BABI NA ARBA'IN DA BIYU

2.1K 177 50
                                    


                  🥀NOOR IMAN🥀

*Fatima Muhammad Gurin*
          *Gureenjo6763 on wattpad*

*'Yar Mutan Adamawa*

💫ANNUR WRITERS ASSOCIATION
(Home of peace, honor, charity and super writers association)

                           *042*

Seda yayi kissing d'inta son ranshi kan  ya janye jikinshi yana kallon fuskanta, wani kunya ne ya rufeta hakan ya sa ta mayar da kanta chest d'inshi tana sunne kai, sossai yayi murmushi tace cikin sanyin muryanta "Na gode kwarai hamma Allah ya biyaka da mafificin alkhairi" d'agota yayi jin har muryanta ya fara rawa yace "da akayi me ne hayatee?" Tace "batun jikin Mama b......" katse ta yayi "mama ta wuce haka a wurina hayatee sbd ita ta kularmin dake ta kuma rainar min ke tun daga yarintarki har na zo na d'auke kayana so kinga anything for her".

Wani irin blushing take sakewa da ya mugun mishi kyau hakan ya sa shi kama lips d'inshi na kasa yana tsotsa a hankali yana kallonta se kuma kunya ya kamata tasa hannu ta rufe fuskanta, murmushi ya saki kan ya 'bata fuska yace "wayyo hayatee yunwa ze kashe miki ni.." waro ido tayi tace "laaa sorry wallahi na manta shap muje please inyi serving d'inka" yana taune lips cikin tsokana yace "kina nan kina soyayyarki Ina zaki tuna" da sassarfa ta fice yana murmushi ya bi bayanta yana mata wani irin kallo.

Serving d'inshi tayi nan fa ya sa mata darun shi kam hannunshi na ciwo baze iya ci ba haka ta zage ta bashi da da spoon zata bashi nan ma yace baya so da hannunta yake so ta bashi a haka ta bashi da ya koshi maimakon ya ce mata ya koshi se In ta sa mishi ya dinga cizan hannunta kad'an kad'an daga baya kam ma se ya d'an mata da karfi "Ahhhhsss" tace tana yarfa hannunta kallon sha'awa kawai yake binta dashi shagwa'bewa tayi tsakani da Allah har da d'an hawayenta.

Da sauri ya rike hannun yasa a bakinshi ya fara tsotse mata razana tayi zata mike yaki sakinta se ma kafanshi da ya janyo ta, wow sossai yanayin ya ma ko wannensu daad'i da kyar ya lalla'bata ya bata abincin shima da hannunshi, a nan suka shantake har aka kira magrib ya mugun kasheta da soyayyarshi me daad'i da sanyaya rai ba surutu sede kawai actions ita kuwa ta cire kunya ta bashi duk wani irin kulawan da yake so daga ita har shi ji sukayi kaman su zauna su dawwama haka.

Kan ya fita seda ya gaya mata daga masallaci asibiti ze wuce wurin Abba, ta kuwa bashi sakon gaisuwa tace ya ce ma Abban se gobe in Shaa Allahu zata zo ta dubashi seda yayi hugging d'inta again kan ya fice, taji daad'i da bai tambayi abinda ya sa ta bar asibiti bata jirashi kaman yadda yace ba, kaman yadda shima yaji daad'i sossai har ranshi da bata nuna mishi komai akan damuwan da mahaifiyarshi ta sanyata ba, kimarta da darajarta ne suka ninku a ranshi.

Da wannan tunanukan ya karasa asibiti ya samu jikin Abba da sauki sossai su rahama da kalthum suna nan har zahra da hafeez suna nan umma, ummu da kuma hamna ne basa nan seda yaji wani iri da a da ne Abba be da Lafiya haka ummu baza ta ta'ba iya barin kusa da shi ba amma ji bata zo da wuri ba haka tayi tafiyanta, fita yayi ya samu doctor yace a sallami Abban tunda jinin ya d'an sauka in Shaa Allahu ze samu kulawa a gida har ya gama warwarewa haka dae ba Don doctorn ya so ba ya bashi sallama ya kuma tabbatarwa Abdul d'in su tabbatar basu barshi yayi skipping pills d'inshi ba, godiya ya mishi ya taho.

Yana tahowa ya samu mijin Anty rahama da na Anty kalthum sun zo duba jikin Abban da sha tara na arziki gaisawa sukayi cikin mutunci kan yayi musu bayanin an ma sallami Abban ai shi karan kanshi seda yaji daad'i dama ba zaman asibitin yake so ba Hafeez da Zahra ne sukayi jigilan kai komai d'insu mota daga nan Abba ya sauko yana tafiya a natsenshi jere suke da Abdul yayinda sauran suka biyo bayansu har motan Abdul d'in.

Ya bud'e mishi baya ya shiga, su Anty kalthum suka mishi sallama da Allah ya kara afuwa inda ya gargad'esu kar ya ga kafan ko wacce a gidanshi gobe In ma zasu zo su bari se zuwa jibi ko gata a haka dae su da mazajensu suka ja motocinsu sukayi gaba, zahra ta shiga motan hafeez su ma suka nufi gida Abdul a gaba suna binshi a baya, bayan sun isa sunyi parking suka raka Abban nasu har part d'inshi Abdul na kallon zarah yace.

NOOR IMANWhere stories live. Discover now