🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🕊 *SAUYIN RAYUWA*🕊
💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞
*Story*
*And*
*Writing*✍🏾
*By*
*Salma mas'ud nadabo*👑🌲 *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*🐄
('''We are the best among the rest''')*Page: 49_50*
D'ago da fuskar Sultan Alex yayi yana jinjiga shi yana cewa, "Sultan...!!!! Cikin d'aga murya gabaki d'aya gidan sai da ya amsa da muryar Alex d'aukar Sultan yayi cak fadawa na biye da shi, Sinbul ne yayi sauri daukar waya dan kira Doctor, tuni labari abinda ya faru ya gwaraye gidan sarki da gidan waziri, waziri na kwance yana bacci matar shi na mak'ale a jikin shi ya fara jin bugun k'ofa zame Adda yayi daga jikin shi tare da mik'ewa a hankali ya nufi k'ofa ya bud'e ganin bafadan shi Hassan ne yasa waziri zuba mashi idanuwa yana saurare cikin rawar murya ya ce, " Ranka yadad'e Sultan..! bai ida jin sauran bayani ba ya koma ciki ya sanyo kayan shi Adda na cewa, "lafiya? tabi bayan shi cikin sauri suka nufi cikin gidan sarki.
sarki na zaune da Gimbiya jalila a turakar sa kasancewar yau ita ke da girki tana ta zuba mashi kisa da kisisi na k'wankwasa kofar da akayi ne yasa Sarki zame jikin shi daga na Gimbiya jalila kasancewar suna like da juna light kiss ya manna mata a lips sannan ya mik'e, jin alamar takowar shi yasa waziri wangale kofar kanshi a k'asa idanuwan taf da kwalla yace, "ran ka yadad'e Sul....!! bakin sarki na rawa ya ce, "don't you tell me wani abu ya sami d'ana" Sarki ya fad'a cikin d'aga murya, bakin waziri na rawa yace, "mai...!! D'aga mashi hannu sarki yayi tare da komawa bedroom ko ta kan Gimbiya jalila bai biba mik'ewa tayi tana cewa, "lafiya kuwa ran ka yadad'e ? Alkyabba shi ya zura yana ce mata, "Sultan ne ba lafiya," waro idannuwa tayi tana cewa, "bari na biyo ka" ko saurara ta baiyi ba ya fice fadawa na take mashi baya, yana fita Gimbiya jalila tayi far da idanuwan ta ta bushe da dariya tare da fad'awa saman bed tayi d'ai-d'aya tana cewa, "aikin ka na kyau Ashad ashe dai d'ana bana wasa bane jar uba.! duk wannan maganar a fili take yin ta alkyabba ta jawo da sauri ta daura ta saman night dress din ta, ta murza idanuwan ta dan sunyi ja tana fitowa suka had'e da yakumbo far tayi mata da idanuwa tare da sakar mata murmushi kusan dai duk maganar da sukayi da idanuwa da baki sukayi ta saboda tsabar mugun hali.Bangaran Sultan doctor Amir har ya zo ya fara bashi taimakon gaggawa dan Sultan ya zubar da jini da yawa sannan Dr amir ya mashi dinkin har a lokaci Sultan bai san inda kanshi yake ba, sannan Dr amir ya daure mashi cikin da bandeji, Maimartaba na isowa umma Sultan ta fad'a jikin shi tare da sakin kuka tana cewa, "kaga za'a kashe min Sultan d'ina maimartaba" ta ida zancan tare da k'ank'ame sarki, rungume ta sarki yayi tsam a jikin shi yana shafa bayan ta yana cewa, "shhh ya isa insha Allah Sultan will be ok my dear," Gimbiya jalila da isowar ta yanzu ganin yadda sarki ya k'ank'ame Gimbiya Nadiya sai da hakan ya 6ata mata rai kukan munafirci itama ta saki maimartaba ganin haka yasa ya dafa goshin shi yace, "ya Allah" jawo Gimbiya jalila yayi itama fafad'an kirjin shi yana lallashi su haka sukayi lamo a jikin shi Gimbiya jalila ko yau zuciyar ta fes ba tak'i Sultan ya mutu a daran yau ba kowama ya huta fitowar doctor amir ne ya katsewa Gimbiya Jalila tunani da sauri maimartaba ya k'arasa yana cewa, "ya jikin Sultan? Dan murmushi Amir ya saki tare da cewa, "Alhamdulillah insha Allah daya farfad'o komai zai zama Normal," murmushi sarki ya saki yana cewa, "masha Allah" sannan suka d'unguma suka shige dakin Sultan wanda yake kwance bai ma san duniyar da yake ba.
Labari na kaiwa ammi hawan jinin ta ya tashi har sai da Doctor Amir ya dubata tare da yi mata alura bacci jakadiya Dara na zaune da ita, Nazili na kwance Azizi ta bude kofar bedroom din ta a hankali ta shiga tashin ta, a hankali Nazili ta bud'e idanuwan ta cike da masifa ta ce, "lafiya malama kin zo kina tashi na daga bacci da wannan daran ni sa'ar ki ce,? Jikin Aziza na rawa ta zayanewa Nazili abinda ya faru, A zabure Nazili ta jawo sleeping robe din ta tasa tare da nanad'e gashin kanta, ta fita daga bedroom da sauri, a dai-dai shiga part din Sultan ta hade da Basmal da Minal da Shukura suna sharbar kuka zasu shiga itama kukan take Nasim ne kawai babu da Ashad, Nasim ko nisan bacci yayi Ashad ko yana can hankali kwance, suna shiga dakin Sultan bakin bed din shi suka nufa, maimartaba yace, "ya kamata kowa ya koma part nashi tunda Sultan abin ya zo da sauki" sannan ya kira waziri tare da sheda mashi yana so abin ci ko mashi koma waye yake kawowa Sultan hari tun yana k'aramin sa kuma wannan karan ya d'au alwashi ba inda zai fida Sultan sai dai ayi kare jini biri ji da masu kawo mashi hari kuma duk wanda ya kama da sa hannu shi a gidan sai ya fuskan ci horo mai tsanani .

YOU ARE READING
SAUYIN RAYUWA
Romancekuka ne ya kwacewa NIHAL tana furta duk addu'ar data zo bakinta wannan wace irin RAYUWA ce yaushe ne zata samu SAUYIN RAYUWA da gata kamar ko wace 'ya, raban ta da wani abu sh farin ciki tun bayan rasuwar mahaifinta. bana tunanin akwai w...