SAUYIN RAYUWA

570 17 3
                                        

🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

  🕊 *SAUYIN RAYUWA*🕊

💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞

*Story*
     *And*
         *Writing*✍🏽
               *By*
*Salma Mas'ud Nadabo*👑

*Edit by*
   *Aliyu Miko Muhammad*

🌲 *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*🐄
('''We are the best among the rest''')

https://mobile.Facebook.com/Real-hausa-fulani-writers-forum-RHFWF-173973194167/?refid=52&red=opera-speed-dial&-tn_-H-R

*Email*:Realhausafulaniwritersforum@gmail.com
*Facebook*:www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITERSFORUM.com

:Free page:

*Page: 29_30*

   Nihal ce ta kalli yaya wanda shima kallan ta yake ta ce, "gaskiya yaya wajan nan yana da kyau sosai, ina san wurin nan dubi yadda tsuntsaye ke shawagi yaya ga wata ni'ima da sanyin daɗi, amma nasan duk daɗin wurin nan bai kai birni ba ko yaya? ina so naje birni naga ƴan gayu abba ya sha faɗa min cewa wata rana tare zamu je birni naga gari amma sai ga..."  lumshe idanuwa Nihal kawai tayi saboda rawar da muryar ta keyi, "ƙanwata kenan shiyasa na zaɓa mana nan dan ki rinƙa samun hutu da nutsuwa, maganar zuwa birni ko ki kwantar da hankalin ki insha Allah zaki je birni har ki zama wani abu na alfahari,"
    "yaya na kenan bana tunanin akwai ranar da zan zama haka, ka duba ka gani tallan safe da ban na rana da ban na dare da ban kabata ganin in da dan tallah ya samu cigaba sai dai ya ƙare a yawo a titi" Nihal ta ida zancan hawaye masu zafi na wanke mata fuska, girgiza kai yaya yayi ya ce, "Nihal ba'a fidda rai ga rahamar Allah ƙanwata ki daina saurin yanke ƙauna akan rahamar ubangiji ki rubuta ki aje komin rintsi komin wuya zaki samu cigaba a rayuwa Nihal" murmushi Nihal ta saki tana tila dutse cikin koramar dake gudana, a gaskiya kalaman yaya na mata daɗi ko ba komai a duk sanda tana tare da shi tana samun nutsuwa, Yaya ne ya katse mata tunani da cewa, "ni ko ƙanwata ina jummala ƙawar ki?
    "Jummala nan bamu haɗuwa shiyasa saboda bana samun wani lokaci bale har mu haɗu da ita kuma makaranta ta boye ta, duk da nasan Jummala tsoran Gwoggo ke hana ta zuwa wuri na"
        "duk sanda kuka haɗu kice mata ina gaishe ta"
      "zata ji insha Allah.

  Baba mai gadi ne  ya ƙaraso da bokitin Nihal ya aje yana jerawa Yaya godiya sannan ya miƙawa Yaya kula dake hannu shi mai kyau ya koma wajan zaman shi miƙawa Nihal kula yaya yayi yana cewa, "ga wannan idan kin koma gida ki samu ki ci ke da Umma karki barmin kankin da yunwa" Yaya ne ya faɗi hakan cikin sanyin murya, idanuwan Nihal ne suka kawo ruwa jikin ta na rawa tasa hannu ta amshi kular, idan zata iya tunawa raban su da abinci ita da Umma tun jiya, girgiza mata kai Yaya yake alamar kar tayi kuka buɗe baki tayi da niyar gode mashi hannu ya daura saman lips din ta alamar baya so sun daɗe suna kallon junan su sannan Nihal ta kauda kanta,  ɗan sosa ƙeya Yaya yayi ya ce, "lokacin tafiya gida yayi ko? daga masa kai Nihal tayi cike da shagwaɓa miƙewa su kayi a tare maƙale ƙafa Nihal tayi saboda tsamin da ta mata ga fason ƙafar ta dake ta mata zafi, yayane ya lura da yanayin da take ciki, kwala wa Baba mai gadi kira yayi yace ya siyo mashi silifas da sauri baba mai gadi ya ƙarasa shago ya siyo yana miƙawa yaya yayi godiya sannan ya miƙawa Nihal wani irin daɗi  ne ya lulluɓe ta godiya ta shiga jera masa tana tsalle-tsalle dariya ta ba shi sosai saboda yadda takeyi.

