30

245 13 0
                                    

🏨KURMAN GIDA 🏨

        Na
Rashida Usman
     (Rashma)

________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w

_*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_

Page 30

بسم الله الرحمن الرحيم

    "Ko ubanka da ya nuna taurin kai yau yana ina?"

    Murmushi kawai Hayat ya yi ya fita kai tsaye gidan DEEDAT  ya nufa koda ya je ya sami su Sa'imah sun dawo sosai ya yi mamaki dan bai gaya masa yau zasu dawo ba cikin fara'a yake gaisawa da su yana jan yaran da wasa da duk sun girma Nu'ayma ta zama ƴan mata sai Nu'aym shima yama fi Nu'ayma tsawo kai kace shine yayan ta  kamar ba su ba sai mamaki yakeyi girman ɗan adam ba wuya wani mata shi ne ya shigo wanda bazai wuce shekara ashirin da uku ba sanye take da ƙananu kaya sun masa kyau sosai gaida Hayat ya yi sannan ya ce "baby zo muje ki raka ni gidan su abokina."

    Kallon sa Nu'aym ya yi yace "gaskiya dai anji kunya Ya Jenio karasa wanda zai raka ka sai wannan marar kunyar bayan haka ma kayi ta yawo da mace."

    Kansa ya nufo aiko ya tashi ya koma bayan Sa'imah yana ƙunshe dariya "Allah Nu'aym ka bari na kama ka sai na zane ka badai ka gama raina ni ba ko?"

   Daga bayan Sa'imah ya ce "ai gaskiya na faɗa........."

    Jin saukar dundu ya saka shi rashin ƙara sawa juyowa ya yi domin ganin wanda ya masa wannan dukan tsaye yagan ta riƙe da ƙugu baki ya turo yana cewa aunty Nu'ayma to ai da wasa nake yi."

    Dariya Gwaggo ta kwashe da ita da take fitowa daga wani ɗaki "kai ba ka rantse bazaka saka musu na gani ba kamar yanda kowa ya saka musuba ai har naman jikin ka zasu iya yagalgalawa."

    Baki ya turo yana hararar ta murmushi ta yi "ai bansan kana hararata ba sai naga idanun ka sun faɗo ƙasa maitsawo kamar daren Salla."

    Aiko dariya ta ƙwacewa Hayat dan tun ɗazu danne ta yakeyi "yoooo eh mana ɗan albarka baka ga duk gidan yafi kowa tsawo kamar fal waya gashi babu ƙiba nifa gani nake idan yana tafiya iska tana kaɗa shi shiyasa idan ana hadari bana so ya fito dan gani nake yi sama zatayi da shi kamar leda."

    Aiko duk ɗakin dariya akeyi shikuma Nu'aym ya cika fam kamar zai fashe fauuu ya wuce aiko Gwaggo ta ce "idan ka iya kafi jirgi gudu ɗan neman mai zuciya kamar kuturu mai falfalelen kai ni inaga ma sai an haɗa da gida da mota sannan zamu sami mai kwasar ka."

    Dariya sukeyi sosai Jenio kam hannu Nu'ayma ya kama suka fita suna dariya shikam Nu'aym sai cika yakeyi Hayat kam duk birge shi sukeyi family suna burgeshi barin ma Gwaggo da ta shiga ransa kai tsaye kallon Hayat Gwaggo ta yi ta ce "nikam wannan mai jajayen kunnuwa yana yimin kama da wance abokin mata da ya fita."

   Kallon ta ya yi yana murmushi sannan ya ce "ai ƙanina ne Mama."

   Tsuke fuska ta yi tana turo ɗan kwali gaba alamar rashin mutunci dariya ya yi sannan ya gyara zama ya fara bata labari abinda ya sani aiko ɗan kwalin ta tuge ta ce "kai ɗan nan ka iya sharo ta yanzu matar da ta rasu a hannu na kace wai ƙanwar babanka ce wai kuma tana nan da ranta haba malam jatau da saura na."

    Murmushi DEEDAT ya yi da shigowar sa kenan ya ce "Gwaggo kenan dagaske yakeyi yanzu haka na tura driver ya ɗauko su sun sauka tun muna can ta yi niyar zuwa amma na ce ta bari zasu zo."

    Wata uwar harara ta rafka masa ta ce "ai dama ba tunyanzu ba ka rainani jan ƙosai kana maidani wata sha tara kafa kiyayeni."

     Tsuke fuska ya yi kamar yanda suka saba indai suka haɗu "wai me yasa kike min haka da girmana da yarana zan dama_ zan dama amma kina ƙaryata ni."

