SAUYIN RAYUWA

376 19 1
                                        

🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
          🕊 *SAUYIN RAYUWA*🕊
💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞

*Story*
    *And*
       *Writing*✍🏽
             *By*
*Salma mas'ud nadabo*👑

🌲 *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*🐄
('''We are the best among the rest''')

*_Ashe dai haka SAUYIN RAYUWA ya tara d'inbin masoya naji dadi sosai da kulawar ku  a gare ni kuma hakan ya qaramin karfin gwiwa yadda zan cigaba da suburbudo maku posting kamar yadda kuke so_*🤪

*Page: 35_36*

Dakyar Nihal ke takawa saboda wani irin jiri dake d'ibar ta ga wani irin nauyi da farantin talla ya mata a haka ta samu ta k'araso har inda suke haduwa da yaya, ko da ta zo wajan ba kowa sai baba mai gadi  data hango yana zaune saman kujera shi kamar kullun, dakyar  ta iya takowa har wurin shi tunda baba mai gadi ya hango ta yake ta washe baki saboda da ya hango Nihal yasan yau gidan shi ba kwanan yunwa, ganin ta k'araso wajan shi ya sashi tashi a kid'ime saboda yanayin da ya ganta a ciki gefen bakin ta a fashe jini na  zuba fuskar nan  tayi jawur ta kunbura, tausayin tane ya lullu6e shi tare da tanbayar ta  cikin nuna tausayi ya ce, "Nihal me ya sameki ? maganar  da  yayi ma Nihal ce tasa ta sakin kuka a hankali ya shiga bata hakuri  duk da bai san dalilin yin kukan nata ba amma dai koma menene yasan irin bak'ar wahala da Nihal ke sha a hannu marik'in nata, jawo hannuta yayi tare da zaunar da ita saman tabirin da  yake zama sannan ya aje farantin ta gefe dan ya lura tsayuwar gagarata take nemanyi,  har Nihal ta zauna bata ce ufan ba sai ajiyar zuciya da take faman saukewa, baba mai gadi ne ya ce, "sannu kinji Nihal bari na kira maki yayan naki ai yana ciki" daga mashi kai Nihal kawai tayi da sauri shi ya k'arasa yana ayana yadda aka maida fuskar Nihal kamar lauje dan duka a dai-dai bakin kofar parlour yaci karo da yaya wanda ke k'ok'arin fitowa sanye yake da shada light  brown tasha aiki da dark brown zare haka hula dake kanshi light brown colour ne da ratsin dark brown ba k'aramin kyau ya zubaba sai kamshi yake zubawa ganin baba mai gadi ne ya sasa tsayawa yana sakin k'ayatacan murmushi wanda fararan hak'oran shi suka bayana, ko da baba mai gadi ya k'araso jiki shi a sanyaye kamar an zare mashi laka ganin haka yasa yaya tambayar shi lafiya tun kafi yayi magana ya ce, "baba  Allah yasa lafiya dai?
      "Eh to lafiya ba lafiya ba yarinyar nan ce Nihal ta zo kamar wadda tayi hadari," ko ida  ji zancan yaya baiyi ba ya wuce baba mai gadi da sauri ya fita, ida baba mai gadi ya bar Nihal  har yanzu nan take sai dai wannan karan kanta na bisa cinyoyin ta, ta dunk'ule waje d'aya tana faman sauke ajiyar zuciya, da sauri yaya  ya k'araso tare dayin kneel down dai-dai saitin Nihal a hankali yasa hannu yana dago da fuskar Nihal wadda a lokaci ta k'ara kunbura rintse idanuwa yaya yayi tare da ware su kan fauskar Nihal  cikin rudewa yana cewa, "k'anwata waya makin haka?  duk wadda ya maki haka bai kyauta ba wannan wani irin laifi kika aikata da za'a maki irin wannan horan" kuka kawai Nihal ke shek'awa musanman taga yayan nata wanda take mashi shagwaba yadda take so kukan da Nihal take shi ya k'ara rikita yaya sai fama lallashin ta yake, cikin sanyi murya ya ce, "ya isa mana kukan kiyi hakuri kijin k'anwata bari na fito da mota na kai ki asibiti kijin" daga mashi kai Nihal tayi ciki gida yaya  ya koma ya ya janyo hadadiyar motar shi luxus me  tsada gaske baba mai gadi ne ya wangale mashi gate ya fito sai da ya  zo dai-dai saitin Nihal yayi parking tare da zagayowa ya bude mata murfin mota, zaro idanuwa Nihal tayi tana kallon motar duk da zafin ciwo da take ji qin tasowa tayi sai idanuwa da dake ta faman rabawa ganin irin yadda take yasa yaya k'arasawa tare da kamo hannuwata sai fama titila idanuwa take cikin rawar murya ta ce, "yaya na warke wallahi," dariya abin ya so bama yaya amma sai ya hade rai ya ce, "shiga muje asibiti zan kai ki kijin" make kafa ta kumayi tana san zame hannuwan yaya daga rukwan da ya mata, ita Allah na gani bata iya shiga wannan motar ace mota  duk bak'i har da window's ai bama zaiyuyu ba ta bishi duk Nihal na wannan zancan azuciyar tane, kamar yaya yasan tunanin da Nihal take ya ce, "tsoran shiga motar kike ko? Saboda bakin