BABI NA UKU

2.2K 173 7
                                    


                   🥀NOOR IMAN🥀

*Fatima Muhammad Gurin*
               •Gureenjo on wattpad•

*'yar mutan Adamawa*

💫ANNUR WRITERS ASSOCIATION
(Home of peace, honor, charity and super writers)

                      *03*

Hadiza wato mama kenan, zuwan mama da kwanaki kad'an ciki ya bayyana a jikin ummana sossai baba ya d'auki son duniya ya d'aura akan cikin, su inna kam da suka ji labari se kunyan yadda suka dinga mata ya baibayesu suka dawo suna son cikin suma kaman su janyo ran haihuwanshi.

Kwarai umma ta wahala a wurin haihuwa na har Allah ya sa ta sauka lafiya inda ta sameni ba karamin farin ciki su inna da baba sukayi da hakan ba, har mama kaman zata had'iyeni zan iya cewa son da take min yafi na ummana a ganina fa kenan, aka saka min sunan inna "saudah" yayinda mama ta saka min inkiya "Noor Iman" shekaruna biyu a duniya ummana ta kara haihuwa nan ma mace "hafsa" sunan mahaifiyarta ce bata yarda kuma a boye mata suna ba.

Bayan hafsy da shekaru biyu ta haifi Nafeesah daga ita da shekaru biyu ta samu Al'amin se Ihlam yayinda ikhlas ta kasance auta, har rana yi ta yau mama bata samu haihuwa ba kuma sam bata nuna damuwanta akan hakan tunda ta d'aukemu a matsayin 'ya'yanta itama karshe ma kyauntana sukutum baba ya bata ganin yadda take kulawa da ni kamar ita ta tsuguna ta haifeni.

Mun girma da son boko kaman yadda baba ya tusa mana ra'ayin kanmu a had'e yake da sauran 'yan uwana mata yayinda suke tausayamin ganin yadda umma ke nuna halin ko In kula da rayuwana zan iya cewa ban ta'ba mintuna biyu cikakke muna magana da ita ba kwata kwata bata san komai nawa ba.

A haka har na girma nayi wayo maimakon In ji na tsaneta amma sonta da son ta kulani suka shigeni, se in dinga shishige mata tana hantarana watarana har dukana takeyi In na matsa mata da magana In ka shigo gidanmu kaga yadda takemin zaka rantse 'yar kishiya nake a gareta, ban san daad'in uwa ba sam ban san d'uminta ba, ko d'akinta na shiga se ta korani waje.

Ko kitso takeyiwa kannena In naje bazata min ba dukda kwarewar ta a harkar, se de in zauna daga nesa Ina ganin yadda take wasa da dariya da kannena wani lokacin har 'buya nake a bakin kofan ta In ta kallonta Ina hawaye, bata ta'ba sakemin fuska ba wadda nake yawan mamakin 'Anya uwa ce'.

Ina girma suffan jikina na kara bayyana da kyaun da Allah ya bani wadda In ka ganni da ummana kaman photocopy banda kiba haka kuma banda rama jikina a murje yake da kalar fatata me d'aukar hankali sbd a chocolate dinma me tsada ne don haka yawan mutane suke fad'a Ina da dimple guda d'aya a 'bangaren kumatuna na dama.

Hakwarana farare sol kanana da su daga tsakiya kuma wushiryace me kyau, se madaidaicin hancina da kuma madaidaitan fararen idanuna na, Ina da cikar kirji da kuma hips yayinda gashin kaina ya kasance marar tsawo har chan amma baki sidik ga laushi.

Ina jss 2 maza suka fara layi a kofar gidanmu don Allah yayini da farin jinin samari hakan yasa baba ya sha alwashin aurar dani da na gama secondary dukda yadda yake so nayi karatu don nice ta gaban goshinshi yana son cika min burina na zama babbar lecturer a duniya amma yana shakka yadda ake zuwa mishi da magana na har tsoro yake bashi.

Kaman yadda na fad'a a baya tun jss 2 bello ya fara takuramin da nuna yadda yake sona ya kuma tabbatar min baze iya rayuwa ba ni ba, tun Ina shareshi har na fara sauraranshi, Ina cikin zana jarabawata ta kare secondary baba ya kirani ya tabbatar min ba zan ci gaba da karatu ba ze aurar dani In miji na ya yarda inci gaba so in turo da wadda nakeso.

Ba 'bata lokaci na gabatar da bello ya ko yi farin ciki sossai kaman ze had'iyeni da aka bashi ni a kuma lokaci kankani, Ina gama neco aka aura min shi, amma kayan takaici a daren ya sakeni ba tare da wani kwakwaran hujja ko dalili ba, wadda hakan yasa baba da sauran 'yan uwanshi kusa kasheni.