                   *****
Bayine ke ta zarya acikin babba Masarautar  *MATAWALE* kowani bawa na sanye da kaya launi iri ɗaya mata nasu rawaya doguwar riga maza ɗinki mai sulke wanda aka sarrafa shi da yadin haɗa da hular, wangale geta ɗin da akayine yasa bayin suka jera layi kowa ya sada kanshi ƙasa, tunda motocin suka fara kunno kai babu motar da tai ƙasa da miliyan ashirin (20) a ƙalla motocin zasu kai biyar biyu gaba biyu baya daya a tsakiya wadda tafi kowace motar dake ciki ƙayatuwa gami da kyan gani, murfin motocin huɗu aka buɗe a tare dogarai ne da security's majiya ƙarfin dantse waƴanda sun sha suit black da baƙin glass dogarai na sanye da riga malin-malin da sharɓeɓiyar bulala wasun su harda tsofaffin taɓaryu kai kace wanda zasu yaƙi, busar da aka fara ne da algaita shi zai tabbatar maka da dan sarki *SULTAN* ya dawo daga ƙasa mai tsarki wato makka wadda ke zaune a nahiyar Saudiya, ɗaya daga cikin security's ɗinne ya ƙaraso da sauri ya buɗe murfin motar tsakiyar ya ja gefe ya tsaya, a hankali ya turo kafar shi wadda ke sanye cikin takalmin sarauta ruwan zaiba  mai matuƙar kyau sai daya jinjina sannan ya idda fitowa gabaki ɗaya bayin dake harabar wurin zubewa sukayi suna masu kwasar gaisuwa, wow masha Allah haɗuwar guy ɗin har kusan sumar dani tayi duk da a lokacin fuskar shi na cikin rawani, zabuni ne sanye a jikin shima mai ruwan sulki wanda yasha aiki da milki zare sai alkyabba milk wanda tasha aiki ta gaji kanshi na sanye da rawani white idanuwan shi na sanye da dan siririn glass fari gabaki ɗaya gurin haskyan shi kawai ke baiyana, yana ɗauke da ɗan siririn hanci da jajayen laɓɓansa wanda suka kasance ƙanana kamar ya shafa janbaki, taku uku zuwa biyu yake cikin isa da mulki fadawa da security's na bayan shi, isar su bakin wata  haɗaɗɗiyar ƙofa yaja ya tsaya fadawan dake bakin ƙofar ne suka  buɗe masa ƙofa, d'aga wa fadawan bayan shi hannu yayi alamar su tsaya bakin ƙofa shi kan shi hannu abin kallo ne fari yake tas yana ɗauke da agogo ruwan haɗalashi na azirfa mai tsadar gaske yatsun hannu shi na sanye da zoben azurfa,

   Haɗaɗɗan parlour ne wanda ya amsa sunan shi yasha Royal chair's ash and black bayine keta kaikawo, gimbiya ce  zaune saman ɗaya daga cikin kujerun tana sanye da  doguwar riga lace mai tsaɗar gaske green ana mata massages,  a hankali Sultan ya ƙaraso yayi hugging nata tabaya wani irin lallaunsan murmushi gimbiya ta saki bayin dake ɗakin ne suka shiga kwasar gaisuwa hannuwa kawai ya daga masu cikin calm voice din shi cike da shagwaɓa ya ce, "habibty I really miss you" ya idda zancan tare da zagayowa  miƙa mashi hannuta tayi yayi kissing nashi sannan ya zauna da nuna alamar gajiya murmushi gimbaya ta saki dan tasan halin ɗan na ta, yanzu yana iya cewa kayan sun isheshi tun kafin ta gama zancan zuci Sultan ya fara ƙorafi "habibty ni dai gaskiya kayan nan sun isheni bana iya  1hour da su" ya faɗa yana furzar da iskar bakin shi, "bari na wuce part ɗina nayi taking shower na dawo" murmushi gimbiya ta saki, "amma kafin kaje part naka ya kamata kaje part din maimartaba da part ɗin second mom ɗin ka first" cike da isa yace,  to.

  Kai tsaye bai zame ko ina ba sai fadar maimartaba, security da fadawa na biye da shi dai-dai bakin ƙofar ya daga masu hannu alamar su tsaya, shiga yayi yana faɗaɗa murmushin shi wanda ke fito da zalla kyan shi, cikin rawani face ɗin shi take amma ana ganin kyata inaga ya cire rawanin, sarki dake saman kujera shi ta mulki datijo mai natsuwa da adalci da sanin ya kamata, Sultan na isa gaban shi ya zube yana kwasar gaishuwa , a hankali sarki ya mike ya dago shi ya rungume tsam  shi kan shi sarki yasan yayi missing dan na shi  sun dau lokaci suna rungume da juna sannan Sultan yayi break up din hugging din yana smile, maimartaba ne ya ce, "masha Allah Sultan ka ganka ko cikakyan babba  mutum mai natsuwa da kamala"  ya mutse fuska Sultan yayi ya ce, "Allah ya taimake ka nifa kayan nan duk sun isheni" ya fada  a shagwabe, murmushi maimartaba yayi irin nasu na manya ya ce, "a hankali zaka saba,"  sun dade suna hira da maimartaba sannan ya wuce part din gimbiya jalila wato second mom din shi step mother din shi, shiga shi part din ta, bayi suka fara kwasar gaisuwa suna mai kirari, gimbiya jalila dake zaune saman royal chair ta wani hada rai tayi zaman yan sarauta tana cin fruit ganin bayin ta na zube wane ya sheda mata dan gold din ya zo wanda ake fifita shi akan ya'ya ta da sauran yaran gidan, tabe baki tayi  tare da mikewa badan ta so ba tana sakin murmushin yaƙe, murmushi Sultan ya saki irin wanda take ji kamar ta kashe shi dan haushi hannu ta miƙa mashi yayi kissing ɗin shi  sannan yayi kissing goshin ta tare da yin hugging din ta cikin sweetest voice din shi ya ce, "ruhi I really miss you" break up din hug din yayi gimbiya jalila na murmushi mai cike da ma'anoni mai cike da dunbun munafurci na gidan sarauta.

'''Taku har kullun Salma Mas'ud Nadabo ''' ✍🏻

SAUYIN RAYUWADonde viven las historias. Descúbrelo ahora