BABIN KARSHE

2.8K 187 51
                                    


🥀NOOR IMAN🥀

*Fatima Muhammad Gurin*
*Gureenjo6763 on wattpad*

*'Yar Mutan Adamawa*

💫ANNUR WRITERS ASSOCIATION
(Home of peace, honor, charity and super writers)

*056*

END

Bayan wattanni.

Zuwa yanzu an jima da sallaman mama taji sauki sossai se d'an abinda baza'a rasa ba na Ciwon sugar da take fama dashi, auren zahra ya kara matsowa Don yanzu haka saura sati biyu, ta 'bangaren soyayyarsu da Abdulraheem kuwa ba abinda ya ragu se ma abinda ya karu sbd bayyanar ciki a jikinta kulan da yake bata na safe daban na rana daban na dare daban, ta tabbatar da yana da dama ko kuda baze yarda ya sauka a jikinta ba bare har tayi wani ciwo.

Kaman yau zaune take tayi nare nare tana cin grilled fish hankalinta kwance tanayi tana kallon wani film a tashar Bollywood, ringing d'in wayanta ne ya d'auke mata hankali daga kan kallon da takeyi ta duba wayan se taga ummu ce ke kira, da sauri tayi picking tare da sawa a handsfree cikin sabo da so tace "ummun mu Barka da warhaka" ummu tace "Yauwa daughter ya kk? Ya jikin?" A kunyace tace "Da sauki ummu am na warke, ya shirin buki?" Ummu tace "za de ki warke daughter, shirin buki gashinan munayi zakuyi missing bukin autana" Tace "wallahi kuma banji daad'i ba dama muna hutu" ummu tace "haka Allah ya kaddaro, kina de cin abinci yadda ya kamata kam?" Tace "eh......" katseta yayi da cewa "Ina kuwa take ci ummu kullum abincin kenan gasashen kifi na rasa yadda zanyi da ita ta dinga cin abincin" ta tsorata Don sam bataji shigowarshi ba hakan yasa ta harareshi.

Murmushi yayi jin ummu na cewa "Ina zata samu abinda zata ci a garin masu jajayen kunnennan bari ma kaji bazan bari ta haihu chan ba kula ba daga ta shiga watan haihuwa zata dawo In kaga dama kayi zamanka tunda lokacin Hamna na chan" murmushinshine ya d'auke jin magannan ummu cikin rashin fahimta yace "wani irin hamna na nan ummu?" Ya karasa yana kallonta kauda kai tayi cike da rashin gaskiya ranshi ne yaji ya fara 'baci, cikin sanyin murya ummu tace "daughter ki kula da kanki se anjima" ta kashe wayan, duk shiru sukayi na mintuna kan ya daure yace "Saudah me hakan yake nufi?" Nan ma Shiru tayi cikin d'aga murya yace "dake nake!!!" Razana tayi don rabon da ya mata tsawa haka tun ranan a masarautar modibbo Adama.

Cikin sanyin murya tace "I'm sorry za'a mayar da aurenku da Hamna randa za'a d'aura na zahra" kankance ido yayi yana me mikewa har ze yi magana se kuma ya fasa ya wuce a zuciye zuwa d'ayan d'akin dake gidan kwanciya yayi ranshi na suya wai sun fishi sanin abinda yake so ne da zasu yanke mishi hukunci ba tare da saninshi ba? Danne 'bacin ran yayi ta kokarin yi har bacci yayi awon gaba dashi.

Ranan haka suka yini be ce mata ci kanki ba sede ya fita ya sayo mata gasashen kifinta me zafi yazo ya ajiye mata, ze fita kenan tayi hanzarin rumgumeshi ta baya cikin kuka tace "kayi hakuri abinda ya dace ne nayi" in tana bashi hakurin nan ranshi kara suya yake yadda ya tsani hamna da uwarta ace wai za'a mayar mishi da aurenta taya ze yi adalci a tsakaninsu? Zame jikinshi yayi cikin son danne 'bacin ranshi yace "abinda ya dace? Abinda fah ya dace kikace? Kece zaki zauna da ita In ta dawon? Kece zaki sauke mata duk wani hakkin da miji ze bata? Me yasa kika aikata abinda tun farko na haneki akai for the first time a rayuwanmu hayatee kin tsallake umarni da gargad'in da na miki aka gayamiki don Ina sonki se ya kasance duk abinda kike so shi zan yi? Bana sonta na gayamiki bana sonta......" Shiru yayi jin kukanta ya fara hawa kanshi yayi yawan da har numfashinta na fisgewa dama cikin ya bata wahala sossai.

Kan ya kuma wani maganan ta sume mishi a rud'e ya d'auketa se asibiti da hanzari aka kar'beta doctors biyu suka rufu kanta shi kuwa se zirga zirga yake yana jin tsanan hamna na kara yawa a ranshi gashi zata mishi sanadiyar yaro tunda ita duk zamansu bata bashi ba, wadda zata bashin kuma tana kokarin shiga tsakaninsu awansu biyu a kanta ta farfad'o likitan ya fito yana fad'an yace cikin nan lalla'bashi ya kamata ayi Don har yanzu barazanar zubewa yake amma sun ki ji ana barinta shiga damuwa to ya kuskura ta kuma fad'uwa haka tabbas zasuyi asarar babyn.

NOOR IMANWhere stories live. Discover now