BABI NA HUDU

153 2 0
                                    

*🍃KISHIN MATA🍃*
               🍃🍃🍃
         _mai dauke da salo na daban🤙..!_

*♟ƖŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾى  ASSɷ*✍

   *NA*

         _*HAFNANCY LURF💕*_
           _*[Hafseesee]*_

   _*💫Dedicated to:-Anty Bahijjata & Grandma Zm Chubado*_

   
*#An_Intense_Jealousy_Story*

          _*💫BABI NA HUDU...🤟☝*_

………! Ah barandar sashin Hajju suka iske ita Hajjun zaune tana jiran isowarsu,hannunta dukah biyun rik'e da wani babban k'warya wanda ruwan magani yayi rabinsa,zaune agefenta kuma Yumma ce,adayan gefen kuma Haj.Karama wato matar Baba Alseny,sai kuma sauran kishiyoyin farfadanta dake tsaye acan gefe,da gud'a aka karaso da Hafsah wajen hannunta sakale acikin na jameelah,Ramlah ta taimakawa Jameelah suka durk'usar da Hafsan agaban Hajju wacce sai faman shesshek'ar kuka take tayi irin dai ta amare,Hajju ta mik'awa Yumma k'warya tana fadin''Ummerherny rika mun nan…!'' Yumma tasa hannu ta karba idonta k'yam akan Hafsa surukar tata,Hajju ta mik'e tsaye dauke da murmushi akan fuskarta ta aza hannunta akan Hafsa tace''yata muna miki barka da shigowa cikin zuri'armu mai albarka,wato zuri'ar *'TSOHO SULEIMANU*' ,,Hafsatu Allah yasa kin shigo asa'a da kuma kafar dama,Allah kuma ya baki ikon bin mijinki sau da kafa da kuma kyautatawa danginsa sannan kuma ya wanzar da zaman lfy atsakaninki da abokiyar zamanki,Allah kuma ya azurtaku da zuri'a zayyaba.....!'' sai jero mata ameen ake tayi,ita kanta amaryar tana ta amsawa ne ahankali,

  Hajju ta cigaba''Akarshe kuma ina rokanki wata alfarma da kika bani dama na gudanar da wasu al'adunmu da muke yiwa duk wata wacce ta shigo cikinmu shi da kuma wacce muka bayar waje wato namu 'ya'ya matan kenan, _*'WANKAN RUWAN KWARYA DA KUMA SHANTA'*_ domin kariya agareki acikin rayuwar aurenki wannan shine al'adar,,shin Hafsatu da mutanenta kun bamu wannan damar?don hakan shine zaisa muyi maraba da ita acikin zuri'armu…!''

  Kai tsaye mutanenta suka ce sun amince,Hajju ta dubi amarya da kanta ke duk'e akasa tace''Amarya inason naji ta bakinki,shin ki amince amiki wannan al'adar tamu…!?'' murya na rawa tace''Naaaa....amin...ce.....!''

Habawa ai sai ko'ina ya dauki gud'a....

   ____________★★

Sauri sosai Baddo take ta raftawa don tazo agudanar da wannan al'ada ta zuri'ar tasu agabanta ta gani sbd ba'a ta6ayi tana nan ba,duk bukukuwan da akai tayi da wayonta dinnan bata samun damar zuwa don alokacin sai kaga tana cikin jarabawa ne,wannan shine karon farko da za'ayi shi agabanta wanda ta dad'e tana ta dokin zuwan wannan ranar,kaya kala uku ne suka wankewa Hajju ita da su Hanifa kannan Kasim tou shine aka kwashe kayan ah igiya aka bata takai dakin Hajjun,wannan dalilin nefa yasa take ta sauri takai kayan dakin sannan ta komo waje tasha kallo,sai ji tayi ta buge mutum ah kofar shiga dakin Hajjun,ninkakkun kayan kanta suka fad'o tare da watsewa akasa,ta daga kai tana duban wanda ta bugen,idonta ne ya sauka akan Gidado wanda ke watsa mata wawan kallo,gabanta yayi wani irin bugawa da sauri ta juya zata koma,ganin hakan yasa yyi hanzarin sa hannu yayo grabing kafadarta cike da mugunta tare da forcing dinta ta waiwayo gareshi,lafiyayyen kwankwashi mai kyau ya zuba mata yace cike da tsanarta''Hegiya kin buge mutum kin juyo zaki koma ba tare da kin bashi hakuri ba dake ni kin rainani ammh na tabbata da'ace wancan abokin iskancin naki kika buge da har rungumarsa zakiyi kina bashi hakuri,come on will u get down on ur knees and say sorry ko kuwa saina fasa bakin tukunnah…!?'' kuka ta sanya masa meh daga hankali tace''kayi hakuri ni wlh bansan da mutum abakin kofar bane....''

''Yar iska kawai ina zaki sani kuwa bayan idanun sun rufe da iskanci?dallah mallama give me way na fita kafin na zaune miki aruwan ciki,dubi abu kamar buhun siminti....'' ya ida maganarsa ah kufule,azuciye tace''Nidai wlh Hamma na gaya maka kabar kirana da er iska ni ba ita bace plssss....''

KISHIN MATAWhere stories live. Discover now