page 7

297 19 0
                                    

🏨KURMAN GIDA🏨

     NA

Rashida Usman
       (Rashma)
________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w

_*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_

Page 7

بسم الله الرحمن الرحيم

     Juyawa ta yi ta koma gida ba tare da ta siyi abinda zata siya ba gaba ɗaya jikin ta ya gama mutuwa dan gani takeyi ba dagaske bane abinda ta gani fatan ta ace mafarki takeyi ba ƙanwar tace ta gani a cikin wannan muguwar shiga ba har ta isa gida jiki a sake ba kowa a tsakar gidan duk sun shiga sallah ita ma ɗakin su ta shiga ta yi alwalla ta yi sallah sannan ta dawo falon su ta zaune cikin ƙannen ta sai momy dake gefen "momy wai har yanzu Husaina bata dawo ba?"

    "Ai kinsan ta bata son zama gidan nan tafi gane ma zama gidan yaya shima baban ku ɗazu ya gama faɗan baya son zaman da takeyi dan dai ba yanda zaiyi ne."

    "Ai nima dan bana son barin ki ne da nima na gudu gidan aunty A'isha."

     "Gara dai ki zauna dan bana iyawa da ƙananun maganganu gidan nan kinsan halin mamanku yanzu zata ce naga malam baya da shi na fara tura ku karuwanci dan ma malam baya yarda da ƙananun maganganu ai da.    yanzu gidan nan ya zama filin yaƙi."

    Taɓe baki Hassana ta yi ta ce "Allah ya kyauta kawai amma nikam nafara gajiya da shirun gidan nan."

    Momy bata tanka ta ba ta fara linke kayan Imran miƙewa Hassana ta yi tana cewa "Imran zo muje ka rakani na siyo taliya muci koda manja ne."

     Daga haka ta miƙe ta saka zumbulelen hijabin ta duk da dare ne amma saida ta ɗaura niƙab ɗin ta da kallo momy ta bisu har suka fita akan farar kujera ta sami Baba zaune gaida shi ta yi ciki_ciki ya amsa mata kamar yanda yake amsa gaisuwa har ta wuce shi ta ji ya ce "ina zaki da daren nan kinsan bana son yawo?"

    "Baba taliya zan siya yunwa muke ji."

    Bai tanka ta ba kuma bai ɗago ba hakan ya saka ta fahimci bayada abin cewa hannun Imran ta kama suka fita yanzu kama shagon Isa a buɗe yake sanyi jiki ta yayi ganin yanzu ma bata ga Hayat ba maganar zuci ta fara "wai kodai bayada lafiya ne amma kam yana lafiya baya zama cikin gida irin wannan lokaci, wata zuciya ta ce mata wai ina ruwanki da shine ki rufa wa kanki asiri."

     Tsuki taja ta tsaya daga nesa da shagon dan duk maza ne sun zagaye shi kuɗin ta miƙwa Imran ta ce "je kace abaka taliya guda biyu sai manja rabin kwalba kayi sauri ina jiran ka."

    Karɓar ya yi ya tafi bai jima ba ya dawo riƙe da leda karɓa ta yi suka tafi tana zuwa ta dafa musu ta ɗibarwa kowanne ɗaki ta aika musu sukuma suka ci a tire ɗaya sallar isha sukayi sannan suka zauna suna fira lokacin mamy ta shigo musu sukayi firar a tare sai ƙarfe tara suka tashi washe gari ma da tazo tafiya bata ganshi ba duk da tana jin wani iri haka ta daure ta tafi tana ƙaryata zuciyar ta.

     Kwanan su Hayat uku suka dawo gida cike da kewar ƴan biyu DEEDAT Nu'yam da Nu'ayma da kuma rayuwar gidan mai cike da farin ciki zaune suke dukan su sai labarin ƴan biyu Hayat ke basu sukuma suna ta dariya wayar Mubeena ce ta yi ƙara ɗauka ta yi ta kara a kunne "ya to ka shigo mana."

   "Ok to gani nan." Daga haka ta sauke wayar ɗaki ta shiga ta ɗauko mayafi ta fito "Aunty Mubeena na zo na raka ki?"

