4

230 15 0
                                    


SAFIYA TA GARI FANTAN MAHBUB:

washegari da sassafe fanta takammala aikin gidah sannan ta taya innartata tai wanka .itama wankan tayi tasaka doguwar rigarta baka wadda Baffa lado yasayamata sannan tayafa mayafin tanadeshi irin yadda taga yan birni sunayi insunxo siyan nono wajensu.tagyare ko Ina takillace tsaf sannan suka kuma bukkar sauro wajen fita Suna jiran captain mahbub yaxo.

To shidinma bayan ya shirya cikin wani yadi brown da milk yai Kyau kamar Wanda za shi gasar zaben kyau.agurguje yai toasting bread yasha da cappuccino ,ya nufi parlor zaune yahango Baba da gwaggo da alama wata maganar suke.karasawa yai cikin parlor dn yaxauna akan center carpet .baba Ina kwana?lapia qalau mahbub ka tashi lapia?lapia qalau baba.sannan yajuya gurin gwaggo tacika fam kamar zata fashe,Ina kwana gwaggo?dauke kanta tai dakyar ta amsa lpy!

Mahbub yatashi yanadan sosa keya,alh sulaiman yakalleshi ya akayini mahbub?aa bakomi key nakeso gwaggo tabani.aikwa dama gwaggwan acike takeda dashi.okay wani salon munafuncin katsiro kenan ko?kana wani dukar dakai kamar wani sabon ango.to baxan bayarba karfinka yakwatarmaka.

Mahbub kasa magana yai illa juya dayai yana kallon babansa.shi Kansa alh sulaiman din yanasan yatsawatar mata amma karfin sihirin dake jikinsa yahanashi aikata komi .mahbub kuwa ganin zata batamasa lokaci yasa Kai yaificewarsa daga gidan.tsayawai yana kallon motocin dake fake a packing space din gidan kusan EOD dn dayake hawa itace karama daga marcedez Benz se toyota da sauran company.tsaki yai na Allah wadai da muguwar kishiyar uwar dayasamu.

Yana tsaye yana tunanin mafita daga karshede yayanke shawarar kiran dr haydar yafadamasa halin dayake ciki.wayarsa yadakko yai dialing dr haydar.hello aboki kana ina?okay kana asibiti to bari naxo.keke napep yatara aka saukeshi a asibitin.yakira haydar yace mashi yashigo consulting room dn bakomi.

Kansa tsaye yashiga.atsaye yatarar da dr haydar dn yana cire labcourt dn dake jikinsa.kallon mahbub yai bayan sungaysa aboki lapia kuwa naganka haka?aboki meyake faruwane.aboki very soon xaku nemeni kurasa .aboki lapia?haba nagaji da rayuwar da gwaggo tasani aciki,ace mutum dagidansu amma bashi da walwala kwata kwata,Kasan Allah aboki bansan farin cikiba se Ina tare da kai ko fanta ko inmuna waya da nawwara.kasan gwaggo kiri kiri tahanani mukullin motata hardasu cemin wai karfi yakwata.imagine fa haba .

Dr haydar yai ajiyar zuciya .hakuri zakai aboki,nasan tabbas gwaggo xata aikata abin dayafi hakama,kayi hakuri aboki .yanxu ga key dn motata kaje kadakko su nasan sunacan kila Suna jiranka.godia ya masa sannan yanufi packing arena din yadauki motar kirar sportage yanufi kauyen na hayin ruga.

Minti 40 yakaishi hayin ruga a bakin hayin yai packing motarshi.sauri yake harya karasa bukkar ta Baffa ardo.sallama Sau uku yayi kafin Fanta ta masa Iso yashiga.numfashinsa har Neman daukewa yai ganin gimbiyar tasa cikin doguwar riga baka sekace balarabiyar Kasar lebanon.gaysheshi tai cikin muryarta me dadin sauraro.amsawa yai dakyar Dan numfashinsa yana barazanar daukewa .

Karasa shiga cikin bukkar yai yagayda innah wuron sannan yabata hakurin kan rashin xuwa dayai dawuri.bakomai mahbub Allah deyasaka maka da alkhairi.tashi sukai dukkansu innah tashiga baya taxauna a owners corner ,ita kuma Fanta tashiga gaba.mahbub yaja se asibiti!

**********

Random hospital yai packing ,Fanta se leke take tana kallon harabar asibitin.futowa sukai daga cikin motar suka shiga ciki .direct office din dr haydar suka nufa Wanda ke xaune yana checking wasu files.da sauri yamike yana kallon wasu kamar jinsin larabawa tareda mahbub,rintse idonsa yai yabude tabbas ba mafarkibane,lalle mahbub yayi dacen mata.

MATSALAR RAYUWA(COMPLETED✅)Where stories live. Discover now