenta da iyaye suka rakata bayan baffah ya kaita.




             Karfe 5 akayi budan kai na amaryar sameer a gidan abbah dayake akwai fili sosai duk dangin da suka rage sun halarta budan kai din su khady ma duk sun je banda su mimi da suke can gidan su inaaya sai lallashin kawar tasu sukeyi tana kuka. Alhamdulillah an watse taron budan kai lafiya sai kuma shirin dinner da za ayi a daren rannan kowa ya tafi domin yin shirin shi na dinner amaryan ma da kawayen ta da danginta duk suna can zasuyi shiri. Aliyu tunda ya koma gida ya shiga part dinshi ya rufe da key ya sakan ma kanshi shower ya kwanta idanunshi rufe amma ba bacci yakeyi ba kawai tunanin halin rayuwan nashi yake yanda zaya koma yana tunanin yanzu ya su abbah suke so yayi taya zaya fara kallon karamar kanwarshi wadda sanda aka haifeta da wayanshi ya dauketa a cikin shawl amatsayin matarsa ta ina suke tunanin zaya iya zaman aure da ita? Duk tunanin da yake kenan ya ma rasa ya zaiyi har magrib tayi ya tashi yayi sallah ya kwanta again sai ga ammah ta shigo dakin dauke da kulolin abinci da kyar tasaka aliyu dole yaci abinci kadan sannan tace ya tashi ya shirya dinner din dan uwan nashi, badan yaso ba haka ya tashi yace to sannan ta fita daga dakin.


          Su inteesar sun sha lallashi har suka godewa Allah itama dai inaaya tayi kuka idanunta sun kumbura sunyi ja ga fuskanta yayi ja ga ciwon kai da wani zazzabi da ya taso mata tayi kuka har ta godewa Allah ta hakura tayi shiru har magrib yayi sukayo alwala kowa yayi sallah inaaya ta jima kanta kasa wurin sujjada tana kai ma Allah kukanta, ta gama suna zaune mamii ta shigo da mai aiki a bayanta da kulolin abinci ta jera ta tafi sai mamii dukkansu hudun tasaka su dole su ci abinci suka samu suka tuttura, da ka kalla inaaya sai kaga canji kaman ba ita ba sai mamii tace duk suyi shirin dinner zaa tafi amsa mata sukayi da toh! Banda inaaya ta tace "mamii dan Allah ku bar ni a gida" hade rai mami tayi duk da tausayin yar tata tace bata zama gida hawaye na ziraro mata tace "mamii dan Allah ki bar ni na zauna kaina na mun ciwo kuma ina jin daci a zuciyana" mamii daurewa kawai take batayi breaking down ba ta tashi ta fita ta dawo da magani taba inaayan ta sha sannan tace su shirya yanzu zata samu sauki ba yanda inaaya ta iya haka suka tashi sai bayan sunyi sallar isha sannan suka fara shiri wani anko ne sukayi na sisters ash color da head ash yayi kyau sosai suka saka kayan nasu inaaya dai bata so ba haka ta saka kayan mimi ta daura mata head din yayi kyau simple gown ne kasan shi kaman fish sai abun peplum wurin gaban rigan, makeup sukayi sunyi kyau banda inaaya da ko kwalli babu a idanunta saida mimi ta takura mata sannan ta barta ta dan gyara mata fuskan ta tayi normal kaman ba ita tasha kuka ba tayi kyau sosai sai sultaana tace yakamata muyi pictures nan suka fara clicking pictures inaaya dai daka ganta batada walwala. Sun sauko kasa gidan duk an gyara ba mutane kaman ba shine aka sha hidima ba suka tarar da mamii ta gama shirin nata itama ta kallesu sunyi kyau sosai sai ta kalla inaaya tace mata "inaaya ina zaki fita haka?" Kallon mamii tayi na rashin fahimta sai mamii tace "wuce ki je ki nemi gyale ki saka" wasu irin zafafan hawaye taji sun zubo mata da gudu tayi sama tana taresu bata san tayi kuka closet din ta nufa ta bude side din veils ta dauko wani ash medium veil ta yafa shi duka a jikinta sannan ta sauko kasa aminnan nata na mata kallon tausayi sai mamii tace to su tafi suka shiga mota suka nufa event centre din. Inaaya zaune tayi cikin mota akan ita bazata shiga ba saida mamii tayi mata fada sosai sannan ta fito suka shiga tare dasu mimi suka samu seat table daya suka zauna dukkansu shiru tunda suka zauna amarya da angon suka shigo suka zauna sunyi kyau they looked so happy and cute together event ya fara saiga yayyen nasu maza sun zo ciki harda aliyu da fareed aliyu yasha wani shadda ash color da matching hula da black takalma yayi kyau sosai suna shigowa fareed ta taboshi yana nuna mishi inaaya a hankali yace "perfect couple look har kaya same color kuka saka" aliyu baice mashi komai ba yayi gaba zuwa table din da akayi masu reserving suka zazzauna coincidentally inda ya zauna yayi daidai da inda inaaya take zaune dayake table din side by side suke nan fareed abunso ya samu ya dunga tsoka nan shi har waya ya jawo ya dunga snapping dinsu countless pictures ita kuwa inaaya yana zama tun bata san waye ba kamshin turarensa ya daki hancin ta saida zuciyan ya buga. Event din passed before you know it, it was enjoyable banda inaaya da ko tashi bata yi ba har saida aka gama sannan suka tashi tafiya gida wurin karfe 11:00pm.

