*ALIYU GADANGA..!*
_(The Story of Young Soldier man)_*Wattpad:Janafnancy12*
_Mallakar:Janafty💖_*DEDICATED TO MY MOMMAH...HAUWA S ZARIA(MMN USWAN)*
_Special gift to my Real Dota RAHMA😘Ladingo yar mutan Niger_
*Intelligent Writers Association*✏
_Sadaukarwa ga FIKIRAR MARUBUTA..,kamar irinsu,HassanAtk,and Hussain80k mai warin baki😹😛,Sai ke my abokiyar Hassada Mrs Sardauna,Ina kike kawata Hassana Dan labarabawa,Walidition,Diyata Ladingo,Sisinah Aisha Alto,my mryam obam Rabi"atu Sbs,Sahibata Hafsart Hafnan,...Da duk jama"ar dake gidan Fikirar marubuta kusani ku kara sani Janafty na muku Son kauna mara iyaka,Ina kuke yan Group din KHADIJA CANDY NOVELS..Ina gaisuwa Salwess,Da duka sauran masu Sharhi dake cikin group din,sai ALIYU GADANGA FANS1..ina kike My Esha,dake mman Muneebata,Aisha Adris,Fatima garba,Mman Ummu(Nemecyna),Kuma yan ALIYU GADANGA FANS2,Ina kai gaisuwa Allah yabar zumunci da duka Sauran group din dasuke Sharhi kan wannan buk din,Ina godiya Sosai Allah yabar Zumunci BOHOT BOHOT LOVE_
*NOT EDITED*💥
*Chapter 21*
""Bai isa Shashen mai martaba ba sai zuwa dare bayan an idar da sallar Issha"i lokacin angama hidimar Fada Sarki ya Shiga cikin gida wajen iyalansa,Lokacin da Umar ya tarar dashi yana kishingide cikin kayatattacen Falonsa wanda yaji kayan alatun more rayuwa,Tuffa ne ahannunsa yana Ci,gefe daya kuma yana duba wani littafin Iziya,jikinsa Sanye da riga da wando,irin na gidan Sarautu,Yana ganin Umar yatashi daga kishingiden yana mikamai hannu Karisawa yayi yana mai mikamai hannun yana fadin"Barka da hutawa Ranka yadade...".
Kusa dashi ya zaunar dashi yana dafa kafadansa yace"Yauwa Umar Sanda,ya aiyukan,nasamu lbrin dawowarka Tundazu toh lokaci muna fada kasan Sha"anin mulki sai da taka Tsantsan,nima dabakazo ba,yanzu nake Shirin zuwa shashen naka.."mirmishi Umar ya saki yana kallon Fuskar mahaifinsa mafi soyuwa gareshi,kafin yace"Eh Abbah Tun dazu na Shigo nima Ban leka Fada ba,saboda gajiya ammh kasan kowani hali nake ciki Dole nazo har shashenka na isheka.."girgiza kafadansa yayi yana fadin"Hakan na dakyau,ya wajen aikin naka Fata dai komai lafiya.
Ajiyar Zuciya Umar ya sauke kafin yace"Lafiya ba lafiya ba Abbah..."kallonsa yayi idanunsa sanye da Wani Farin medicated glass mai karama Mutum karfin gani,kafin yace"Lafiya meyafaru Umar zaki.."?Kada kai yayi yana Fadin"Wlh Abbah mganar hadin gwiwar nan ne Kasar Nageria ta nemi gwannatin kasarmu data hada hannu Suyi tare,Toh acikin Sojojin, daza"a Tura Nigeria Abbah harda tawagarmu kuma nine shugaban Tawagar.."Kallonsa yake har ya dire dan mirmishi yayi mai kafin ya maida kansa gefe yana kallon wani waje Mamaki yakama Umar a ladabce,yace"lafiya Abbah ko acikin mganata akwai Abunda yabata maka rai ne?.."girgiza kai kawai maimartaba yayi kafin ya saka hannu ya zare gilashin dake idonsa kafin yace.
"Ko daya Bata batamin rai ba,saima Tuno min da wani gibi dana kasa cikewa,karka damu Umar Allah natare dakai kuma addu"ar iyaye na bibiyanka,insha Allahu zakuje lafiya ku dawo cikin Nasara.."kai tsaye Umar yace"Ammh Abbah ka taba zuwa Nageria ne,wai ina Nufin koda yawan Ran gadin gidan Sarauta ne?" Kallonsa yake kur kafin ya kauda kai yayi Shuru sai zuwa chan yace"Na taba Rayuwa A Nageria bama zuwa ba Umar.."Da mamaki Umar ke kallon mai martaba kafin ya washe baki yace"Toh Abbah wani yanki ka zauna..? Yanayin Fuskarsa sai ta chanza Jikinsa yayi sanyi yayi Shuru baiyi mgana ba,ganin haka yasa Umar Saurin cewa"Afuwan Ranka ya dade bansan Tambayata zata bata maka rai ba Allah huci Zuciyarka.."bai yi mgana ba sai ma mikewa dayayi yazura takalminsa irin na gidan Sarauta hanyar wani kofa ya nufa sai da yakai kofar dakin kafin ya harde duka hannuwansa ta baya ya waigo yana fadin"Baka Batamin ba Umar,tambayarkace ban da amsarta domin nikaina Bansan awani yanki na rayu ba balle har na dora da wani Abun,Abu daya na sani inaji ajikina cewa ada achan baya nayi Rayuwa da wasu mutane,wanda Ahalin yanzu suke bukata,ammh kuma Allah ya boyemin Abun,addu"a zaka taya mahaifinka Allah ya bayyanar da Duhu yazama haske.."Yana gama fadar haka ya Shige kofar da hanzari.