tinted" kallon shi Nihal tayi dan ita bama tasan me tinted din ba, cike da kauyanci Nihal ta ce, "me kuma hakan yaya" dariyar da yaya yake ta boyewa ce ta kubuce masa  sakin baki Nihal tayi tana kallon shi ganin bai daina dariyar bane yasa Nihal sakin kuka shuru yayi yana kallon ta  murmushi ya saki tare da ja mata hanci ya ce, " ke ko wallahi kin iya rigima wannan mijin ki ya bani da rigima shiga muje a duba min lafiyar ki haka nan za'a lalatawa yar k'anwata kyakyawar fuskar ta da duka," murmushi Nihal tayi bata ce ufan ba ta shige motar tana dari-dari rufe murfin motar yayi tare da zagayowa ya shige  motar ya ja su, a hankali yake tukin duk bayan mintina yana kallon Nihal wanda sanyi AC motar ke san sata bacci, isowar su harabar asibitin yasa yaya gyara parking sannan ya 6ale murfin motar  ya zagayo ya  budewa Nihal, ko da suka shiga asibiti office din Dr suka shiga dressing aka mata sannan aka mata alura wadda sai da aka sha fama dan dakyar ta tsaya, sannan Dr ya basu magunguna  tunda Nihal tasha alura take aikawa yaya harara da murguda mashi baki sai faman kumbure-kumbure take a dole fushi take da shi, abinma dariya yake bashi Hakan ma da take ba k'aramin k'ara mata kyau yake ba, har suka zo shiga mota ba wanda yace k'ala bude mata murfin motar yayi  ta shiga sannan shima ya shige bai zame da su ko ina ba sai wurin shitu me tsire a nan ya siyi tsire sannan ya shiga shagwan kusa da shi ya siyo lemo masu sanyi, ya dawo back seat ya bude ya aje ledojin sannan ya dawo ya zauna mazaunin driver har lokacin  Nihal  fushi take da shi, a hankali ya daura hannuwa shi saman na Nihal dago idanuwa tayi suna kallon juna shagwabe fuska yaya yayi ya zama abin tausayi ya ce, "please ayima yaya hakuri a daina fushi da shi haka mana please" ya ida zancan yana shagwabe fuska dariya Nihal ta saki tana cewa, "dama manya na shagwaba yaya?
    "Eh mana  manya na shagwaba musanman idan yaya yayi ma k'anwa laifi" ya ida zancan yana jan cheeks din Nihal, dariya Nihal ta kuma tintserewa da ita tana cewa, "amma gaskiya yan birni ke haka  gaskiya mu nan kauye ba namijin dake shagwaba" murmushi yaya ya saki ya ce, "Dan Allah?
     "Allah kuwa"
"ta6 muko birni kowa na shagwaba" yayi maganar cikin sigar wasa kamar yaro washe baki Nihal tayi ta ce, "Kasan wani Abu yaya?
  " a'a sai kin fada"
"gaskiya yaya ni dan birni zan aura," dariya yaya ya saki yana mai cigaba da tukin da yake ya ce, "ah lallai k'anwata ta fara zama yan'mata" rufe fuska Nihal tayi ala dole tana jin kunyar yaya  dariya sosai yaya yake ya ce, "karki damu indai dan birni ne kin samu ni da kaina zan zaba maki miji ko ki fada min irin wanda kike so na samo maki  me hankali da nutsuwa wadda zai kulamin dake," murmushi kawai  Nihal tayi, janta fira sosai yaya yayi har suka k'araso gida tunkafin ya shiga da mota cikin gida Nihal ta sauka shi kuma ya k'arasa da motar ciki, bayan yayi parking ya dawo inda suka saba zama dauke da ledoji a hannun shi sai da suka k'ara gaisawa da baba mai gadi ya k'ara tanbayar shi me jiki sannan shima ya mik'a mashi ledar dake hannu shi guda daya sannan ya k'arasa wajan Nihal wadda ke zaune tana wasa da yar tsuntsuwa isowar yaya ne yasa yar tsuntsuwar tashi sama, murmushi ta saki ganin yaya zama yayi sannan ya bude leda d'aya ya ce, "oya matso ki sama cikin ki wani abu nasan kina jin yunwa" washe baki Nihal yi tare da janyo ledar lafiyayan tsirene yaji albasa da tumatur da k'uli gefe guda kuma ga mango juice , wani miyau Nihal ta hadiya tare da gyara zama ta faraci hannu baka hannu k'warya yaya na kallon ta wani irin tausayin tane ya lullu6e shi insha Allah sai ya fida ta daga cikin wannan kuncin wannan promise yayi ma kanshi, daina cin da tayine yasa yaya tanbayar ta ya ce, " kanwata kar dai ki ce min har kin koshi so kike na maki dure ko,? idanuwan Nihal ne suka kawo ruwa ta ce, "yaya inata cin dadi na manta da umma na gaskiya ban kyauta ba ko yaya,? Murmushi yaya yayi ya ce, "to yar  umma ai umma ba taki bace ke ka d'ai nima na aje mata karki damu ki cinye wannan nakine," murmushi Nihal ta saki ta mai godiya a gaskiya bata da abinda zata ce ma yaya shiyasa ta aje shi waje na musanman ita ko tayi ma kanta alk'awari duk randa yaya ya nemi wani abu a wajanta zata mashi sai dai inya sabawa shari'a musulinci ne ba zatayi ba.

SAUYIN RAYUWAWhere stories live. Discover now