Basuyi la'akari da laifin nawa ne ko ba nawa ba, abunda ya fi yi min zafi kuma son da nakeyiwa bello amma aikin gama ya gama a shekaruna na sha takwas har na zama bazawara, tun baba na had'e min rai bayan dawowanmu gadon kaya, har ya daina ya fara min nasiha a kullum da yadda rayuwa yake da kuma fa'idan zaman aure duk laifina yake gani ba laifin bello ba.

Abun takaicin kuma yawancin nasihanshi na karkatuwa ne ga girman laifin zina wato shima ya yarda da rashin kai budurcina ya sa bello sakina hakan na sani kuka sossai da kunar rai, bayan mutuwar aurena da bello da watanni bakwai na had'u da Ahmad matashin saurayi me ji da kud'i a asibiti muka had'u bamu wani jima muna soyayya ba ya nemi turowa na fad'awa baba ya dinga ci min albarka.

Ba 'bata lokaci aka yi buki aka d'aura min aure da Ahmad, bayan d'aurin aure angwaye sun kasance suna turowa amarensu sakon jin daad'insu amma ni sakon bakin ciki da takaici Ahmad ya turo min, bayan an watse ya kirani a waya ya ci min mutunci akan ni bazawara ce bamu fad'a mishi ba muka cuce shi ashe ni 'yar iska ce, wai ashe yawon iskancin da nakeyi yasa mijinan chan ya sakeni.

Nayi kuka har na gaji da wannan sharrin haka aka kaini tunda aka kaini kullum wulakanci har dukana yana yi sede be ta'ba kusantata ba bare ya san gaskiyata na wahala sossai a gidan Ahmad na wata shidda kan ya sakeni na dawo gida, a lokacin hawan jini ya kama baba, kaman aurena na farko har gida su goggo kamila suka zo gabad'ayansu suka lakad'amin na jaki.

******

Ta'bani da mama keyi yasa ni dawowa daga duniyar tunanin da na fad'a "Iman tashi kinyi bacci bakiyi sallahn isha ba gashi har karfe goma, tashi maza kiyi sallah" salati nayi ina mikewa daga kwancen da nake na fad'a bayi, alwala nayi na fito na samu mama ta gama shiryawa zata tafi d'akin baba da yake itace dashi, sallama mukayi ta fita ni kuma nayi sallahna kan na koma gado na kwanta.

Ruri wayana ya fara yana neman agaji a kasalance na sa hannu na d'aga, Haka kawai wani lokacin se in manta Ina da waya sbd ba me kirana en uwana se na kirasu sbd duk haushina sukeji har gwara hafsy amma sauran kannena da sukayi aure ba me kirana haka goggonina ko na kirasu ba d'agawa sukeyi ba, na rasa kaddarannan kam ni na d'aurawa kaina ko ko Allah ne ya d'auramin.

Sake shigowar call wayana ya dawo dani daga tunanin da na fad'a da sauri na d'aga "salamu Alaikum" na furta cikin sanyin murya, murmushi na saki jin muryan zarah tana cewa "Amma baki da mutunci Noor Iman yanzu bakiyi saving number na ba? Don daga jin yadda kikayi sallaman nan baki san who's in the line ba" cikin murmushi nace "sorry zarah, wallahi shap na mance banyi saving ba amma karki damu yanzunnan zanyi".

"Ni de Allah nayi fushi tun fah d'azu nayi saving numbernki da my besty amma ke bakiyi ba" cikin mamakin halin sangarci irin na zarah nace "amma ke zarah 'yar autace ko?" Tace "yes Anty Rumah, ya Abdul, ya hafeez, Anty kalthum duk auta suke ce min har ummu da Abbu" na lura zarah yarinyace don na tabbatar zan bata akallah shakaru hud'u zuwa biyar amma zan d'auketa kawa don tana da daad'in zama kuma ma ni ta fini kiba da tsawo don duguwace sossai ba kaman ni da nake tsaka tsaki ba.

Itama na tabbatar da ta san asalin shekaruna sede ta fara kirana da Anty, ga aurarrakin da nayi, "Lallai auta nima haka zan dinga ce miki" I bet ta turo baki kan Tace "ni de bazan yarda ba sede my besty" nace "ohkey besty duk yadda kikeso haka za'ayi" "ke gobe fah muna da lectures d'in Dr. Abdulraheem kuma 8, dan Allah kizo da wuri karki yi letting ya koreki" cikin sanyin jiki nace "Ohk dear in shaa Allah se mun had'u, bari na zo na kwanta". Sallama mukayi na kwanta bacci.



                      🖤Gureenjo🖤

NOOR IMANWhere stories live. Discover now