5

240 17 0
                                    


jirginsu mahbub yasauka a safiyar ranar asabar bejira kiran driver ba yaxo yadaukeshi danyasan koyakira baxai samu ba.hanxari yai yatsaida taxi yakaishi har gida.begakowa a parlor ba sede masu aiki daketa Kai kawo wajen ganin sun gyara ko ina agidan.

Dakinsa yawuce kai tsaye Dan agajiye yake ,wanka yai yabi lapiar gado yakwanta danso yake da sassafe yaje hayin ruga yasanarwa baffanin Fanta abinda ke xuciarsa nagaba da fanta.

Safiyar wayewar garin ranar lahadi,mahbub yai wanka yai shirinsa shigar Shadda yaina light golden sannan yasaka hula da takalmi dark golden.

Indomie yadafa yaci da kwai sannan yadau mukullin mota yafita.hayin ruga yanufa amma kafin yakarasa seda ya tsaya awani store yasai cartons na taliya da lemon roba se lemu da ayaba Dan yasan cimar fulani bata wucce haka.

Minti arba'in yai sannan ya Isa kauyen na hayin ruga,ya faka motarsa a'inda yasaba parking.sannan ya'isa kofar gdansu Fanta Wanda yasa almajirai suka tayashi da Kayan,yana xuwa kafin yakarasa gidan wasu yara dake wasa a dakalin kofar gdan suke fadamasa cikin hausarsu wadda bata fita sosai cewar Fanta bata gdan takoma gdan Baffa lado can hayin shanu.nemayai dasu rakashi gidan,nande cikin tafiyar sassarfa suka rakashi rugar ta Baffa lado.

Godia yaiwa yaran tare da zaro kudi yamika masu,girgiza Kai sukai tareda doriyar anhanasu karbar abu agida gun wanda basu saniba,yabawa yai kwarai da hankalinsu.sallama yai asauren gidan wata yarinya taleko taga waye ?kice mahbub ne sanin cewar su baffan sunsanshi.komawatai cikin gidah tareda fadawa baffan shikuma yafito hade da bada umarnin shinfida masu tabarma asauran.

Bayan sungaysa ne mahbub yasa almajiran suka shigo da kayan suka Saka asauro ,Baffa lado yayi godia sosai haryakewa mahbub wasan ya akai yasan cimarsu ta fulani.mahbub yai dangyaran murya kafin yace Wlhy nima baffa tafiya naine shiyasa banxoba naje Lagos nadubo kanwata datai rashin lapia.

Baffa lado yadangutsiri goro aibana kam ana ciwo canjin rani ne,babu komai mahbub Allah deyasaka maka da alkhairi abubuwan dakakeyi.mahbub yace amin baffa,nima de akwai maganar da nakeso miyi dakai idan Kanada lokaci baffa .baffa yawashe baki har inada wani lokaci dayafi yanxu?karkaji komai mahbub fadi komenene karkaji dar dar!yanxu de bari akawomana fura da abinci muci tukun.

Fura aka kawo masu damammiya da tuwon dawa miyar kuka dayaji nama ga manshanu ci sukai suka koshi har lokacin sallah yai sukai sannan suka koma suka zaune,Baffa lado yai murmushi to yanxu tunda ciki se ai magana sosai.mahbub yace Baffa kana Hausa kamar bahaushe hakama innah wuro kun iya hausa sosai akan su Baffa Sheri.ehh kam munfisu iyawa dayake ni nafi shekara sama da goma Ina aikin gadi awani gida a habuja(Abuja).itakuma wuro itama ai itada ardo megidanta sunyi zaman bunni,to kaji yadda akai.ohh okay hakane.

To dama maganar daxan fadama kashine ehm....Baffa tunsanda nafara ganin Fanta nake Santa,to amma kuma banfadamataba saboda naga da alamin yarinta atattare da ita ,toh sena gayawa innah wuro ko anmata miji?setace Dani a'a ba'ai mata miji ba.amma sede neman auren Fanta ba'a wajenta yakeba yana wajen baffaninta.haka mukai da ita.

Baffa lado ya fadada murmushin dayake miji kam ba aima Fanta shiba hasalima yarinyar ita bakula maxan takeba,kuma koda anyi auren da daya daga cikin maxan garinnan batare da anba dangin mijin al'adar da aka Saba yiba to tabbas amaryar xata xama abun nuni kuma gori xeshiga tsakaninta da mijinta.tabbas mahbub naji dadin wannan maganar taka kuma na yaba da hankalinka kwarai dagaske saboda kai Dan mutuncine tunda Kasan mutunci kuma Kanada mutunci .sede inaso Kasan yarinyar nan marainiyace banaso tashiga MATSALAR RAYUWA ,wallahy yadda nakejin Fanta ajinina kamar diyar dana haifa take.sobada haka nabaka auren Fanta katuro magabatanka muyi magana Nima xankira kannena da baffaninta na Uwa.

Mahbub dadi yacikashi kamar Wanda akama bushara.gwiwoyi akasa yai godia sannan yamike xe tafi?haryasa Kai xefuta.baffa lado yatsayardashi bari nakira fantan taimaka rakiya ko.nixankarasa can hayi,nagode agaida mutan gidan.sa yaro yai akakira fanta.wadda tafuto sanye cikin hijabi ja.atare suka jera Suna tafiya bayan tatsugunna harkasa tagaisheshi.

MATSALAR RAYUWA(COMPLETED✅)Where stories live. Discover now