p 9

28 1 0
                                    

*WATA UNGUWA*
*(Labarin game da wata hargitsattsiyar unguwa mai cike da abubuwan al'ajabi)*

*ALƘALAMIN RUƘAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)*

*AREWA WRITERS ASSOCIATION*

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

16- june 2021

Free p9

BABI NA TARA

Tsaye take a ƙofar banɗaki sai jijjiga ƙafa take tana kaɗa jiki da alama a matse take sosai amma tana jiran na ciki ya fito ne.
Can bayan kamar mintuna biyu ta fara magana kamar haka "Habah Iyan Hazze don Allah ka yi sauri ka huto in har ba burinka ka ga Marata ta yi bindiga ba ne."

Daga cikin banɗakin Iyan ta ƙyaro zance "Gaskiya kina da damuwa Jilde, yanzu uzurin nawa zan datse don kawai ki shigo?"

"Wannan dai siga hakki ne ko hanzin cikinka za ka kasayar ya ci ace ka gama, wallahi nan da minti ɗaya in baka fito ba sigowa zan yi." Jilde ta faɗa a kufule, cikin hausarta irin ta su ta Fulani.

Cikin gatse Iyan Hajje ta ce "Don Allah shigo abinki, ai dukkanmu mata ne kowa bisa ga uzurinsa."

Abinda Iyan bata sani ba Jilde bafulatana bata san gatse ba, ga shi a matse take kawai sai faɗawa ta yi ciki faram-faram ta yi uzurin da ya kaita, ba tare da ta kalli sashen da Iyan take ba. Kusan a tare suka fito, Iya na ta mamakin Jilde duk shekarunta ace bata san gatse ba?

Ko da yake a zahiri ba wai ta damu da yanda Jilden ta tarar da ita ciki ba ne, domin ita a nata ƙaramin tunanin hakan ba komai ba ne tun da yake dukkansu mata ne, kuma ma abu ga gidan haya shi ya sa bata yi mata magana ba.

Tana fitowa ta nufi ƙofar ɗakinta inda ta kasa sana'arta ta kayan miya, yara maza biyu da mace ɗaya ta tarar suna jiranta a gun tana ƙarasowa ɗayan yaron ya ce "Iya a bani tumatur da salak na Hamsin."

Bata tamka shi ba, ta ɗaga hannu tare da zaro wata cukurkuddar leda a saman rufin rumfar ta saka masa kayan a ciki sannan ta miƙa masa.

Ɗayan yaron ma haka ta sallame shi har a lokacin 'yar macen nan bata ce komai ba.

"Sarauniyar miskilanci me za'a baki?" Iya ta tambaya.

Da ƙyar ta yi magana kamar mai ciwon baki "Attarugu da yakuwa, sai albasa da Kabewa duka na ɗari."

Karɓar kuɗin ta yi ta saka mata sannan ta bar gidan, ita kuwa Iya ta nufi ɗakinta tana faɗar "Ke! ke!! Hafsa, ban ce ki je gidan Baba mai ice ki siyo mun kai ɗaya ba ne? Me kike jira ga shi an kusa Azahar ba mu ɗora komai ba."

Hafsar ta fito tana zumbura baki alamar bata son aiken, dai-dai ƙofar fita ta ci karo da 'yar Garbe kanuri shi ma mazaunin gidan Hayar ne, bata yi wata-wata ba ta mintsini yarinyar ta fita da gudu tana dariya. A wajen ma kafin ta yi nisa ta tarar da wata yarinya zata je markaɗe ta saka hannu ta ture robar ta zuba a guje tana dariya.

Nan ta bar yarinyar na kuka tana faɗar "Allah zai saka mun, kuma wallahi sai ma na je innarku ta biya ni, ba dai kuna siyar da kayan miya ba?."

Daga can cikin gidan kuwa Fa'ee ce ta kammala wankinta, ta zo zata yi shanya ta tarar da kayan Shamsiyya akan igiyar, bata cewa kowa ƙala ba, ta saka hannu ta ture tufafin Shamsiyyar a gefe alhali tana sane da cewa basu bushe ba, kawai ta hau shanya nata tana hura hanci irin ga isasshiyar nan.

Fitowar Shamsiyya daga ɗaki kenan idonta ya faɗa kan wannan ɗanyen aikin da Fa'ee ke mata.

Ba bata lokaci ta yi kukan Kura tana zuwa ta saka hannu ta janyo kayan Fa'ee ta watsar da su a tsakiyar gidan.

WATA UNGUWAWhere stories live. Discover now