ALIYU GADANGA..

2.3K 102 1
                                    

*ALIYU GADANGA..!*
_(The Story of Young Soldier man)_

*Wattpad:Janafnancy12*
_Mallakar:Janafty💖_

*DEDICATED TO MY MOMMAH...HAUWA S ZARIA(MMN USWAN)*

_Special gift to my Real Dota RAHMA😘Ladingo yar mutan Niger_

*Intelligent Writers Association*✏

      *Chapter 26*

    *After 1 week*

    Bayan Sati daya da dawowar Azeema gombe,har kuma yau basu ji wani mgana daga bakin Gadanga ba,koda goggo ta gaji da Fushinta ta kirashi wayarsa bata Tafiya,Itako Azeema bata gayama Goggo Abunda yafaru Tsakaninta da Azeeza ba,saboda batasan taya zata kama lbrin ba,ammh tabi Shawaran goggo ta maida lamarinta ga Allah Shine zai warware komai cikin Sauki,Azeeza kuwa Aranta tana mata Fatan shiriya,Yanzu ta rageyawan kuka da damuwa ammh ba kewa  Tare da kaunar gadanga bai bar Ranta ba,kullum dashi take kwana take tashi,gashi Tunda tazo take Fama da zazzabin dare,dakuma gari yawaye sai ta nemi zazzabin Tarasa,gashi bata cikin kwanciyar Hankali ammh taKara haske sosai Fatarta tayi kyau,Kullum sai dai Tasha paracetamol ta kwanta,itama goggo Abun na damunta ammh Sai Azeema tashashantar da zencen Zuwa asibitin,mganar cin abinci kuma bata cika ci ba,sai da yanzu Tafi kauri wajen kayan kwalama,irinsu goriba,wainar Fulawa ta manja,da kuma Danwake wanda kullum cikin yinshi take,goggo dai kallonta kawai take ammh kasan zuciyarta tana zargin wani Abu,Allah yasa hasashenta yazama gaskiya,Shiko mallam lawal kullum zai Fita kasuwa sai ya Shigo sun gaisa da goggo yaga kwanar Azeema,in ko yadawo sai ya Shigo yakawo mata Sakonta nasu goriba da dan Ta matsitsi tunda ya lura tana so sosai,Sune yanzu Abun shanta da Tsamiyar biri,Daga goggo har Mallam lawal sun tabbatar da hasashensu kan Azeema domin alamomi dadama sun bayyana zarginsu.

Ranar Asabar sai ga Kawu bala Shida Ummah suka diro gombe,Murna wajen goggo ba"a mgana tarasa ina zata sakasu saboda murna,kawo musu Wannan kawo musu wanchan,Sai da suka huta sukaji abinci kafin su shiga tattauna Abun yakawosu Goggo tana Fada tana gayama Kawu bala cewa gadanga bai kirata ba,kuma takirashi akashe,mirmishi kawu yayi yana fadin"Kiyi hakuri Suwaiba komai zai Wuce,ninaje wajenshi har cikin barikin na sameshi,kwance baida lafiya abokinsa na kula dashi,ammh yaji Sauki sosai,yace aiki ne yayi musu yawa,tunda Sojojin hadin gwiwan da"a ke sa ran zuwansu gobe ko jibi su zasu bi Tawagar Cheif Army of Staff,suje Abuja su Taho dasu nan barikinsu Tunda kinga babban bariki ne,mai wakiltan Arewacinmu na Nageria,shiyasa ,kuma komai fa Ahankali zamu bi Suwaiba Har Allah ya warware komai"Jinjina kai goggo Tayi kafin tace,"Shikenan yaya Allah ya Shigemana gaba.."Da Ameen suka karba kafin Kawu yace"Suwaiba kiramin Azeeman nayi mgana da ita.."Tashi goggo tayi tashiga ciki takira Azeema wacce ke zaune ta zabga Tagumi,koda Tafito sanye da dogon hijabinta kasa ta durkushe tana kara gaishesu domin sun gaisa sanda sukazo,hakuri ya Shiga bata tare dayimata nasiha mai Shiga jiki,Tare kuma da Umartanta datayi hakuri tadauka wannan Jarabtane daga Allah,gyada kai Azeema ketayi tana Tsiyayan Hawaye,Ummah dake kusa da ita,tajata kan jikinta tana lallashinta kawu ya kalli Goggo yace"Suwaiba mganar jarabawarta zan baki kudi Ranar monday Ki dauketa kuje tare,kiyimata Rigistration Din,Allah ya Rufamana Asiri yakuma bada sa"a.."Da Ameen goggo ta karba tamai godiya,Itama Azeema tashiga mai godiya,yana girgiza kai baice komai ba.

Basu Tafi Aranar ba ,sai washegari da safe suka koma,bayan ya cika goggo da kudi da kayan Nau"in Abinci kala kala,Mallam lawal ma yasamu nashi kason,don daya dawo daga kasuwa yaShigo nan suka hade da kawu,suka Shiga hirar yaushe gamo,Tare sukaci abinci sai wajen goma ya Shiga gida,Aljihunsa cikeda kudin da kawu ya bashi,koda inna Ramatu Tafara Tsiyarta yana gayamata inda ya tsaya da kudin da kawu yabashi harda kayan abinci,washe baki Inna Ramatu tayi tana Murnan sun samu kudi,domin dama idonta fa Anaira yake,Dubu biyu yabata harda dari biyar,sai kaji baki ya mutu ta kalmashe kafa tana mai Hira harda Cemai in Azeema zata koma zata bita taga dakinta,jinta kawai yake yana jinjina son Abun Duniya irin na Ramatu sam bata iya boye kwadayinta.

ALIYU GADANGADove le storie prendono vita. Scoprilo ora