33

201 15 3
                                    

🏨KURMAN GIDA 🏨

        Na
Rashida Usman
     (Rashma)

________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w

_*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_

*Assalamu alaikum!!!*

*_Ina kuke masoya ma'abota son gyaran jiki🗣️🗣️🗣️Ina kike uwargida ran gida sarautar gida sannan sarautar mata,👌😉Sannan ina kike amarya amarsu bakya laifi ko kin heke d'an masu gida😜😉Ina 'yan mata iyayen son gyara da qamshi👌😉To ku matso dukanku kuji nesa tazo kusa._*

*Ku bud'e kunnuwanku kuji hanya mafi sauki da zaku bi domin dawo da martabarki amarya da uwargida haka 'yan mata ba muna mata ba,wannan sirrin na wayayyiyar mace 'yar kwalisa ne*

*K&A SOAP* _Shine sirrin mata iyayen son gyara,Wannan sabulu ne na gyaran jiki Wanda kesa kyawun mata tayi santsi tayi laushi kana fatarki tayi fresh duk Wanda ya gani sai ta Burgesa._

*K&A* *SOAP*

Muna aikawa ko wacce jaha ga masu buqata zasu ne memu ta wannan number domin qarin bayani 09031974044.

*K&A* *SOAP*
*Shine sabulun gyara na musamman 'yan uwa.👌💃💃💃💃

Domin neman qarin bayani👇
  09031974044
*Sai kunzo.*

Page 33

بسم الله الرحمن الرحيم

      Murmushi Sa'imah ta yi "anriga da an horar dasu da haka domin kuwa da su tona asirin su gwanda ka kashe su."

    Jinjina kai ya yi sannan ya kalli Hassana kafin  ya yi magana ta riga shi da cewa "nikam ai na zame mu ƙasa garen bakin tulu idan aka barni na ɓata ruwa idan kuma aka matsa akace sai an kashe ni a fasa tulun hakan ya saka suka rasa ta inda zasu ɓullo ma lamari na tun bansan kaina ba na fara ganin abubuwan akan Mama saidai kuma miskilanci na ya hana nayi magana wanda ya samo asali daga mahaifin mu wanda ya kasance mai tsanani sosai baya wasa da yaro bai damu da damuwar mu ba sannan kuma bamada ƙawaye bare na fasa zancen saidai yana ta cin raina Baban mu babban malami ne hakan ya saka duk wani ƙyale_ƙyale na duniya ba'ayin sa a gidan mu a haka muka saba da wuya kaga murmushi a fuskar ɗan gidan mu hakan ya saka ake ce masa KURMAN GIDA saboda yana yin gidan mu indai kai ba mahaddaci Alƙur'ani bane to kada ma ka nemi aure domin bazai baka ba duk wannan taka tsantsan da yakeyi da iyalin duk dan ya kare su daga shiga wuta ashe bai sani ba yanada bokanya a cikin gida kuma ana masa tsafi a cikin gida ana shan jini a gidan sa hakan ya saka na ƙara tabbatar da lallai GIDAN mu KURMA ne baya ji wata irin rayuwa akeyi a cikin sa na takura ma Mama ƙwarai da gaske domin kuwa na addabeta har na kiyaye lokacin da take tsafin ta ni kuma lokacin nake raɗaɗa murya nayi ta karatu sai kuwa ta gigice ta fito ɗakin ta idanun ta jajir ni kuma sai nayi ta dariya wannan dalilin ne ta saka min karan zuƙa na fara rashin lafiya a cikin ciwon ne naje ɗakin ta ita kuma tana waje bincike na fara da ƙyar na sami sarƙar da naga tana sakawa sannan ta fara shaiɗan cin ta ɗauke ta da nayi naga tashin hankali domin kuwa har ƙaramar hauka saida Mama ta yi ni kuma ciwon da nake fama da shi ya ƙaru hakan aka ɗauke ni da ga gidan zuwa Abuja gurin Yayar mamana cikin ikon Allah na sami sauƙi a nan Abuja na tashi amma a kullum hankali na yana gida duk da ana fita dani kusan kullum amma hankali na ya gagara kwanciya har dai suka dawo dani sannan hankalina ya kwanta a nan na saka ma Mama idanu sosai da mutane dake  zuwa gurin ta a nan nake jin karɓar sarƙar dake hannu na wanda  itace makullin su har yau idanun su a kaina ya ke sannan akwai wani Abu da ya haɗa su da Dady su Hayat domin kuwa naji Isa mai shago yana cema Mama Dady yana da taurin kai sai an ɓullo masa ta wata hanya nidai a lokacin ban tsanan ta bincike ba bare na gane wani abu dan a lokacin banma sanku ba duk da tsanani Baba haka matar nan take fita tana tsula iya shegen ta kuma bai taɓa kamata ba kai har yaranta basu sanda komai ba domin kuwa ta iya takunta sosai."

     "To yanzu ina zamu sami ita manga?"

    "Gaskiya ni yanzu bana ce ga inda take ba saidai Isa ko wani da suke cewa Alhaji Garba a nan yake Kaduna."

    "Alhaji Garba yana hannu mu saidai shi Isah baya hannu mu."

