page 21

288 26 3
                                    

🏨KURMAN GIDA 🏨

        Na
Rashida Usman
     (Rashma)

________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w

_*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_

Page 21

بسم الله الرحمن الرحيم

  Har ta shiga cikin gida tana masifa ita dai Salma batace mata komai ba sai kallo da ta bita da shi gajiya ta yi ta shiga gidan su zaune ta sami baban ta ya dawo daga aiki har ƙasa ta duƙa ta gaida shi sannan ta cire hijabin ta ta shiga Kitchen ta karɓi aikin da Umma keyi ita kuma ta fito tana share zufa kusa da Baba ta zauna "wash Allah na duk jikina ciwo yake min."

    "Sannu ai kuna ƙoƙari girki ba abu bane mai sauƙi bare gaki da lalura ai kin kusa sauka ki huta."

   Murmushi ta yi tana shafa cikin ta da ya zama titsetse haihuwa yau ko gobe "tabbas na tabbata haihuwa rabo ce sai wanda Allah ya so yake bawa sannan kuma sai lokacin da ya ga dama yake baka kaga fa Baban Salma magani wane iri ne bansha ba akan nasami ciki amma duk a banza saida lokacin ta ya yi sannan na samu."

   "Haka ne wani rabonsa yana nesa wani kuma kusa yake mu ƴan Adam dama munada gajen haƙuri akan abinda muka ƙwallafa rai."

  Haka suka ci gaba da firar su saida aka kira salla sannan Baba ya yi alwalla ya fita koda ya dawo Salma ta gama jera komai cikin kwano ɗaya suka ci dukan su uku cikin farin ciki da jin daɗi  kwantawa Salma ta yi akan cinyar Umma tana shafa cikin ta ta ce "my baby kaci tuwo ka ƙoshi babu abinda kake so?"

   Aiko kamar ya sani ya motsa murmushi ta yi har sautin ta na fitowa yawwa my baby tunda ka ƙoshi ka gyara kwanciyar ka zan baka labarin abubuwan da nayi yau." Dariya ta yi sannan ta fara ce wa "my baby yau da safe naje makaranta boko koda naje na makara hakan ya saka akayi min bulala saida nayi kuka hakan ya sa kaina ya yi ta min ciwo kuma ina dawowa naje islamiyya na iya hadda hakan malamin mu ya bani alawa kuma na kawoma taka da aka taso makaranta muka haɗu da Fadila muka dawo ta re shine na samu Umma na saka mun kai aiki bari naje na ɗauki ma taka sweet kasha."

   Aikuwa ya motsa dariya ta yi har jerin haƙoran ta suna bayyana girgiza kai Umma ta yi ta ce "ni kam bansan yaushe Salma zata girma ba shekara sha bakwai amma kullum sai ta ɓara takeyi."

   Dariyar jin daɗi Baba ya yi yace "ki barta mana ai sun saba firarar su tuna daga lokacin da ta san kinda ciki."

   Sweet ta dawo da ita guda biyu ɓarewa ta yi ta ce "Umma ha."

   Ba musu ta buɗe ita kuma ta saka mata komawa ta yi ta kwanta ta ɗora hannu akan cikin daga nan bacci ya yi gaba da ita kwalliya Fadila ta caɓa ta saka wani wando da riga wando iya gwuiwa rigar kuwa iya karta cibiya gashin ta ttare ta ɗaura shi a tsakar kai sai ya sauko yanata yawo a gadon bayan ta   ko sallama bata yiwa kakar ba  ta fita  wata danƙareriyar ce ta faka ƙofar gidan su bataji kunyar mutane dake zaune a gurin ba ta shiga mota suka ja suka tafi sunyi nisa  da tafiya kamar waɗanda zasu bar garin Kano ya ce "wai haryanzu ƙinƙi shawo min kan ƙawar nan taki?"

    "Saminu kenan kai angaya ma shawo kan Salma abune mai sauƙi Salma fa ba irin sauran ƴan mata bane da nake ƙawance da su na sati biyu uku   sun bani yarda amma Salma mun kwashe shekara biyu da ita amma ko bakin titi bata yarda ta raka ni."

KURMAN GIDAWhere stories live. Discover now