p 11

29 1 0
                                    

*WATA UNGUWA*
*(Labarin game da wata hargitsattsiyar unguwa mai cike da abubuwan al'ajabi)*

*ALƘALAMIN RUƘAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)*

*AREWA WRITERS ASSOCIATION*

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*



22 june 2021

Free page 11

BABI NA SHA ƊAYA

Kafin Inna ta shigo ɗakin tuni ya fara tsula masu mulalar ba ji ba gani.

Nan fa suka gigice suka sake mannewa guri ɗaya tare da kankame juna ƙam, sai ihu suke don azabar raɗaɗi.

Ko da yake abun ne ya masu yawa wai shege da hauka, ga zafin raɗaɗin ciwon jikinsu ga kuma raɗaɗin bulala da yake tsula masu.

Shi kuwa ko kaɗan bai damu da duk wannan iface-ifacen da suke ba, Babban burinsa shi ne ya ga ya raunata su, bayan raunin da yake jikinsu. Sai kumfar baki ya ke "Ba ku ga 'yan iska tijararru ba? Yau zaku ga ƙarshen ƙaryar karuwanci da iskanci, wato ku ga 'yan tasha fanɗararru. Waya sani ma ko kun fara yan kurɓe-kurɓen nan na zamani?"

Ya daga bulalar zai sake tsula masu kenan, Inna ta shiga tsakaninsu tana ƙoƙarin dakatar da shi, bisa tsautsayi bulalar ta sauka kan gefen fuskarta, wutsiyar  bulalar ta tsokane mata ido. A take ido ya shiga ratatar ruwa.

"Waah! Shi ke nan Malam ka kashe ni, dama can idon ya yake bare yanzu?" Inna ta faɗa cikin raɗaɗin ciwo.

Ihun da Innar ta saka ne ya dawo masa da hankalinsa a muhallinsa, nan fa ya yada bulalar icen yana faman tambaya "Miye ne haka kuma Luba? Ya kike mana ihu kamar ƙaramar yarinya?"

"Malam baka ga yanda ka shauɗa mun bulala a fuska ba? Har fa cikin idona." Ta faɗa da alamun har yanzu tana cikin zafin ciwon.

"Ai duk laifinki ne, me ya shigo dake cikin faɗan nan saboda Allah? Ko da yake tun can azal haka kike da shiga sharo ba shanu, dama kuma ke ki ke ɗaure masu ƙugu shi ya sa suka rainani da yawa, yara duk sun zama fitsararru, da ai ba haka suke ba." Ya faɗa yana huci.

A maimakon ya tsaya duba idon nata ko kuma halin da yaran suke ciki kawai sai cewa ya yi "Allah ya sawwaƙa Luba." Daga haka ya kaɗa bujensa ya yi waje yana jin zafin yanda Luba ta shiga tsakaninsa da burinsa na lallasa yaran, ko zasu gane cewar shayi ma ruwa ne kala ce ta bambanta su.

WAIWAYE

ASALINSU.

Malam mudi ɗa ne ga Alhaji Usman mijinyawa wanda ya kasance haifaffen unguwar Garwa ne.
Mahaifinsa ya kasance mai rufin asiri sosai a zamaninsa domin shi bafatake ne, fatauci ne sana'arsa yana yawo gari-gari don kai hajarsa idan ya siyar sai ya siyo ta su ya dawo gida ya siyar.

A garin yawon fataucinsa wata rana ya isa wani ƙauye mai nisa a cikin wata jiha mai suna Sambusa, a can ya auro wata budurwa mai suna Mari, bayan lokacin tashinsa daga garin ya zo ya je ya shaidawa iyayenta akan zai wuce da matarsa can garinsu MAMBIYA.

Sai da aka kai ruwa rana kafin iyayenta suka amince ya taho da ita. Ita ce Allah ya azurta da haifar ƴaƴa maza guda Biyar mata uku.

Shehu shi ne Babba sai Iliya, Mariya wacce suke kira yaya Kande sai shi Muddasiru da suke kira Mudi Ali(Baba ƙarami) sai kuma Dije Sannan Ummaru(ɗan lami) sannan Auta A'i.

Gidan Alhaji Mijinyawa gida ne na jama'a gida ne da aka inganta gininsa cike da soyayya da ƙaunar juna, yaransa sun taso da haɗin kai fiye da zaton mai zato.

Hakan nan da baƙo da na gida kowa nasa ne, ko da yake yawon fataucinsa ba ya bari ya share tsawon lokaci tare da iyalinsa, amma hakan bai saka yaransa sun taso cikin wani mummunan yanayi mai kama da yunwa ko ƙishi ba.

WATA UNGUWAWhere stories live. Discover now