SAUYIN RAYUWA

641 29 1
                                        

🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

    🕊 *SAUYIN RAYUWA*🕊

💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞

*Story*
    *And*
        *Writing*✍🏽
             *By*
*Salma mas'ud nadabo*👑

*Edit by:*
    *Aliyu Miko Muhammad*

*Follow me on wattpad: salmamasudnadabo*

🌲 *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*🐄
('''We are the best among the best ''')

https://mobile.Faceook.com/Real-hausa-fulani-forum-RHFWF-173984973194167/?refid=52&ref=operaspeed-dial&-tn_-=H-R

Email:realhausafulaniwriters@gmail.com
Facebook: www.Facebook.com/REALHAUSA FULANIWRITER'SFORUM.com

*Wannan littafin na kudi ne for those of you da suke san karanta liattfin complete zaku turo 200 kacal a account number na 2261453630 ummusalma mas'ud nadabo zenithbank sai kiyi screenshot na evidence of payment ki turo ta number na ta WhatsApp 07063683025 sai nayi adding dinki a group din da nake posting, zaki iya turo katin Mtn for those of you da basu da account*

Free page

*Page: 02*

Kamala tatar kokon Nihal keda wuya, ta juye shi a bokitin da take zuwa talla da shi.

  Ganin Gwaggo na ɗaki yasa tayi sauri ta shige ɗakin su, cike da sallama ta Shiga ɗakin tana mai kallan umman ta, dake kwance saman tabarma wadda ko motsi ba tayi daga idanuwan ta sai bakin ta, dake motsawa sakamakon ciwon da take, kallo ɗaya zaka mata kasan mahaifiyar Nihal ce, a hankali Nihal ta matso kusa da ita, duk da warin da take tabbas abinda Gwaggo ta faɗa gaskiya ne, babu abinda umma keyi banda tashin wari kasancewar uwa uwa ce shiyasa ko jin warin ba tayi.  murmushi ta kuma saki tare da daura hannun ta saman gashin umma, Wanda ya cukurkude amma duk da haka ana ganin tsawan shi da laushinsa, wasu hawaye ne masu zafi suka sulalo  ma umma, girgiza kai Nihal tayi ta ce, "umma na abin alfahari na, ki daina zubar da hawayan ki insha Allah zaki warke umma, ki dinga yawo kamar kowa kin ji rabin raina,"  ta ida zancan tare da shafa gefen fuskar umma. 

    
   murmushi Umma tayi ta buɗe baki a hankali wadda ya mata nauyi ta ce,"Allah yasa maki albarka Nihal,"
     "Amin Umma, sai kinyi hakuri yau Umma na naso ace tun kafin asuba na tashi, har na maki wanka amma yanzu lokaci ya ƙure," murmushi kawai Umma tayi Nihal ta miƙe har ta kai bakin ƙofa ta juyo tana kallon Umma sannan ta fita da sauri.
 
   Cikin sa'a ko da ta fita Gwaggo na ɗaki sai shewarta da ke tashi ita da yar lelan ta, bokitin koko kawai ta ɗauka, sannan ta sa kai ta fita tana tafe tana sauri kansancewar har yanzu gari bai waye ba sosai, gashi ƙafar ta ko arziqin takalmi bata samu ba, sai zafi da kasan ƙafar ta ke mata haka dai ta samu har ta kai tasha,  wato inda suke sai da koko.

    "Nihal". "Nihal" sunan ta da ake ta kira ne ya sata waigowa cike da fara'a ta CE, "jummala"
      "na'am"
"me yasa yau baki biyo min ba?. rausaya kai jummala tayi ta CE, "ina san zuwa Nihal amma abinda Gwaggo ke maki ne bana jin dadi shiyasa Nihal."

    Rausaya kai Nihal tayi ta ce, "karki damu jummala lokaci ne ya kawo haka tare da sauyin rayuwa, yau kusan shekar hudu kenan raban dana tsinci kai na cikin fari cikin jummala" ta ida zancan wasu hawaye na sulalo mata hannu jummala tasa ta goge mata hawayan, "ba komai ƙawata Allah yana tare daku ke da Umma" a haka suka ƙarasa har gaban bishiya suka zauna.

    Wani ɗan matashin saurayi ne ya ƙaraso gaban su, cike da murmushi yana kallon jummala ya ce, "samin dan wakyan 50," sannan ya samu guri ya zauna yana kallon Nihal ya ce, "ni ko jummala na rasa me nayi ma ƙawar ki, bata min magana kullun fuskar ta daure" ya fada yana kallon fuskar Nihal cike da fara'a, girgiza kai jummala tayi ta ce, "laaa wallahi baka fahimci Nihal bane shiyasa"

    "To shikenan yanzu dai duka nawa ne kudin koko dana dan wakyen?Bana so ina ganin ku anan kuna talla" duk Wannan zancan da saurayin keyi kan Nihal na ƙasa ko Kallon  inda saurayin yake ba tayi, murmushi jummala tayi ta ce, "Ni ko kana bani mamaki, har  yau ka kasa faɗa mana sunan ka, amma kullum sai ka siye kayan mu duka kuma da alama kai ɗan birnine ko?"

