p 3

62 1 0
                                    

*WATA UNGUWA*
*(Labarin game da wata hargitsattsiyar unguwa mai cike da abubuwan al'ajabi)*

*ALƘALAMIN RUƘAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)*

*MARUBUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH*
*YAR GANTALI*
*RIKICIN MASOYA*
*RASHIN GATA (GAJEREN LABARI*
*HALITTAR ALLAH CE*
   
                      *AND NOW*
*WATA UNGUWA*

*AREWA WRITERS ASSOCIATION*

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

3 june 2021

Free p3

BABI NA UKU

Wani kyakkyawan saurayi ne durƙushe akan gwuiwoyinsa ya haɗe hannayensa biyu alamar roƙo ya na fuskantar wata 'yar kyakkyawar budurwa cakulet "Don girman Allah Mahee ki taimakawa rayuwata, ban zo nan don na yaudare ki ba,tsananin so da ƙaunarki ne suka mun jagora zuwa gurinki duk da kina wulaƙanta ni, na kasa barinki ki jure ki sama mun matsugunni a zuciyar ki komai ƙanƙantarsa in fake."

Wani mugun kallo ta bi shi da shi tare da jan wani siririn tsaki "Gaskiya wannan ganyen ka yada zuciyarka kare ya ɗauka, sau nawa zan gayama ka fita harkata, amma ka ƙi ji?"

"Ki dai ƙara haƙuri sahibar zuciyata ina matuƙar ƙaunarki ne shi ya sa..."

"Don Allah dakata malam!
Ta faɗa cikin tsawa tare da ɗaga masa hannu. "Irfan kake kowa? Ka saurare ni da kyau, don Allah ka fita harkata domin ina da wanda nake ƙauna, dukiyarka ba ita ce a gabana ba. Ni ba zaka iya siye ni ba kamar yanda ka siye mahaifana, don haka ka je Allah ya haɗa ka da rabon ka....."

Har ya bude baki zai sake cewa wani abu, ta ja wani uban tsaki ta wuce fuu abunta ta bar shi nan ɗurkushe a cikin zauren.
Duk da cewa yana tsananin ƙaunarta duk irin cin kashin da take masa baya damuwa amma wannan karon ya ji ciwon abun da ta masa sosai.
Miƙewa tsaye ya yi tare da juyawa ya bar soron gidan zuciyarsa ba daɗi. Tabbas da ba don Maheerah ba ce ko wace yarinya ce ta masa kwatankwacin haka zai bar ta barin mantuwa.
Amma abun mamakin shi ne ko kaɗan bai ji son da yake mata ya ragu a zuciyarsa ba. Hakika so makaho ne baya iya ganin matsugunnin da ya dace da shi, da ba don haka ba kyakkyawan saurayi kuma ɗan gata me zai yi da Maheerah 'yar talakawa?
Tafiya ya fara yi yana nufar inda ya faka motarsa domin mota bata iya shigowa layin na su, bai yi aune ba sai ji ya yi ya ci karo da mutum. A take ya ji ransa ya ƙara ɓaci.
Cikin hanzari ya ɗago kansa da niyyar ya sauke zafin akan koma waye.
Daidai lokacin ita ma ta ɗago kanta da nufin ta amayar masa da ruwan masifar dake cikinta sai dai me?
Suna haɗa ido ta yi saurin soke kanta ƙasa tana wasa da yatsun hannunta.
‘’ke wace irin jaka ce? Ko ke makauniya ce da zaki hada ƙazamin jikinki da ni’’ ya fada cikin daga murya yayin da yake binta da kallon tsana.
So take ta dago kanta ko don ta ƙare masa zagi, amma ko kaɗan zuciyarta ta kasa amincewa da wannan tunanin nata.
Ganin bata da niyyar magana kuma har yanzu bata kauce daga gabansa ba ya saka shi ratsawa ta gefenta ya wuce ya na faɗar "Ka da ki sake haɗuwarmu ta gaba ta kasance haka domin komai zai iya faruwa.’’
Bayan tafiyarsa Sofi  ta juyo baya tana kallonsa a ranta ta ce "Gaskiya kyakkyawa ne ajin farko, da yana masifar ma sai ya ƙara kyau.’’ Tana zuwa nan a zancen zucinta murmushi ya ƙwace mata.
Tsayawa ta yi tana kallonsa har ya shige motarsa ya bar gun, sai da ta daina hango motar sannan ta bar gun cike da nishadi.
A bangaren Irfan kuwa ko da ya je gida ya tarar da abokinsa Ma'eesh a ƙofar ɗakinsa yana jiran zuwansa.

Tun daga yanayin shigowar motarsa cikin gate ɗin Ma'eesh ya fahimci akwai damuwa tattare da abokin nasa, bare yanzu da ya ƙaraso suna gaisawa kallo ɗaya ya masa ya tabbatar da zargin da yake a kansa, Lallai ya na cikin damuwa sosai.
"Sannu da ƙarasowa matumina." Ma'eesh ya faɗa ya na kallon ƙwayar idon Irfan.

"Yawwa Abokina, yi haƙuri ka zo bana nan, wallahi na manta da na kira ka akan ka zo, shiyasa ban gayama ba da zan fita." Ya faɗa ba walwala.

"Ah! Badamuwa Mutumina ko dai an je gurin Sahibar ne?.." ya faɗa yana yar dariya.

WATA UNGUWADove le storie prendono vita. Scoprilo ora