page 22

259 26 0
                                    

🏨KURMAN GIDA 🏨

        Na
Rashida Usman
     (Rashma)

________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w

_*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_

Page 22

بسم الله الرحمن الرحيم

       Tundaga bakin ƙofa yake kallon ta yana dariya a ransa kamar ba ita bace take rashin kunya da masifa ba "barka da isowa yallaɓai."

      "Yawwa barka. Ga wani case kije ki fara binciken akai."

    Buɗe file ɗin ta yi ta duba   sannan ta rufe ta juya tayi tafiyar ta da kallo ya bita har ta ɓace ma ganin sa ƙarfe huɗu suka tashi amma ba ita ta isa gida ba sai biyar  a gajiye ta shiga gida   soyayya da shaƙuwa suna ƙara ƙarfi tsakanin Hassana da Hayat  kwance ya ke ya ɗora laptop akan cinyar sa yana aiki ita kuma tana zaune a ƙasa ta miƙe ƙafafuwan ta da suke mata zugi   waigowa ta yi ta kalle shi gira ɗaya ya ɗage mata alamar ya dai murmushi ta yi ta ce "wai me kakeyi ne haka?"

   Hmmmm "bincike nakeyi dangane da wannan zanen da nake gaya miki shi kaɗai ne na riƙe hujja kuma na samu bayanai akan sa sosai saidai anɓoye muhimman to shine nayi musu zagon ƙasa yanzu komai ya bayyana naga komai wanda ya kashe min jigo na suna cikin wannan ƙungiya to yanzu ina so na fara da takan Isa mai shago."

    Kai ta gyaɗa tana cewa "gaskiya koni na saka ayar tambaya akan sa dan kaga ko ranar da zamu taho yana laɓe yana kallon mu dan har hoto saida ya mana ni nama ɗauka tsabar gulma ne."

    Murmushi ya yi yana rufe laptop ɗin "Maman ƴan biyu ya dai?"

Hararar wa ta masa tana cewa "waye Maman biyu ɗin?"

   "Ki gayawa wanda bai sani ba duk ɓoyon ki ya fito ai."

   "Kanka akeji ni banida wani ciki kawai ƙiba nayi shine nayi tumbi."

   Wata mahaukaciya dariya ya kwashe da ita, itama dariyar ta yi miƙewa ta yi tana cewa "kanka kuma akeji nikam nayi nan bacci nake ji."

   **** **** ****

   Kuka takeyi kamar ranta zai fita tana durƙushe riƙe da ƙanin ta Salman ga matar baban nasu tsaye akan ta sai Baba dake ta faɗa ta inda yake shiga ba tanan yake fita ba ɗago jajayen idanun ta tayi ta kalli Baba ta ce "wallahi Baba ko ina bana zuwa bare kuma naje ɗakin wani."

   Wani mari ya kwashe ta da shi saida ta faɗi "to kina nufin ƙarya zanyi miki kenan na shiga uku ni Ladingo lallai Salma wuyanki ya yi kauri barikin taki ta gawurta yanzu ni kike ƙaryata wa."

   Take kuwa Baba ya ƙara harzuƙa idanun sa sun rufe take ya rufe su da duka saida Ladingo taga lallai zai iya kashe su sannan ta janye shi tana bashi haƙuri Salman kam ya riga da ya suma cikin jan numfashi take jihiga amma ina ruwa ta zuba masa ta ke ya saki wani irin kuka mai ban tausayi rungume shi ta yi tana mai sakin kuka tana tuna rayuwar su ta baya mai cike da soyayya da ƙauna rumtse idanu ta yi tana me jin zugi da jikin ta ke mata ƙaninta, taɗauka ta shiga ɗakin su Baba ma fita ya yi sai huci yakeyi yana ji a ran sa kamar baiyi dai_dai ba Ladingo  na ganin ya fita ta laga mayafin ta tafita gidan su Fadila take suka sha firar su da Kakar Fadila kamar babu abinda ya faru saida Fadila ta dawo daga yawon gantalin ta sannan suka haɗu suka keɓe kamar ƙawaye "yawwa Ladingo yanzu kinyi rabin aikin ki ga dubu hamsin Alhaji ya ce abaki yanzu abinda ya rage shine zaki sa Baba ya kai Salma aikatau garin Lagos dan Alhaji a can yake to idan taje can zai nemeta da soyayya kinga hakan baza'a ga laifin ki ba saidai ma ace yawon banza takeyi."

KURMAN GIDAWhere stories live. Discover now