"Jummala Ashe ana gane yan ƙauye irin mu kenan"? dariya Jummala tayi ita da Nihal wadda sai a lokaci ta dan dara.

     Wannan ɗan saurayin da ke zaune kusa da su Nihal ba yau ya far zuwa tasha ba, kuma kullun fes zaka Ganshi shi dai baza'a kira shi da fari ba amma dai ruwan tarwada ne, daka kalle shi kasan dan  hutu ne  dan bai yi ruwan dan kauye ba, har wa yau dai bai taɓa faɗa masu suna shi ba, duk sanda Jummala ta tanbaye shi sai yace mata sunan shi bawan Allah, hakan yasa Jummala ke Kiran shi da dan uwa haka itama Nihal duk da ba wata magana ke shiga tsakanin su ba, amma duk san da ya zo sai ya kafe ta da idanuwan shi, hakan yakan sata jin nauyin shi, haka ya ƙirgo kuɗin ya basu sauran yace sunyi sadaka haka suka dinga mai godiya, har yayi gaba Nihal ta ce, "yaya Allah ya biya maka buƙatunka na alheri" lallausan murmushi ya saki ya ce, "amin Nihal, sannan suka cigaba da Raba talla, har Nihal ta dibar masu dan idan zata iya tunawa raban su da abinci tunda jiya.

Kasancewa juye sukayi yasa tun karge  10:00pm ta kamo hanyar gida jummala tayi hanyar gidan su, har ta shawo kwana taci karo da Mudi da alama ya sha ya bugu kallo ɗaya zaka masa kaji baka marmarin maimatawa, shine babba ɗan Gwaggo daga shi sai saratu wadda yayi mata nisa sosai  ko wajan haihuwa, rabawa tayi ta gefan shi zata wuce,  fisgota yayi ya kifa mata mari ya ce,  "dan ubanki har kin isa na wuce ke ma ki wuce baki bari na gama wuce wa yo ko uwar ki Hansatu ta isa na wuce itama tazo zata wuce," tunda Mudi ya wanke ta da mari ta kafe wasu hawaye masu zafi na bin kuncin ta ko kallon ta bai kuma yi ba ya wuce, yana  zuƙar sigarin da ke hannun shi zamewa tayi ƙasa tare da sakin kuka me cin rai sai da tayi kuka ta gaji sannan ta ja jiki ta shiga ciki, muryar Gwaggo da dillaliya kawai ke ta shi a gidan. 

"Haba Indo ke kanki kin sani ina maki sauƙin kayan nan kinfa san ke kaɗai nake ma sauƙin kaya Indo"
  "To shinkenan yanzu dai ki ajiye min su idan Malam ya dawo daga birni zan faɗa masa"
    "yauwa ko ke fa ƴar gari.

   Sallamar Nihal ce ta katse masu zancan su ko ta kanta basu bi ba, sai hirar gaban su da sukeyi, gaishe da larai dillaliya tayi cikin ladabi kawar da kai tayi kamar bata ji ba, ganin haka yasa Nihal aje bokitin koko, ta ciro kudin dake habar zanin ta ta ce, "Gwaggo gashi" wartar kudin tayi ta irgasu tsaf sannan ta kalli Nihal ta ce, "wallahi naso ace kuɗin nan kabo ta bace kiga yadda zan kusa kashe ki a gidan nan", Sun kuyar da kai Nihal tayi tana wasa da yan yatsun hannu ta sannan taja jiki zata shige daƙin su, tsawa Gwaggo ta daka mata ta ce, "baki gamamin aiki ba ai da har zaki shiga ciki, kayan Sara nan na jiran ki idan kin gama ki shiga ɗakin Mudi ki gyara inda yayi amai fes, sannan  ki kwaso kayan shi masu dati ki wanke, idan kin gama ga alalan rana najiranki kuma duk wannan aikin da zakiyi karki wuce karfe ɗaya da rabi 1:30 na rana.

  Sara Gwaggo ta shiga kwallawa kira fitowa tayi tana miƙa tace, "Haba Gwaggo  ina  bacci duk kin bi kin dameni da kira dan Allah, kawai kin katsemin jin dadi" ko kallon larai bata ishe ta ba, bale kuma gaisuwa, murmushi gwoggo tayi ta ce, "haba ƴar lele aini ban san bacci kike ba dama kayan wankin ki zaki ɗauko Wannan yarinyar ta wanke maki" tsaki taja sannan ta shige ɗaki ta dauko kayan ta watsawa Nihal a fuska tare da gyara tsayuwa ta ce, "kuma ki wanke min kaya da kyau kin ji na faɗa maki" sannan ta shige daki  abin ta

SAUYIN RAYUWAWhere stories live. Discover now