ALIYU GADANGA..!

1.9K 139 2
                                    

*ALIYU GADANGA..!*
_(The Story of Young Soldier man)_

*Wattpad:Janafnancy12*
_Mallakar:Janafty💖_

*DEDICATED TO MY MOMMAH...,HAUWA S ZARIA(MMN USWAN)*

_Special gift to my Real Dota RAHMA😘 Ladingo yar Mutan Niger_

*Intelligent Writers Association*✏

*NOT EDITED*💥

        *Chapter 6*
         

    Jabir ya dade dakin Goggo suna hira sai wajen 10:00pm na dare,Goggo taga Aliyu baida niyyar bude kofar shashensa,fitowa tayi da kanta ta isa har kofar shashen tahau bugawa tana fadin"Gadanga kazo,ka bude kofarnan.."kazo ka bude nace ko?goggo take fada cikin fada.

  Yana kwance akan Daya daga cikin kujerun Falo,inda Allah ya taimakeshi lokaci da"akazo za"a yima Ni"ima jeren kayanta,hanawa yayi,saboda bazama zasuyi anan dinba,cemusu yayi kada su damu,ko gidanshi na cikin barikin akwai komai,so no need su wahalar da kansu,dayake dama already ya rigaya daya gyara barayinsa nasa bayan ya kawatashi dakayan alatun more rayuwa.

  Yanajin Buga kofan Goggo,da maganart,ammh yayi mata banza,yana kwance dagashi sai boxers kadai,babu ko riga ajiknsa,gashin kirjinsa yayi kwance luf dashi,Idanunsa suna lumshe ne,ammah ba barci yake ba,Damuwa tareda bakinciki ke mukurkusan shi,shi yanzu bama ta Ni"ima yakeyi ba,ta makomar rayuwarshi yakeyi,"Waye Mahaifinsa?inda  gaske Goggo takeyi shi ba shege bane,to ina mahaifinsa da Danginsa suke? Tambayar da haryau bai samu mai amsamai ba.

Goggo jin Shuru ya sata matsa jikin tagan kofan tana fadin"wlh ko kazo ka budemin,ko in kira gardawa suzo su balle kofan,na shigo har cikin naci maka mutumci,tunda kan mace,gadanga zaka dinga min kyaluwa ina mgana.."Tafada tana kwafa,Ajiyar zuciya ya sauke kan ya mike jikinsa asanyaye,bude lumsassun idanunsa yayi,bansan sadda na Furta subhannallah ba,saboda yadda idanunsa,suka chanza launi,sunkoma red sosai,Jikinsa babu kwari yazo ya murza key din kofar ta bude,bai bi takan Goggo da jabir dake tsaye ba,ya juya yakoma cikin falon yazauna kan kujera,yana kauda kansa,Shigowa dakin Goggo tayi tana fadin"Gadanga..Gadanga..Gadanga.."Saunawa na kiraka.."

Ko dagowa baiyi ba,yace cikin husky voice dinsa"Wai ni Goggo don Allah menayi miki ne?kamata fa yayi ki tsausayamin na rasa,love of my life,ammh kinzo sai fada kikemin.."Yafada yana wani kyabe fuska kamar zai yi kuka,Jikin goggo ne yayi sanyi ta karisa gareshi tana fadin"Yo ai kaine gadanga wani lokacin da ban haushi,ai ni na dauka bazaka wani damu ba,duba da yadda mahaifinta ya tozartaku gaban dubban jama"a,wlh indai kana da zuciya bai kamata kaji dacin Abun ba.."tafada tana zama kusa dashi kansa ya dauka ya kwanta bisa cinyarta yana fadin"koma miye,goggo i Love her,duk da Abunda mahaifinta yayi i knowa Ni"ima tana cikin wani hali yanzu cuz she luv me goggo i swear she can do without me.."Yafada yana damke hannun goggon

Dungure masa kai tayi da dayan hannunta tana fadin"Wai ban hanaka min mgana da wannan yaren Nasaran ba,sai na fara cin kaniyarka tukunnah ko"Tafada tana yar dariya,bai tankata ba ganin haka yasa ta hausha  shafa kanshi tana fadin"karka damu kanka Kaji,Allah yabaka mace tagari saliha,na tabbatarmaka Azeema zata zemamaka sanyin idaniya nan gaba,mganar mahaifinka kuwa mucigaba da addu"an gadanga inda rabon sake haduwa,Allah zai hada,ammh ina ji ajikina,Abdulnaseer bai mutu ba yana nan Araye,Ammh inda yakene,ban sani ba,Allah shiya barma kansa sani.."Tafada idonta na cikowa da hawaye,mikewa Aliyu yayi yana kallon goggo kan ya saka hannu ya shafa fuskarta yana fadin"To goggo,in bai mutu ba,yana ina,? ko yan"uwanshi ba wanda zaki tuna,ko yataba fadamiki.."Shuru goggo tayi kan ta sauke ajiyar tana fadin"Gaskiya baitaba fadamin ba,sai dai yana yawan Ambatan Agadez domin yacema mallam ko abaya daga yankin ya fito,ammh kasan Agadaz ba karamin gari bane,kuma shekaru sunja,gaskiya mawuyanci Abune,agano wanda ya sanshi sakamakon babu wata shaida da zata bayyana hakan,..,"Tafada muryanta asanyaye."

ALIYU GADANGAWhere stories live. Discover now