          Duk sunyi shirin kwanciya suna zaune a daki mimi tace "yanda Allah ke abubuwan shi daban ne wlh ni ji nake kaman it's all a dream zaa tada mu mutashi" sultaana tace "seriously har yanzu I'm finding it hard to believe" inteesar ma tace "yeah kaman a mafarki wallahi" inaaya dai duk da ido ta bi su dan itama bata yadda da abun ba haka sukayita fira  jefi jefi su kadai har bacci ya daukesu inaaya kuwa sam ba bacci a idonta sai wani kishin ruwa taji ta tashi ta sauko kasa ta yafa veil saman pj's din ta zata dauka ruwa saboda babu ruwa a fridge din dakinta haske tagani parlour tazo zata wuce taji muryan daddy yace "mamana" a hankali ta tako zuwa parlour wurin daddy taganshi zaune da ya sa'id kusa da daddy ta samu ta zauna daddy yace "fushi mamana takeyi dani ko" shiru tayi batace komai ba yace "kiyi hakuri ki bar fushi da daddynki komi kika gani Allah ya tsaro babu yanda za muyi nasan ke me hakuri ce da biyayya kuma InshaaAllah zakiga sakamakon biyayya nan gaba, ke da aliyu duk yarana ne kuma duk nasan halayyarku kuma i can assure you aliyu ba zaya taba cutar da ke ba baya da matsala saidai kowa 9 yake bai cika goma ba da kun yi hakuri kun zauna da juna zaku ga ribar abun" hawayen daya sauko mata ta goge tace "daddy ni ba fushi nakeyi dakai ba" murmushi yayi ya dan yi hugging diyar ta sa yace "mu iyayenki ne a kullum masu sanki ne bazamu taba cutar da ke ba forget sa'id aneesah and twins you're the real favorite" sa'id dake dayan kujeran yayi gayaran murya yace "daddy i can hear that" duk dariya sukayi a tare whole heartedly tayi dariyan wanda duk a ranan yau bata yi ba sa'id ya dawo inda suke ya yi hugging din inaaya yace "don't be unhappy baby sis daddy is right everything happens just as Allah planned have sabr it'll be good InshaaAllah" murmushi tayi ma ya sa'id ta amsa masa da yes sai ta tashi tace dasu ruwa zata dauka ta tafi daki tayi masu saida safe ya sa'id yace "ohh abun mamaki lil sis is all grown up it's unbelievable yanzu daddy before you know it sai ka fara ganin yan jikoki na yawo ace yaran inaaya ne wow!" Dariya daddy yayi ita kuwa inaaya ta bata rai tana turo baki sai daddy yace "sa'id kar ta takura wa mamana fa kaima kaine next saida kaji mun daura maka auren" gwalo tayi mishi ta nufa kitchen ta dauko ruwa tazo ta wuce daki tasha ta kwanta nan da nan bacci ya dauketa.









Hello dearies❤️ so I think our inaaya is already accepting fate she's so strong 💪

Please please and please don't forget to
VOTE
COMMENT
FOLLOW AND
SHARE

LOTS OF LOVE❤️🔐

INAAYA💖Where stories live. Discover now