*ALIYU GADANGA..!*
_(The Story of Young Soldier man)_*Wattpad:Janafnancy12*
_Mallakar:Janafty💖_*DEDICATED TO MY MOMMAH...HAUWA S ZARIA(MMN USWAN)*
_Special gift to my Real Dota RAHMA😘Ladingo yar mutan Niger_
*Intelligent Writers Association*✏
*Chapter 28*
Aliyu da kanshi ya dauki Azeema da hannunsa ya sakata acikin mota goggo ta Shiga baya,jabir na Driving,su Muneera ma Motarsu, suka Shiga suka Mara musu baya,Mallam lawal Bai bisu ba,yadai bisu da addu"ar Fatan samun lafiya,general Hopital suka kaita,suna zuwa aka karbeta da gaggawa,likitan yana ganin yadda take yafara Sakamata drip tare da wasu Allurai,domin yace ba Suma tayi ba,jikinta ne babu karfi sam,Jininta aka diba First,aka tafi dashi lab,domin gwadawa,itakuma Dama Ruwan daya samata saboda yataimakamata wajen samun karfin jikinta.
Gwajin Farko ya Tabbata da Samun ciki Azeema na Tsawon Sati Takwas koda Resuilt din ya Fito Gadanga aka Damkawa murna kamar bakinshi zai zage,Rumgume jabir yayi yana godiya ga Allah,goggo ko mirmishi take na Farinciki,domin dama Tuni Ta Fahimci ciki ne da Azeemar,itako Azeema batasan wainar Da ake toyaba,tana kwance duk jikinta ba karfi,bata dade ba ta Farka tana Fadin"Goggo Ruwa..." da hanzari Goggo ta bata Ruwa,kafin ta taimakamata tatashi Tana tashi idonta na kan Aliyu wanda yakafeta da ido,yana kallonta lokaci daya da mirmishi bisa Fuskarsa,kauda kai tayi tana amsa Sannun da Ni"ima da Munnera suke mata,amsa musu tayi da kai,tana Kara kallonsu,ita Ni"imar nema ke bata Tsausayi,jabir ne yayimata sannu takarba dakai,Aliyu dayake tsaye chan gefe sai ya matso kusa da ita yana fadin"pretty ya jikin?Kura masa ido tayi tana Tuna sanda yayi Shuri da ita,Runtse ido tayi hawaye na kwararomata,kauda kai tayi tana cije bakinta,ganin haka yasa goggo ta Girgiza kai ta saka kai Ta fice,Jabir ma yabi bayanta Ni"ima ce ta karisa gaban Gadon Azeema tace"Zamu Tafi Azeema,Allah ya baki lafiya.."
"Gyada kai tayi kafin tace"ngd..."Dakyar cikin muryan ciwo,kallon Aliyu tayi kafin tace"Captain zamu Tafi,ina Fata dai An yafemana kuran damuka aikata.."Tafada idonta na cikowa da kwallah,Mirmishi yayi yana kallonta kafin yace"Bakomai Ni"ima buh next time Kada hakan takara Faruwa ko ba akaina ba,ku koyi yaki da zuciyarku don Allah..."
gyada kai tayi kafin ta Share kwallah Tana Fadin"Insha Allahu hakan bazata kara Faruwa ba.."Gyada mata kai yayi yana Fadin"Toh Yayi kyau naji dadin haka,share hawayenki kibar kuka hakanan,komai ya wuce.."Mirmishi tayi batayi mgana ba,sai ta waiga tana kallon Azeema wacce ta Runtse ido ammh kaf Abunda suke Fada akunnanta ne,Dafata tayi tana fadin"Congratulatino Sisto Allah ya inganta.."Daga haka tajuya,muneera dake tsaye itama tayi Fatan samun lafiya kafin su Fice,awaje sukayima su goggo sallama,suka Tafi suna jin zuciyarsu tayi sanyi Tunda komai ya Wuce yanzu.
Suna Fita ya karisa gareta lokaci daya yana harde hannuwansa bisa kirjinsa kallonta yake dakyau yadda Fuskarta tayi Fayau tabashi Sha"awa,Sunanta yakira ahankali.."Pretty..." Tana jinsa tayi mishi banza harda dan nishinta alamar barci takeyi,yana kallonta yar dariya ta kamashi,sai ya saka hannu ya dan,matse hannun Da aka sanyamata Drip,taji zafi da hanzari tajaye hannunta tana Fadin"Wash.."tafada tana Jaye hannunta bata bude ido ba,ta mirgudamai baki,dariya ta kamashi sai ya Rankwafa yana lakucemata hanci yake Fadin"Matar Sunnah bata Fushi da mijinta,kuma in yayimata laifi yakamata ta Sausautamai,koyasamu damar bada hakuri..",tana jinsa tayi mishi banza,sai ma juyamai baya datayi,Kai ya dafe yana Saka hannu abaki,kafin ya Sauke ajiyar zuciya yace"Shikenan ki Adanamin duka Fushinki pretty har na dawo,nayi alqawarin daukan kowani mataki kika Dauka akaina,ammh i want to u to know one Thing i relly miss u so much,and kinbiyani Tunda kikayi Saurin Cafkan sako na,Adaren Farkomu,Allah ya saukeki lafiya.."Yafada kafin ya duka ya bata kissa Ahannunta,ya saka kai Yafice yana mai jin Farinciki,Sai da ta tabbarta da yafita kana ta bude ido tana Dafe kirji tace"Ina da cikin yaya captain yanzu a wannan cikin? tafada Tana dafa cikinta lokaci daya tana Sakin mirmishin Farinciki,hawaye suna zubomata ta sanya hannu ta Share Tana fadin",Allah na godemaka..Ni nan da wata Tara nazama mama"Tafada kafin ta saka dariya ita kadai,shafa cikin take tana mirmishi ita kadai,kafin chan kuma ta Tura baki tana fadin"Ina Sonka,ammh ina Fushi da babanka,duk da kewarsa da Soyyyarsa bazata taba barina Fushina yayi Tasiri Akanshi,Alhamdulillah Allah nagodema.."take Fada tana mirmishi ita kadai.
