🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🕊 *SAUYIN RAYUWA*🕊
💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞
*Story*
*And*
*Writing*✍🏾
*By*
*Salma mas'ud nadabo*👑🌲 *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*🐄
('''we are the best among the rest''')*_godiya gare ku masoya na abin alfahari na ina mik'a gaisuwa a gare ku masoya, wannan littafi nima ina sanku irin sosai din nan damu biyo ni ta private da masu comments ta group duk ina gaishe ku wannan shafin naku ne kuyi yadda kuke so da shi_*
*Page: 51_52*
Gidan waziri shirye-shirye ake sosai na tarbar ammar sai hada-hada bayi suke suna kai kawo, waziri ne ya fito yana gyara zaman rawanin shi tare da kallon Adda yana murmushi ya ce, "yau fa ba zama tunda ammar zai dawo ko shirya ni kin kasa yi nama fara kishi," Murmushi Adda ta saki tana cewa, "haba ranka yadad'e ni na isa nak'i shirya d'an tsoho miji na kawai dai ina so idan ya dawo ya ji dadi tarbar da zan mashi tunda ya dad'e baya gida,"
"Kuma fa haka dan gaskiya ko ni ina missing ammar,"
"Yauwa dama ina so anjima na lek'a Sultan da jiki"
"Toh shikenan, ni wallahi yaron nan tausayi yake bani ace aita farautar ran mutum kamar wata daba"
"Nima dai abin nan na daure min kai ran ka yadad'e ace aita abu yak'i ci yak'i cinyewa kamar cin k'wan makauniya"
"Ke ma dai kin fad'a bari na k'arasa fada"
"A dawo lafiya Allah ya tsare min kai"
"Ameen Gimbiya ta"****
Bayan Nihal ta sha kukan ta ta gaji ta ja jiki ta shige gida, wani irin mugun kallo gwoggo da Sara suka watsa mata gwoggo ta ce, "uban waye shi wanda ya zo duba ki,? har nake jin ana fad'i mashi wani suna," shuru Nihal tayi tana raraba idanuwa tana wasa da yatsun hannuwanta, wata uwar ashar gwoggo ta antaya mata ta fisgo ta, ta warce ledar hannu ta, ta fara kila ta tana cewa, "wato abokanan watse warki wajan talla har sun fara biyo ki cikin gida, aiko uwar ki zanci" duka Nihal take kamar Allah ya aiko ta tanayi tana masifa, mudi ne da shigo warshi yanzu yabi gwoggo da Nihal da kallo tare da tanbayar lafiya gwoggo na haki ta d'ago, Nihal ko ta samu ta runtama da gudu d'aki tana kuka gwoggo ta ce, "ai wallahi indai ni dake ne yanzu muka fara yo in ba iskanci ba, a ce har aboka nan watsewar ta sun fara biyo ta gida wato wata rana a gaban idanuwan mu za'a ci ta ko," mudi ko tunda gwoggo ta fara magana ya lula duniyar tunani ashe dama Nihal yar hannu ce a lallai dama ya dad'e miyan shi na tsinkewa musanman yanzu da yan'matan ci ke bayana a jikin ta ba komai ke tafiya da imanin shi ba kamar hips din ta da d'an k'aramin bakin ta, lumshe idanuwa yayi tare da kad'a kai shima k'wallan shi ta kosa shiga raga, ko ida saurara gwoggo baiyi ba ya shige daki yana tufka da warwara yana hango sura Nihal wanda yanzu ta fara zama cikakiyar budurwa, bude ledar da yaya yaba Nihal gwoggo ta shiga yi kayan zak'ine kamar suyi magana bak'in cikine ya tokari zuciyar gwoggo dan tasan bame kawo mata wannan abin arzik'in sai wannan d'an birni sannan ta d'au alwashin sai ta masu waman farak'a idanma shi ke sata rawar kai, haka Nihal taci kuka ta gaji wanda kuka yanzu ya zamar mata jiki, jakar ta dake sak'ale jikin 6usa ta janyo ta ciro wasu hotu na wayanda sukayi da su umma tana kallon pictures din tana hawaye a haka har wani wahalalan bacci ya kwashe ta.******
Horn yayi mai gadi ya wangale mashi gate yana sakin murmushi a hankali ya sako hancin motar shi cikin compound d'in gida tare da parking motar parking lot a hankali ya bude murfin motar bayi na ta zubewa suna kwasar gaisuwa kai tsaye part na su ya wuce.
main parlour ya shige ba kowa cike da murna da zumud'i yake cewa, "Adda your son is back" Adda dake shiryawa gaban dressing mirror ta juyo muryar Ammar murmushi ta saki tare da feshe jikin ta da turare ta fito da sauri shima ammar da sauri ya k'arasa gaban Adda tare da kai mata hug yana cewa, "I miss you Adda" d'an ture shi Adda tayi tare da d'an had'e ranta ta ce, "ba wani you miss me kaje kauye kayi zaman ka kai kad'ai, wai me ake haka a kauyan nan ne? har yasa ka manta gida" far ammar yayi da idanuwa tare da kashewa Adda idanuwa yace, "Akwai story amma first lemme take bath tukun na," murmushi Adda ta saki tana cewa, "Allah yasa naji Alheri"
"Alheri mane Adda ga car key dina kiba sani ya curo kaya a boot ya kaimun su bedroom"
"OK"
Part nashi Ammar ya shiga kayan shi ya rage sannan ya shige toilet ya dad'e yana wanka cike da tunanin Nihal sai da ya kamala wanka tsaf ya fito sanye da bathrobe da k'aramin towel yana goge jikin shi, trolley shi ya kalla wanda sani ya aje tare da kauda kan shi, shiryawa yayi cikin black yadi me d'an kauri sannan ya feshe jikin shi da turare yasha kyau har ya gaji, a hankali ya bude handle din kofar bedroom ya fito kallon parlour shi yayi shi kan shi yasan yayi missing gida, fita yayi daga part d'in ya wuce na Adda zaune take tana kallo Arewa24 ana program din akoshi da rufi rungume ta Ammar yayi ta baya yana cewa, "Adda bari naje wajan Sultan I miss him wallahi,"
"Ka bari ka fara yin lunch sai ka je mana" d'an kwa6e fuska Ammar yayi ya ce, "nafi so na fara ganin shi sannan zan samu peace of mind"
"Toh shikenan ka ce mashi ina gaishe shi Allah ya bar soyayya" dariya Ammar yayi tare da ficewa zuwa gidan maimartaba,

YOU ARE READING
SAUYIN RAYUWA
Romancekuka ne ya kwacewa NIHAL tana furta duk addu'ar data zo bakinta wannan wace irin RAYUWA ce yaushe ne zata samu SAUYIN RAYUWA da gata kamar ko wace 'ya, raban ta da wani abu sh farin ciki tun bayan rasuwar mahaifinta. bana tunanin akwai w...