2

245 1 0
                                    

*KISHIN MATA🍃🍃*
               🍃🍃🍃
         _mai dauke da salo na daban🤙..!_

*ƖŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾى  ASSɷ*✍

   *NA*

         _*HAFNANCY LURF💕*_
           _*[Hafseesee]*_

_*💫Dedicated to:-Anti Bahijjata & Grandma Zm Chubado*_
   
*#An_Intense_Jealousy_Story*
*#Love#fiction*
_•Copy cats ar advised not to transform diz publication by any means_

_#In this article, we will investigate what is going on in the minds of men who seek to marry more than one wife. What are their views on the matter? We also want to know what their wives think about their husbands’ looking to marry again_

         _*💫BABI NA BIYU…✌*_

___________★Akan idon Gidado motoci suka tashi kuma duk yana kallon irin gudun gangancin da Jameelah takeyi da mota asaman kwalta,ahankali ya furta''ke kuwa Jameelah salon naki kishin kenan?tou Allah ya kyauta...!'' komawa yayi inda yabar wasu abokan aikinsa wa'enda basu samu zuwa daurin aure ba shine sukazo tayashi murna da yammacin nan,wasu acikinsu sai cewa suke matarsa ta burgesu ayayin da wasu ke cewa suna tsoro kar tayi fuckup cuz mayb she's upto something freakish,murmushin yake kawai Gidado yayi tare da cije kakkauran lips dinsa yace''I trust my wife bazata ta6a bani kunya ba...!'' daga kafadu sukai suna fadin''Tou Allah yasa,fatanmu dai Allah ya baku zaman lfy dukah..''

Ameen shine abunda ya amsa da kana suka sallameshi shi kuma yayi musu rakiya wajen motocinsu,bayan wucewarsu ne ya koma ciki sai part din mahaifiyarsa *'Yumma'*

Ya cimma jama'a sun dan ragu ah part dinta,tsirarun mutane ne kawai ke zaune ah katafaran falon mai alfarma,bayan ya gaishesu ya wuce dakin Yumma direct,da sallama abakinsa ya shiga cikin dakin,Yumma ce kawai ta iya amsawa don ita da Ramlah kanwarsa ne kadai adakin,fad'a take mata sosai akan cin zarafin Jameelah da tayi acikin jama'a,ita kuwa Ramlar sai kuka take kaman zata hadiye zuciya ta mutu,Yummah na ganinsa ta yanke fadarta bayan ta amsa mishi sallamar,itama Ramlar shiru tayi da kukanta kamar anyi ruwa an dauke,tsit kakeji don mugun tsoronsa take kamar wani mala'ikan mutuwa,

Idonsa k'yam akan Ramlah wacce sai faman ajiyar zuciya take ta saukewa ajere,tun kafin ya karasa wajensu ya doka mata wani irin gigitacciyar tsawa''K…! maza knees down tun kafin na karaso wajen na tattakaki awajen stupid gal kawai...!'' ya fadi da jajayen ido,ai tuni ta zamo daga kan gado jiki na rawa takai gwiwowinta kasa kamar yadda ya umarta,yana isa gareta beyi wata wata ba ya daga hannu zai sharara mata mari,da sauri Yumma ta daga hannu ta tareshi,cike da dacin rai tace''Haba Gidado meye haka ne wai kke kokarin yi?wai kai meyasa idan ranka ya 6aci sai ka nemi ka fita cikin hayyacinka ka koma tamk'ar mahaukaci ne?ni nasan abunda kake wa zafin ran ammh ai yakamata ka dakata tunda ka cimma ina mata fad'a ne,,mutumin banza kawai mtssss...!''

Cike da mmki yake nuna Ramlah yace''Ya rabbi…! Yumma yanzu agaban mara kunyar yarinyar nan ne kike zagina salon ta kara rainani...?'' saurin taran numfashinsa tayi''Kai kana da kunyar ne?ba agabana kke kokarin jibgarta ba?dake kai baka da ta ido dukan d'a agaban idon iyayensa,tou wlh kar inji kuma kar in gani ka sake dukan Ramlah agidan nan,karshe ma daga daketa sai data kwanta jinya dake kai baka da imani ko kadan.....!''

Maganarta ta karshe ya kara fusatashi yace''Ai wlhy bata ma kwanta jinya dakyau ba har sai naga na fasa jikinta da belt tukun idan har bata fita aharkar matata ba,ga matar dan'uwanta nan Azeema da kuma yar'uwarta Surayyah cikinsu duk bbu wanda ya haihu ammh dake tawa matar ta raina shiyasa take takata son ranta kuma ana gani ayi shiru,tou wlh Yumma ki gargadeta bazan sake daukan wannan rainin da wulaqanci ba,ni kowa ya fita daga harkan matata,tunda dai kunsa na qaro wani auran zamu gani ai ko ita din zata haihun ammh adai cin zarafin Jameelah banaso.....!''

KISHIN MATAWhere stories live. Discover now