    "Yoooo har wani girma ne da kai kamar bansan lokacin da kayi zama tuzuru ba."

   Miƙewa Sa'imah ta yi tana girgiza kai dan tasan indai Gwaggo ce tana gamawa da DEEDAT zata dawo kanta da kallo Gwaggo ta raka ta tana taɓe baki har ta ɓacewa ganin sa juyo wa ta yi ta kalli DEEDAT cikin ƙasa da murya alamar gulma  ta ce "nidai wannan matar taka akwai abinda yake damunta kaje ka jiyo mana dan ina tambayar ta zata hau kaina gaba ɗaya daga ita har Indo sun gama raina ni damar ma inada su Audu masu sona kawai dai nafison gidan wannna tsaƙurar matar nan taka ne shiyasa nake zama na anan amma sai yanga take min."

    "Wai shawara kike bani ko kuma ƙarar ta kika kawo min mu bamu ma gayyace ki ba ki tattara ki koma Dubai ko Saudiyya."

    Dundu ta sakar masa tana cewa "ai dama na daɗe da sanin baka so ina zuwa kuma kayana ma zance a tattaro min na dawo kenan."

   Ba tare da ya kula ta ba ya bi bayan matar sa ya barta tana mita dawowa kan Hayat ya yi suka ci gaba da fira shidai sai dariya yakeyi suna firar su Momma suka sauka da mamaki yake kallon su  ganin gaba ɗaya gidan suka tattaro Jawahir na ganin sa ta riƙa zillo daga hannu Momma murmushi ya yi ya karɓeta yana cewa "an mata na an girma."  Zama sukayi Gwaggo sai washe baki takeyi sam bata gane Ammi ba ita kuwa sai kallon ta takeyi duk da ganin da ta mata da dare kuma tana cikin mawuyacin hali suna cikin gaisawa Sa'imah da DEEDAT suka fito gaisawa sukayi mai aiki tana ta kai kawo tsakanin Kitchen da falo kafin kace me ta cika musu gaba da kayan motsa baki Nu'aym ne ya fito da yaji haniya mutane cike da girmamawa ya gaida su ya ja hannun Hafsat yana mata wasa suka fita da mamaki Amjad yace "ikon Allah yarinyar da bata yarda da kowa shine harda binsa su fita."

    Caraf Gwaggo ta ce "indai wancen dogon ne duk ƙiwar yaro idan ya tara hannu tsab zai yarda dashi."

    Ammi kam gajiya ta yi tace "mama baki gane ni ba halan."

   Cike da firgici ta kalle ta duk da Hausar Ammi ta gauraya da larabci amma bazata taɓa manta ta ba tsaye ta miƙe take taga kammani ta suna bayyanar mata cikin rawar murya ta ce "yarinya kece kodai mafarki nakeyi ne."

   Wani abu Ammi ta haɗiye ta ce "Mama nice Allah bai ƙaddara kwana sun ƙare ba da sauran kwanaki na a gaba."

   Take Gwaggo ta fara sharar hawaye tana basu labarin abinda ya faru duk shiru sukayi suna jin labari Gwaggo uwar labari har labarin rayuwar su saida ta basu duk tausayi ta basu su Momma kam harda sharar hawaye Momma ce ta yi ƙarfin hali ta ce "to ina yaron nawa yake?"

   Hawaye ta goge sannan ta tsuke fuska "wai kafi mata ya fita shida ƙanwar sa wai zata raka shi gurin abokin sa."

   Da mamaki Momma ta kalle ta tace "yaron nawa ne kafi mata?"

    Zama ta gyara ta fara cewa "kedai tayani duba yarinya duk wani abu da mata keyi ya iya shi hatta da kwalliya shi yake ma waccan koɗaɗiyar yarinyar can mai kama da zabaya."

    Kai DEEDAT ya girgiza a ransa yana cewa jita kamar ba yanzu ta gama kuka ba, su Nu'ayma ne suka shigo bata ma lura da mutane ba kawai muryar Gwaggo ta jiyo tana ce mata zabaya "ni na rasa me na tsare miki kike saka mana idanu idan kika yi wasa zan ɗaure ki na saka a jirgi ya kaiki Dubai duk kin damemu."

    "Rabu da ita baby basai kin kaita Dubai ba kurukukun Dady kawai zamu kaita kona kwana ɗaya ne......."

   Ai kafin ya ƙara sa ta ɗora hannu akai tace "haba kafi mata kaji tsoron Allah kaifa matsalata da kai mugunta............

It's Rashma

KURMAN GIDAWhere stories live. Discover now