BABI NA ASHIRIN DA TARA

1.9K 154 9
                                    


                 🥀NOOR IMAN🥀

*Fatima Muhammad Gurin*
             •Gureenjo6763 on wattpad•

*'Yar Mutan Adamawa*

💫ANNUR WRITERS ASSOCIATION
(Home of peace, honor, charity and super writers)

                          *029*

"Hahahahahhaa Baku da matsala da wannan, Don ko banyi aiki ba akwai me aiki a kanta baze ta'ba kusantarta ba inba an karya wanchan alkadarin ba, in ya matsa kuwa komai ze iya faruwa da shi har ita karan kanta, hahahahhaa" da mamaki Umma tace "wani irin aiki kenan yake kanta boka? Naka ne?" Wani dariyar ya kumayi yace "ba huruminku bane kuma In kun matsa komai ka iya faruwa".

Hamna tace "to boka batun mahaifiyarshi naga kaman ta sakankance da maganar auren ba kaman farko ba" nan ma dariya yayi kan yace "yaro yaro ne, Ai tashin hankalin da muke kara sa mata akan auren ko uwarki wannan bazata iya d'auka ba se ta tsinewa d'an, kaman yadda na gayamuku da farko akwai babban al'amari a kanta duk randa ya karye kuwa ni zan dasa mata nawa, zakuma ki iya tarewa gidansu ba wadda ze ce dake komai a kai, lokacin ku ya kare ku sallameni maza ku tattara ku bar nan".

Kud'i umma ta zuba mishi kan suka mike suna mishi kirari da munmunar kalamai yana washe baki har suka fita, a cikin mota se tunanin wani irin al'amari ne boka ke magana hamna keyi ta kasa Shiru ta fara tambayar umma, umma ce ta hanata tana cewa "baki ji abinda yace ba kar ki matsa da bincike? Toh kar na kara ji kinyi maganan" Shiru duk sukayi ba su suka iso masarauta ba se dare basu san me akayi a gidan da safe ba bare rana.

******

Tunda suka farka daga bacci har sukayi wanka suka zauna karyawa Zarah bata ce komai ba, abin se ya dami Noor cikin jin wani iri tace "Zarah ko akwai abinda na aikata gareki ne cikin rashin sani?" Da sauri zarah tace "ko d'aya wallahi ba wani abu" iman tace "to me yasa kika koma haka? Ko akwai wani abu da ze iya samunki wadda ban kai In sani ba?" Zarah ta kuma cewa "ko d'aya iman ban son damuwana ya shafeki har ya 'bata miki mood kinga yau akwai event wadda shine na karshe, sannan damuwar fa ba wani damuwa bane na azo a gani, in kin koshi tashi mu fara makeup kan waenchan tsuntsayen suzo su damu mutum".

Murmushi Iman tayi kan ta mike kuyangar dake jiran su gama ci ta tattare ta fara tatarewa a tsanake har ta gama ta fice da trays d'in, zama sukayi zarah ta janyo Kit d'inta ta 'bud'e suka fara, ba me cewa komai chan wayan Zarah ya d'auki kara, kallon fuskan wayan tayi da mamaki ta d'ago wayan ganin Muhammad, akan lips d'inta ta furta 'hammad!!' Har seda ya kusa tsinkewa kan ta d'aga.

"Assalamu alaikum" yace "wa'alaikissalam warahmatullah malama zahra" Tace "Ina kwana?" Yace "Lafiya klau Alhamdulillah ya gd? Baki jini ba ko kwana biyu wallahi kuna raina kasar na bari yanzu saukowata hutawa kawai nayi nace bari In kira inji ya abubuwan suke tafiya?" 'Dan Shiru tayi kan tace "normal, Iman tayi Aure da yayana kuma Alhamdulillah ba wani damuwa ko matsala".

Cikin excitement yace "masha Allah na mata murna sossai, Allah ya basu zaman lafiya da zuri'a d'ayyiba" Tace "Ameen, se anjima" yace "wait wait madam Ai ban gama maganan ba" Tace "uhmm" murmushi yayi kan yace "wata biyar aka bani In fidda mata In ba haka ba Amin auren dole...." katse shi tayi da "Allah sarki se ka fitar ba" yayi murmushi ya fahimci ta fuskanci abinda yake son fad'i amma take fuskewa yace "Da farko da naga Iman se zuciyana ya bani duk duniya ba wacce zan iya zaman aure da ita inba ita ba, bazan boye miki ba sonta lokaci d'aya ya shiga zuciyana kaman abin asiri se kuma Mom taki auren namu irin kin da banyi zato ba, se kuma nayi sa'a babba a ranar da na rabu da Iman washegarin na samu wata me irin halayen Iman, duk kwanakin da suka shud'en nan tana cikin raina daram na kasa fidda ta da tunaninta nake kwana dashi nake tashi".

Kwa'be fuska tayi tace "congrats to ni me nawa a ciki ko kasa fad'amata kayi shine zaka wakilceni gani bbc" dariya yayi har Iman seda ta dara dukda ba jin abinda d'ayar bangaren yake fad'a ba take, on top of that bata ma san wayene ba, cewa yayi "a'a ko d'aya, tabbas wakiltanki zanyi zuwa ga Zuciyarki ki bata Sakon zuciyata, zuciyata tace "tana mata so irin na tsakani da Allah" wani irin dariyar rainin hankali Zarah tayi kan tace "Allah ya baka lafiya" ta kashe wayanta tana tsaki.

NOOR IMANWhere stories live. Discover now