BABI NA HAMSIN DA BIYU

2.3K 158 23
                                    


               🥀NOOR IMAN🥀

*Fatima Muhammad Gurin*
     *Gureenjo6763 on wattpad*

*'Yar Mutan Adamawa*

💫ANNUR WRITERS ASSOCIATION
(Home of peace, honor, charity and super writers)

                             *052*

Da hanzari ya d'auke towel d'in cikin sigan neman tsokana ya d'age hannu sama me makon ta nemi wani abin se ta fara neman kwace towel d'in hadda tsallenta wadda hakan ya bashi muguwar dariya aiko be rike ba ya fara yana kuma d'age towel d'in sama yayin da ya kankance idanunshi yana morewa kallonta hakan, ganin dariyarshi da kuma kallon da yake mata na kara karfi ne yasa ta hankalta da abinda take aikatawa da azama ta shige bayanshi ta rungumeshi tare da 'boye fuskanta a cikin bayanshi tasa hannu biyu ta zagayo cikin shi.

Murmushi ne ya subuce mata jin har yanzu dariyarshi yake, rana na farko kenan da taga ya jima yana asalin dariya ba murmushi da ya saba ba wadda hakan itama ya sata jin sanyi har cikin ranta, muryan shi ta tsinta yana cewa "oh hayatee come on zo ki kwace kayanki mana ko kin hakura..." da wani irin murya yake maganan, cikin shagwa'ba da bubbuga kafa kasa tace "uhm uhm zaujii bana so" murmushi yayi yace "Toh zo kici gaba da wankanki" Tace "uhm uhm se ka fita plssss" yace "Toh sakeni In fita" nan ma ta kuma cewa "uhm uhm sede fa ka juya mu tafi a haka kana fita In rufo kofa" siririyar dariya ya saki yana cewa "Lallai ma hayatee toh me zaki 'boye min me ban gani ba? Ko se na siffanta miki yadda duk wani hallita na jikin ki ya....." katse shi tayi da wata shagwa'ba me kashe zuciya "uhm uhm ni Allah bana so zaujii ko kayi shiru ko Inyi kuka" Murmushi ya saki yana kama baki yace "errrh Abdulraheem kama bakinka kan Sarauniyarka ta fara rigima Don bazaka ji da daad'i ba".

Dariya tayi da ita d'in makale bayanshi ya juya suka fara tafiya dariya abinda ta sa sun ya ke bashi, in ba gulma ba bayan ta gama tsalle yanzu a gabanshi kuma ta koma bayanshi wai bata so ya ganta, suna isa kofa maimakon ya fita se yayi wuff ya juyo ta wadda hakan ya sata tsala mishi kara ta kuma shigewa jikinshi dariya ya kuma saki, ya rungume ta tare da kissing kumatunta yace "can't love you less hayatee, My drama queen" sakinta yayi zata kuma makaleshi yace "kinga idanuna rufe suke ba ganinki nake ba" kallon idanun tayi aiko rufe suke a ganinta fa kenan amma shi fess yake ganinta, murgud'a mishi baki tayi tana d'an hararanshi seda ya fita ta rufo kofa tukun yace "I see that!!! Kuma se kin gayamin da wa kike Allah ya fito dake" baki ta kama tana zare idanu tana jinshi yana waka har ya fice.

Murmushi tayi tana sauke ajiyar zuciya kan ta koma ta karasa wankanta ta fito mai ta shafa tayi feshe feshen turarukanta masu bala'in kamshi da sanyi atampha ta d'auko zata saka se kuma ta fasa ta d'auko less riga da zani wadda d'inkin rigan ya had'u karshe leshin ma kana gani zaka san ba karamin kud'i ke gareshi ba, gashi purple and pink ba karamin amsanta yayi ba, haka nan ta tsinci kanta da shafa powder ta saka kwalli tare da shafa pink wet lipstick a saman lips d'inta a hakan ba karamin kyau tayi ba tayi wani fresh da ita kamshinta na amare ya bule ko Ina ya had'u da na turaren da ta saka bayan ta gyara d'akin kan shiganta wanka, d'aurinta ta kafa kan ta mike ta fito parlorn saman ba kowa se tvn dake kara.

Kitchen ta nufa Don wani irin yunwa ta tashi dashi don ma ta sha tea cikin dare had'e da magani, freezer ta bud'e ta fiddo kaza ta ajiye tana kokarin fiddo kayan miya ne taji an rungumeta ko bata juyo ba ta san waye daga kamshin sassanyar turarenshi da take bala'in so, juyowa tayi tana murmushi ta sakala hannayenta bisa bayan wuyanshi tare da karya kai tace "zaujiiii" ta wani ja sunan har cikin ranshi yake jin amsa kuwwan muryanta me matukar kashe mishi jiki da bud'e mishi duk wata kofa ta tsikar jikinshi In ta kirashi da zaujiin nan.

Wani irin mahaukacin kaunanta ke kara ninkuwa cikin rai da zuciyarshi, kasa amsa mata yayi se gira da ya d'age mata yana me kallonta musamman pink lips d'inta, motsa su tayi tana cewa "yunwa..... bari In girka mana abinda zamu ci" seda ya tsotse lips d'innan da suka tsone mishi ido kan yace "ummu says karkiyi girki ki shirya muje gidanta, and am sorry zan sake baki wahala Abba yace mu shirya zamu tafi yola gabad'aya".

NOOR IMANWhere stories live. Discover now