SAUYIN RAYUWA

1.9K 59 4
                                        

🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
   🕊 SAUYIN RAYUWA 🕊

💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞

  Story
           And
                   Written✍🏻
                                  By
Salma Mas'ud Nadabo 👑

      
    🌲 *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*🐄
   ('''We are the best among the rest ''')

https://mobile.Facebook.com/Real-hausa-fulani-Writers-forum-RHFWF-173984973194167/?refid=52&ref=opera-speed-dial&_tn--=H-R

Email:realhausafulaniwriters@gmail.com
Facebook: www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITERSFORUM.com

  *GARGAƊI*
'''Ban yadda a juya min wannan labarin ba, ta kowace hanya, ba tare da izini na ba, don haka a kula a kiyaye.  '''

TUNATARWA
'''Labarin dake cikin wannan novel ɗin ƙagaggen labari ne dan faɗakarwa da nishaɗantarwa haka kuma suna yanda ke ciki|'''

'''BISMILLAHIRAHAMANIN RAHIM'''

Free page

Page: 01*

Wanke-wanke ne jibge a tsakar gida Wanda ko gidan biki ne sai haka, yarinya ce wadda baza ta wuce shekara goma shahudu ba, zaune saman kujera tayani gulma, ta tasa wanke-wanken gaba, sai sharar ƙwalla take inda sabo ya kamata a ce ta fara sabawa da wannan baƙar wahalar, kallo ɗaya zaka mata kasan a wahale take, ko kayan jikin ta sun sha ruwa  har sun gaji, yar riga da zanine sun mata yawa saboda tsabar rama, ko ba'a fadama ba kasan yunwa na galabaitar da ita, fara ce amma saboda tsabar wahala  tayi jirwaye  bama a gane farin sai ta daga wuyan ta, tana ɗauke da dan siririn hanci da baki dan qarami pink, duk da kodewar da tayi hakan bai hana aga kyan da Allah yayi ma *Nihal* ba,

    Tsawar da aka daka mata ce ta sata ɗagowa a razane, cikin ɗaga murya indo ta ce, "dan uwar ki uban me kike da har yanzu kin gaggara gama wanke-wankyen nan ba."

  "Shegiya mai ruwan maita, kiyi ƙoƙari kisa na rasa cinikin safe, dan wallahi bazan lamunta ba" goge hawaye  Nihal tayi tare da cigaba da wanke-wankyen da takeyi, dan sarai tasan wacece Gwaggo indo, dan ba yau ta saba rufe ta da duka ba.

     Cikin sauri ta samu ta sauke kwanikan ta kai su ma'ajiya, qoqarin bude  daki take, gwoggo ta daka mata tsawa keeee!!!.. Birki Nihal taci ta juyo cike ta fargaba tana zare ido, harara Gwaggo ta aika mata ta ce, "me kike nufi da haka? sai kin gama taɓa ƙazamar uwar taki, sannan zaki dawo ki sheƙamin koko"?

   "Masu siya susha su mutu kenan tunda ba uwar ki keda asara ba ko, aiko zan gwada maki kuskuran da ki  kayi na ƙoƙarin  shiga ɗakin Hansatu."

     Janyota gwoggo tayi kiii ta soma jibga  sai da ta mata lilis sannan tayi kwallo da ita kanta ya daki bango,  qara sakin kuka Nihal tayi, Gwaggo kuma sai faman  haki take ta ce, "narantse da Allah daga ke har Hansatun ba wadda ta isa ta ƙasarani wallahi uban kuma ya ja da mu ya zama gawa bale ku wallahi ƙarya kuke,"

    "Bari malam ya dawo shima zanji dalilin aje min ku a gida, da bai watsa Ku almajiran ci ba daga ke har uwar taki"

  "Na baki nan da yan mintina ki sheƙa koko, in kuma ba haka ba jikin ki ya gaya maki" sannan gwoggo ta ja dogwan tsaki tana qoqarin shigewa ƙurya ɗakin ta, lallausan murmushi ta saki kamar ba ita ke hargowa ba ta ce, "a'a yar baba har antashi kenan"
     "Eh wallahi Gwaggo" Saratu kenan ɗiyar Indo wadda ta daurawa san duniya ko tsinke bata so ya taba ta bale mutum.

Kuka ne ya kubucewa wa Nihal tace , "astagafurillah Wannan wani irin *SAUYIN RAYUWA* ne" jiki ba ƙwari ta miqe tare da Shiga madafa tana sharar ƙwalla, Saratu ta bita da harara.

     Duk Wannan tijarar da Indo ta gama, duk a kunnan Umman Nihal  tayisu wasu hawaye ne masu zafi suka sulalo mata.

    Ba ta taɓa tunanin ko a mafarki Ahalin  *Tanimu* zasu wulaƙanta su ba amma sai gashi yau  mutuwar malam taja masu  tabbas sun ga *Sauyi Rayuwa*

SAUYIN RAYUWAWhere stories live. Discover now