BABI NA GOMA

1.9K 153 2
                                    


                 🥀NOOR IMAN🥀

*Fatima Muhammad Gurin*
            •Gureenjoh6763 on Wattpad•

*'yar mutan Adamawa*

💫ANNUR WRITERS ASSOCIATION
(Home of peace, honor, charity and super writers)

                        *010*

Duk kasa suka sauka suna gaida Abban banda Abdulraheem, dayake duk se yanzu suke ganinshi sa'banin Hafeez da tare suka je sallahn asuba kuma sun gaisa achan amma yanzu ma seda ya kara gaidashi, amsawa yayi da fara'a yana tambayansu rahma iyalansu duk da lafiya suka amsa, "auta ina nawa smoothie d'in ko yayunki kawai kika sani?" Ya ja zarah da wasa idonshi na kan Abdulraheem da ya mike zaune daga ganinshi ka san ranshi a matukar 'bace yake sede sam hakan be nuna a yanayin fuskanshi da idanunshi ba sbd Allah yayishi mutum me danne 'bacin ranshi irin Abban.

"A'a Abbana Ai In kana nan Ina na san wasu Anty rahma? Yanzu kaima zan je In maka irin zobon da kake so" duk dariya sukayi Abba yace "yauwa 'yar albarka bari In je parlor na In jiraki" da gudu ta mike tayi kitchen suna mata dariya, wucewa Abba yayi parlornshi yayinda Abdulraheem ya tashi a kasalance ya bi bayanshi.

A kasa ya zauna kanshi kasa yace "ranka shi dad'e barka da rana" Abba yayi murmushi kan yace "yauwa babana ya ayyukan?" 'Bata fuska yayi kan yace "so stressful wallahi ni Abba na gaji da lecturing d'in nan, haba Abba ga aikin gomnati ina dashi, sannan ga business inayi Amma ka sawa mutanen nan hope akan zanyi aiki dasu".

Wannan dattijo Allah ya halicceshi da fara'a murmushi kam be d'aukewa a fuskanshi "Abdulraheem koyarwa fah lada ne dashi ba wai samun kud'i kawai ba, ni da Ina da yadda zanyi na koma koyarwa da na koma, don ma ban saka kayi a secondary school ko islamiyya ba" nyamutsa fuska yayi a zuciyarshi yace Tab!!! Murmushi Abba ya kara fad'ad'awa kaman ya san abinda Abdulraheem d'in ya fad'a a zuciyarshi.

"Rayuwa d'an hakuri ne Babana musamman harkar mata ka kara hakuri amma In kaga zaka cutu ka kara aure, ban de goyi da bayan ka saki matarka ko ka wulakantata ba kaga de 'yar uwarkace" kanshi a kasa yace "In shaa Allahu Abba, bari naje Ina da meeting" Abba ya ce "Toh Allah ya bada sa'a ya taimaka, Allah yayi muku albarka" da "Ameen" ya amsa yana mai jin daad'in adu'ar ya fice.

A parlorn Ummu ya tsaya tare da bankawa su Anty Rahma harara kaman baze yi magana ba kuma se yace "Munafukai kun had'ani da uwata ai kun huta" dariya suka kwashe dashi Hafeez yace "mu de ba ruwanmu ai kun fi kusa wa ze san shiryawarku?" Kalthum tace "yanzu haka se a shirya dashi mu ba'a shirya damu ba" Anty rahma tace "kya fad'a 'yar uwa" kara hararinsu yayi kan ya haura saman Ummun da sallama ya tura d'akinta ciki ciki ta amsa.

Seda yayi murmushi ya girgiza kai kan ya karasa ya zauna a gefenta tare da d'aura kanshi kan kafad'arta yace "Allah huci zuciyar uwa ta gari, ki dena damun kanki plz akan zancensu Kalthum, ba me ta'ba miki 'yar gwal d'inki bare kuma ayi maganar yi mata Kishiya ita kad'aice ba Kari in shaa Allah" a take ta saki fuska tace "yauwa  Son ko kaifa se yanzu na ji magana su kuma kilbabbun chan zasu gamu dani Ina daidai da zamaninsu".

Murmushi ya saki tare da d'an ta'be baki yana mikewa yace "muna neman albarkanku ummu zan wuce" tana murmushi ta shafa kanshi tace "Allah yayi muku albarka gabad'ayanku, ya tsareku daga sharrin masharranci ya bada sa'an aiki" yace "Ameen thumma Ameen" kan ya fice tana bashi sakon gaisuwa wurin d'iyarta.

***********

"Assalamu Alaiki yake ma'abociyar kyau da kwarjini" d'an ta'be baki tayi kan tace "wa'alaikassalam, Ina yini" yace "Lafiya kalau dear ya gd? Ya su ummanmu?" Tace "Lafiya" yace "ya kaman baki gane me magana ba? Lallai na san matsayina wato ko numberna ba'ayi saving ba?" Siririyar dariya ta saki tace "yanzu fisabilillahi ni yaushe nace ban gane me magana ba?" "Toh Ai yadda kike amsawan ne kaman baki gane me magana ba, Toh In kin gane bawan Allahn, me sunanshi?".

NOOR IMANWhere stories live. Discover now