BABI NA TALATIN DA SHIDDA

2K 156 17
                                    


                 🥀NOOR IMAN🥀

*Fatima Muhammad Gurin*
             *Gureejo6763 on Wattpad*

*'Yar Mutan Adamawa*

💫ANNUR WRITERS ASSOCIATION
(Home of peace, honor, charity and super writers)

                        *036*

Cikin tausayawa ta d'aga hannunta da ba Karin ruwa a jiki ta d'aurashi kan kwantaccen sajenshi ta kuma narkar da idanunta cikin nashi cikin kasa da murya tace "hamma!!!" Lumshe idanunshi yayi wani tausayinta da wani abu da har yanzu be tabbatar menene ba na taso mishi, tattausan hannunshi ya d'aura kan nata shima cikin sanyi yace "ki ci abinci pls kinga baki da lafiya" yana kai nan ya zame hannunta tare da maida hannunshi kan spoon ya kuma d'ibowa ya kai mata baki, ba musu ta fara ci.

Anty rahama da Anty kalthum dake gefe suka had'a idanu suna dariya, waya Anty rahama ta d'auko tana cewa "Ina zarah ta tsaya ne daga d'auko kaya har yanzu bata dawo ba, bari In kirata inji" kallon Anty rahama yayi yace "Anty karki kirata zaki sa ta kuka, kalthum zo ki kar'ba ki sayo mata duk abinda kika san zata bukata a supermarket" ya karasa yana karkatawa tare da zaro dubu dubu da d'an yawa yana mikawa Anty kalthum, kar'ba tayi, Anty rahama tace "me ze sata kuka kuma Abdul? Sannan ga sabbin kaya a akwatunanta me yasa za'a sayo wasu kuma?".

Lumshe idanunshi yayi tare da waresu kan Iman dake kallonshi baya so ya sata kuka da damuwa haka kuma bayaso a kira zarah don ya Santa sarai ko zuwa yanzu tayi shiru aka kirata aka tambayeta In har zata bada labari se ta kuma yin kuka, gwara de ita Iman d'in tana gabanshi ne ze san yadda ze yi ya hanata yin kukan sossai, labarin Abinda ya faru ya basu dukda ba in details ba don main point d'in kawai ya fad'a.

Salati suka d'auka a tare Anty rahama tace "Allah ya isa fa? Ka gayawa Abba?" Anty kalthum tace "Toh kwata kwata ma me auta ta sani ina ita ina Allah ya isa?" Idanunshi na kan Iman da tayi kaman bataji abinda yace ba da mamaki yake kallonta ganin bata nuna damuwanta ba dukda kuwa shi yana iya ganin tashin hankalinta a cikin kwayar idanunta, ita kuwa tayi Alkawari bazata kara nuna mishi damuwanta akan fuskanta ta kara mishi damuwa bayan wadda ya sa kanshi a ciki Don ita ba.

Cewa yayi "Ba zan iya ci gaba da fad'awa Abba komai ba, shi karan kanshi yana cikin damuwa ummu ta chanza gabad'aya har a yadda take kula da shi da yanzu kwata kwata batayi, menene kuke ganin ze sauko da ummu ta koma kaman da?" Anty kalthum tace "Hamma ni kam wallahi ban yarda Haka kawai ummu take ba why not mu nema mata magani?" Anty rahama Tace "sannan ni inaga fad'an da Abba da kuma su baba galadima ke mata yake kara tunzurata kan Iman kuma tabbas akwai alamun asiri ko shafan aljannu jikinta, ummu yanzu ko ni da bama kwana bamuyi waya da juna ba tunda na kawo kayan auren nan ko na kirata bata d'auka bare har muyi shawarwarin da muka Saba".

Hafeez ne ya katse maganan da Abdul ke niyyan yi, ba tare da yayi magana ba ya ci gaba da bata abinci yana kallonta, ganinsu jugum jugum yasa ya tambayi me ya faru? Anty rahama ce ta bashi labari, Shiru shima yayi cikin nazari da tunani da gaske kaman yadda sukayi hasashe ne shima yana Zargin In ba asiri ba to fa akwai aljannu jikinta.

"Ga shawara" duk kallonshi sukayi har malabo, "ina da numbern Baba fufore why not mu kirashi mu mishi bayanin duk yadda takeyi ko akwai taimakon da ze iya bamu?" Anty rahama tace "yes hakan yayi ba se mun fad'awa su baba galadima ba kar hankalinsu ya fi na yanzu tashi" abinci ya kai mata baki se ta shagwa'be fuska da gira ya mata tambayar ya? A hankali kasa kasa tace "na koshi Allah in na kara amai zanyi" shi karan kanshi ba don yana kallon bakinta ba da baze ji me ta fad'a ba murmushi yayi yana ajiye bowl d'in, se suka had'a ido da en uwanshi harara ya dankara musu kan yace "ban son gulma da sa ido Allah".

Dariya suka saka har Iman seda ta murmusa yadda yayi maganan kaman irin dama wani gulman suke har had'e rai ya kara yi, kallon Hafeez yayi yace "kirashi mana y ko credit ne baka da?" Anty kalthum tace "haba ya isa manager guda?" Murmushi hafeez yayi Yana dialing numbern baban, bappansu ne wato yayan sarki na yanzu, yaki gidan sarauta Don ko lokacin babansu be rike mukami ba, sede yayi karatun Addini sossai da sossai, jama'a moddibo suke kiranshi wato malami a hausance amma su Hafeez baba fufore suke ce mishi Don duk rayuwarshi a fufore yayi wurin en uwan Mamansu da bata kasance er sarauta ba.

NOOR IMANWhere stories live. Discover now