"Don girman Allah Suleiman karka sakeni,ka tuna fa igiya ɗaya ce ta saura atsakanina dakai,ka tausayamun karka maidani bazawaran ƙarfi da yaji..." afusace yace"baki son ah sakeki shine kike kunsa mun baƙin ciki akodayaushe...?yanzu menene dalilin shigowa dakin ƴar'uwarki ah irin wannan lokacin bayan na tabbata kin kwana da sanin cewa mijinta yana ciki...?har uwar ɗaka fa kika biyomu Hafsa...?kuma har kike neman illatamu akan baƙin kishinki...."Haɗiye miyan takaici yayi yana jin yadda zuciyarsa ke masa radaɗi,itama ɗin afusace ta miƙe tana fadin"so kake in ƙyaleku kuci amanata don bani da wayau...? yau fa ake cike kwanaki ashirin da uku da aurenmu amma sbd baƙin halinku na maza wai ace Suleiman har ka yo man kishiya? Jamilar ce wawiya data zauna take kallonka har ka mata kishiyoyi biyu, toka sani ni bazanyi shiru in tsaya kallonka kana aikata abunda kaga dama da wannan kucakar yarinyar bayan ni anawa daran farkon ma ko hannuna baka taɓa ba, shin baka ma ji kunya ba da kake kokarin haɗa shimfiɗa da ƴar cikinka...?"sauran taran numfashinta yayi yace azuciye"menene abun kunya aciki ina ce dai matata ce wacce dubban jama"u suka shaida daurin auranmu...?fine yanzu na gano dalilin shigowarki har cikin ɗaka,so kike kiga yadda zan raya sunnar ma"aiki da matata,shikenan Hafsa yau zan baki mamaki,zan nuna miki cewa bake kadai ce kika iya fitsara da rashin kunya ba akwai shugabanki anan, Zan................."