p 12

30 1 0
                                    

*WATA UNGUWA*
*(Labarin game da wata hargitsattsiyar unguwa mai cike da abubuwan al'ajabi)*

*ALƘALAMIN RUƘAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)*

*AREWA WRITERS ASSOCIATION*

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*


26 june 2021

Free page 12

BABI NA SHA BIYU

"Zubairu me kake shirin aikatawa ne?" Ta faɗa muryarta na rawa.

Saurin sauke yarinyar ya yi daga cinyarsa ya miƙe yana 'yan kame-kame.

"Me kika gani ne? Kuka fa na tarar tana yi shi ne nake rarrashinta" ya faɗa.

"Ka dai ji tsoron Allah, ka sani duk abun da kake aikatawa Allah na ganinka domin Ubangiji baya barci balle gyangyaɗi." Ta faɗa yayin da take binsa da kallon tuhuma.

Ɗaga kafaɗarsa ya yi irin ko ajikinsa ɗin nan ya zo zai wuce ta yana Faɗar "Dama wani kyakkyawan albishir na zo gaya miki amma kin ɓata rawarki da tsalle, tunda ki ke zargina, ni na yi gaba."

Har ta buɗe baki da nufin ta dakatar da shi, sai dai kafin ta kai ga motsa harshenta ya fice daga gidan.

Tana ganin haka kawai sai ta ƙarasa cikin ɗakin inda ta tarar da Salma tana sauke ajiyar zuciya alamar ta sha kuka, fuskar nan duk ta yi jirwayen hawaye.

Kallon Salma ta yi ta ce "Ke kuma menene? Kin san Allah Salma idan baki daina koke-koken munafurcin nan da kika tsira kwanan nan ba ni da ke ne. Wannan da 'yar kishiya ce ke ai sai ki saka a zargi ko ina zaluntarki ne."

Shiru yarinyar ta yi bata ce komai ba, sai ci gaba da sauke ajiyar zuciya da take.

Fizgo hannun yarinyar ta yi da ɗan ƙarfi "Ni don Allah taso na miki wanka duk da dai shekaranjiya na miki wanka, amma ko don tsoron masifar fitinannen mahaifinki dole na kuma miki wani yanzu."

Tsakar gidan ta fita da ita ta mata wanka tana tsaka da shirya yarinyar ne ta tuno da bikin ƙanwar ƙawarta da ta gayyaceta ga shi kuwa ta manta bata sanar da Habibu ba, amma ta kudurce a ranta sai ta je, in ya so in ya dawo gida sai ta gaya masa ta fita.

Cikin gaggawa ta ci gaba da gudanar da aikinta, yau kam sai da ta share ko ina tsaf, ta yi lafiyayyen girki ta saka a kula ta ajiye masa a falo, wai ko da zai dawo ya tarar bata nan.

Ɗibar abincin ta yi itama ta ci sannan ta sanyawa Salma nata tana ci, a uzurce ta shige banɗaki ta yo wanka mai kyau, wanda marabin  ta da yin kyakkyawan wanka tun bikin Basira da yake shi ne biki na ƙarshe da ta fita sai kuma yau da ta ke shirin fita. Sauran ranakun da take gida kam ko ta yi wankan asarar sabulu da ruwa ne kawai, don jiƙa datti kawai take.

Bayan ta fito ta buɗe lokar kayanta, ta zaɓo na can ƙasa.
Wani lace ne dark purple mai masifar kyau, da ganinsa kasan zai yi tsada ko da ba sosai ba.

Zaunawa ta yi ta tsantsara kwalliya irin wacce take yi Lokacin tana budurwa, ta saka lace ɗin nan sannan ta kashe ɗauri.
Abu ga farar fata sai ta fito cas abunta kamar ka sace ta ka gudu.
Wanda bai mata farin sani ba idan ya ganta a ranar zai iya rantse cewa ba Biba ƙazamar da ya sani ba ce.

Mayafinta ta yafa sannan ta saka turare sama-sama, ta fito tare da kulle ƙofar ɗakin.

Hannun Salma ta ja suka wuce bayan ta kulle gidan da maƙulli.

Salma ta kalle ta cikin alamar mamaki ta ce "Mama ina zamu? na ga yau kin yi kwalliya."

Murmushi ta jefi yarinyar da shi ta ce gurin biki za ni Salma.

WATA UNGUWAWhere stories live. Discover now