   Girgiza kai ta yi "zo muje autan Momma ba kowa bane ya Abba ne magulmaci."

     Murmushi ya yi yana shafa sajen sa  "a'a tafi kayanki idan ma naje ya Abba zai koroni jeki kayanki."

    Fita ta yi tana murmushi "Momma wallahi Ya Abba soyayya sukeyi da Aunty Mubeena."

    Dungure masa kai Fatima ta yi tana cewa "dalla can banza rufewa mutane baki magulmaci."

    Gurin ya shafa yana turo baki "ni kam gaskiya Dady ya muku aure na huta da wannan cin zalin da akeyi Mani a gidan nan, koma mutum ya samu ya yi aure duk kumbo kun kananaye komai ni wallahi nagaji."

     Filon kujera ta wurga masa be same shiba ta miƙe ta ɗauko gasar waya ai da gudu ya tashi ya fita "da ka tsaya kaga yanda zanyi da kai marar kunya kawai."

     "Bafa zai yuba keda Nury kunsa min yaro a gaba da fita haba."

    "To ai Momma a gabanki yake mana rashin kunya ni dama anbuɗe masa shago a ƙofar gida ko mun huta."

    "Cab yarona sai kamfani yarinya wane irin shago."

    Hayat kuwa saida ya leƙa su Mubeena sunata firar su taɓe baki ya yi ya ce "Wallahi Dady zangayawa ya yi sauri ya muku aure kar ku ƙone ma mutane."

     Marfin motar Ya Abba ya buɗe ya fito ai da gudu Hayat ya fita har yana wucewa da butar da mai gadi ke alwalla da ita "ƙaramin ɗan iska ai da ka tsaya kaga yanda zanyi da kai."

    Bai tsaya ko ina ba sai teburin Isah me shago hannu ya bawa abokan sa suka gaisa a nan suka zauna suna fira fitowar ya Abba ne ya saka shi ɗaga murya yana cewa "masoyi baka bani kuɗin zance ba."

    Gefe ya samu ya faka motar ya fito fari ne kamar Hayat dogo ƙaƙarfa yana sanye da manya kaya sun masa kyau sosai sai gashin sa da yasha gyara naɗe hanayen rigar sa ya fara yana cewa "yaron nan idan ban lallasa ka ba,bazaka shiga hankalin ka ba."

    "Ah tsaya mr man me zakayi ka rufawa Momma así taga jikoki na idan ka daken wallahi mutawa zanyi."

     Ya Abba be kula shi ba ya ƙara matso shi ihu ya buga ya antaya da gudu girgiza kai ya yi yana cewa "naga ranar da zakayi hankali ƙaton banza."

   Daga haka ya juya ƴan shagon sai dariya sukeyi saida yaga tafiyar ya Abba sannan ya dawo yana dafe ƙirji dariya wani Bashir ya yi yana cewa "haba man ya dai da guduwa?"

   "Ai bakasan halin wannan jibgegen ba yanzu nan zai min bugun ƙatti."

     Washe gari sauri takeyi tana ta haɗa kayan aikin ta cikin jakar da zata tafi da ita sai kallon agogo takeyi  ko karyawa bata yi ba ta fito a ƙofar gidan su ta gansa tsaye yana sanye da kayan sport  daga gani daga gurin gudu ya dawo "Dr kin makara yau gashi har bakwai da rabi yi sauri na raka ki."

     Bayan ta tsakiya kalla ta gani ko baba baya nan  numfashi ta sauke data ga ba kowa da sauri ta fara tafiya bayanta ya bi yana mata surutu har suka kai bakin hanya ya tare mata a daidaita ta shiga ya mata adawo lafiya ya juyo ya koma gida ya kusa cin karo da wani "kai dan ubanka kada nasake ganin ka da ita tawa ce......."

    Ko waye wannan mutumin?

    Kuyi maneji munkoma makaranta yau dama kunsan bana typing weekend saboda makaranta insha Allahu sai Monday zakujini.

It's Rashma

   

KURMAN GIDAWhere stories live. Discover now