    Murmushi Hayat ya yi yace "ai Isah ya daɗe a hannu na yanzu haka yana lagos."

   "To sune zasu gaya muku inda take amma fa saida ta ka tsan_tsan domin nasan haɗarin Mama da abinda zata iya akan kanta bataƙi ta kawar da kowa ba."

    "Shike nan ku tashi muje insha Allahu ƙarshen su yazo duk da girma ya kamani amma dole ne tsaya tsayin daka domin ƙasata."

   A haka suka dawo gida duk kallon yaransa yakeyi kowanne su ya nufi makwanci sa washe gari suna gama shiri suka nufi gurin Alhaji Garba har da Hassana amma banda Sa'imah yana ganin ta kuwa ya shiga ruɗani ya gagara zama sai kace mai cutar basir duk share shi sukayi zama sukayi Hassana kuwa ta kafe shi da idanu ko ƙiftawa bata yi hakan ya ƙara ruɗar da shi "Abba me Dady ya tsare maka a duniyar nan?"

    Kame_kame ya fara yama kasa zama bare ya yi magana tsawa DEEDAT ya daka masa hakan ya saka shi ɗan nutsuwa murmushi Hassana ta yi ta ce "tsoho ka tuna magana ta ta yarinta a lokacin da nasha kama ka da Mama kuna masha'a na ce maka akwai ranar da nice zan zama ƙarshen wannan ƙungiya ta ku a wacan lokaci kun ɗaukeni yarinya bansan me kukeyi ba sannan ka tuna ranar da nagan ka da mama tana gaya maka tana don ɗan ɗana zumar ƙanin ka dake indiya har ta maka alƙawarin baka babban matsayi a ƙungiya."

     Wasu irin yawu ya haɗiye yana kallon Hassan wani murmushi ta sakeyi "tsoho ka faɗa musu komai kar ka bari na buɗe baki nace zanyi magana domin kasani gaba ɗaya bankaɗo ku zanyi."

   "Koma baki ce ba zanyi musu bayani dama wannan ranar nake ta gudu dama mai share hawaye ta gaya mana ƙarshen mu maza biyu mata biyu ne amma ɗaya ce mai ƙarfin ikon tuve kujerar Manga to tundaga lokacin maka shiga neman ku babu ji babu gani amma bama ganin komai sai duhu, da farko dai ni nasaka Umar dawowa ƙasar nan kuma ni na nema masa gida kusa da gidan Manga domin ta buƙaci haka dawowar sa da kwana biyu muka bijiro masa da buƙatar mu bayan mun gama duk wani sidabaru amma me ya rufe idanu yamana tas harda zagi hakan ya saka Manga taji haushi shine tace koda da bala'i saita mallake shi abinda ya mata katangar ƙarfe da shi shine Hassana da ta shiga cikin ku wannan dalilin ne ya saka muka bishi a hankali sai kuma gashi mai share hawaye ta bada umarni a kawo mata jinin sa domin kawai a sami saɓani tsakanin mu ya saka na tura wani yaro na mai suna Hassan wanki babban bargo domin ya shawo kan Mubeena ta aure shi ya koyi nasarar shawo kanta dan ya ƙware ta wannan fannin bayan haka ma ina baƙin ciki da yafini arziƙi ina ganin ai bai kamata a ce ya fini kuɗi ba harda wannan dalilin ya saka na tura shi Hassan wanki babban bargo da mai shagon nan Isa suka kashe shi, shi Nura munyi rigima da shi ne akan ina so ya auri yarinya ta amma ya rufe idanu yayi min tas wannan yasaka naji haushi na ce a haɗa dashi sannan su kwaso min ƙadarorin mahaifin ku."

     "To kuɗin da ka karɓa gurin mu fa sannan me Yaya Saif ya maka ka mantar damu shi shima ya manta damu?"

    "Mai share hawaye ce ta fito min tana gaya min cewa tabbas jinin Umar shi zai durƙusar dani saidai bata ga ko waye ba hakan ya saka na na katange shi daga gareku domin ina ganin shine mai hankali tunkarata ina ganin ka wawa baka san me kakeyi ba shiyasa ban kawo ka a sahun da zasu sani ciwon kai ba sai gashi wanda nayi tunani bashi bane."

    "Hmmmm Abba kenan  ni ba Wawa bane kamar yanda kowa ke ɗauka ko a lokacin ina aiki saidai kowa bai sani ba ina yima jami'an tsaro aiki ba tare da sanin kowa ba kasancewata nasan computer ciki da wajenta tun lokacin da kayi wannan rigima da faɗan na saka maka alamar tambaya na fara bibiyar ka karkayi mamaki nasan Isah yaron ku ne saidai Hajiya Manga ce ban sani ba kuma bandamu da nasanta ba tuni Isah ya daina yi muku aiki yanzu ni yakeyiwa yana ɗauko min bayanan ku yanzu haka kuna shirin yin gagarumin taro inda zaku baje kolin ku tare da tattaunawa dangane damu da muke muku ɗauki ɗai_ɗai."

    Daga haka ya miƙe ya fita rai a ɓace......

It's Rashma

KURMAN GIDAWhere stories live. Discover now