BABI NA UKU

183 2 0
                                    

*🍃KISHIN MATA🍃*
               🍃🍃🍃
         _mai dauke da salo na daban🤙..!_

*♟ƖŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾى  ASSɷ*✍

   *NA*

         _*HAFNANCY LURF💕*_
           _*[Hafseesee]*_

   _*💫Dedicated to:-Anty Bahijjata & Grandma Zm Chubado*_

   
*#An_Intense_Jealousy_Story*

          _*💫BABI NA UKU...🤟*_

____________★Ba tare data tsaya neman shawara awajen manya ba ta kamo hannun Azeema,kai tsaye suka danna kai cikin gidan dauke da sallama abakunansu,gaban Azeema sai faduwa yake sosai ita ko uwar gayyar ko ajikinta,idanuwansu ne ya sauka akan enmata kusan goma zaune ah karkashin wani canopy,fuskarsu duk ah murtuke bbu ko digon fara'a,suna ganin shigowarsu duk suka mike tsaye,,kowacce ta kama kwankwaso ta hau girgije girgije,lura da hakan yasa Jameelah kallon Azeema tare da sakin wani irin shu'umin murmushi tace''Ahh lallai zuri'ar tsoho akwai munafukai sosai aciki,wato ga dukkan alamu ya nuna an kira an sanar musu da cewa ina cikin wa'enda zasu zo daukar amarya ne kuma nasan Ramlah ce tunda tana da kyakkyawar alak'a da kanwar amaryar Nabeelah...!'' cike da rawar murya Azeema tace tana kallonsu''Jaaa...meee..lah gaskia ni..fa bani qaunar rigima arayuwata kawaiiii mu koma waje mubar su goggo su shigo....!'' wani wawan kallo ta wurga mata wanda ya kusan tarwatsa hanjin cikinta tace tana hararata''Meh kike yi haka ne sai kace ba mace ba?Azeema tsoro ba nki bane tunda har kina tare ne da matar dan sanda,don haka ki kwantar da hankalinki ni bbu rigimar da zan mayi dasu ammh one word is enough for the foolssss....!'' ta fadi da jajayen ido wit full seriousness...

   ''Nabeelah wai waccece uwargidan tasa aciki ne?...'' wata mai suna Fa'iza take tambayar kanwar amaryar,ta6e baki Nbeelah tayi kan tace''Itace katuwar cikin abu kamar buhun shinkafa...'' dariya suka fasa dukah kuma iskanci ne kawai irin nata in ba haka ba Jameelah ba katuwa bace kawai she's juz chubby and sexy,kishi ne kawai suke taya yar'uwarsu Hafsah,wata mai suna Ruqayyah tace''Da wannan dariyar banzan da kuka tsaya kuna yi why not muyi saurin taransu tun kafin su karaso inda muke muci kutumar uban hegiya?''

''Tunda ita ta kawo kanta da kanta ba...'' wata Ablah ta karashe,gabaki daya su wajen goman suka nufesu,ita Nabeelar ce dai akarshe don mugun shakkar Jameelah take,agabansu suka tsaya cak!

Cike da tsoro Azeema tace''Haba bayin Allah ya haka?meya faru?

Yasin tsoron Azeema ba karamin haushin yake bawa Jameelah ba,ta kwasheta da wani irin harara tace''Azeema wlh karki bani haushi,kina ganin mutane sunci damarar zuwa wasan dandali irin dai wacce akeyi ah k'auye shine zaki wani tsaya tambaya?hanya ce dai suke neman abasu shiyasa suka tsaya mana kerere aka,,ammh abun ya bani mmki wai ace ana irin wannan wasar acikin gari kamar Abuja,kodayake na manta duk inda kaje akwai kauyawa....!'' jan hannun Azeemar tayi suka ja gefe tana mai watsa musu wani irin mugun kallon daya fadar da gabansu dukah tace''Ga hanya nan ku tafi agaida samarin dandali....!''

Sai suka ji duk kunya ta kamasu don kam gaskia ta fad'a duk wanda ya kallesu tabbas kai tsaye zaiyi tunanin dandali zasu,kukan kura Ruqayyah tayi tare da shak'o wuyar Jameelah tace''Kutmar ubaaaaa! mu zaki ciwa mutunci haka?tou kuwa na rantse da Allah sai munci ubanki da uwarki anan wurin yau tunda ke kika kawo kanki da kanki...!''

Ana cikin haka ne sai gasu Goggo Karime sun danno kai cikin gidan,ganin rikici na neman barkewa tsakanin dangin amaryar da kuma su Jameelah yasa suka nufi wajen da sauri''Kai kai meye haka ku bari,ke sakarta man...'' acewar Goggo Fatoumata,adaidai lokacin manya yan dangin amaryan suma suka nufo wajen don hayaniyar da suke ta jiyowa,bbu wanda ya kula da marin da Jameelah ta yankawa Ruqayyah sbd sauran yan'uwanta da suka rufeta,sai ji kke tass! aka rasa wanda aka mara,,Jameelah ta fashe da kuka tana fadin''Innalillahi baiwar Allah meh namiki haka ne kika mareni?'' cike da mmki ake kallonta hatta wacce ta maran don har kasa magana tayi balle tace zata rama,sauran suka had'a baki sukace''munafuka ta mareki kodai kika mareta?''

KISHIN MATAWhere stories live. Discover now