p 14

27 0 0
                                    

*WATA UNGUWA*
*(Labarin game da wata hargitsattsiyar unguwa mai cike da abubuwan al'ajabi)*

*ALƘALAMIN RUƘAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)*

*AREWA WRITERS ASSOCIATION*

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*


12 July 2021

Free page 14

BABI NA SHA HUƊU

Da wannan tunanin Fa'ee ta rarumo wani guntun ice wanda ake kira bakin wuta, ta yi kan Atika.
Sai da ta ware iya ƙarfinta ta laftawa Atikar shi a gadon baya.
Sai dai da alama matar bata ma san tana yi ba don ji ta yi tamkar susa ce Fa'een ta mata.

Lura da hakan ya ƙara tunzura budurwar ta juya baya da sauri tana waige-waige, can idonta ya yi tozali da wani madai-daicin dutse.

Cikin azama ta nufi gun tare da sanya duka ƙarfinta ta tallabi dutsen ta nufi gurin da Atika ke zaune kan ruwan cikin Mamanta.

Ba tare da tunanin komai ba, ta ɗaga shi tare da kwabɗawa Atika shi a tsakar ka da iya ƙarfinta.

"Ah wayyo! Wayyo Allah!" Atika ta saki wata irin razananniyar ƙara.
A gigice ta saki wuyan Maman Fa'ee da take damƙe da shi ta saka hannun akai ta shafa.

A razane ta dawo da hannun saitin fuskarta tana kallon jinin da ta shafo daga kanta, lokaci ɗaya kuma tana jin raɗaɗin raunin dake kan nata.
Lokaci ɗaya ta dakatar da mamakin da take, ta gayyato mummunan ƙuduri zuwa zuciyarta.

Cikin baƙin nufi ta nufi Fa'ee ta janyo ta ta haɗa su guri ɗaya da Mamanta da ta yi nasarar miƙewa daƙyar, ta gwara kansu guri ɗaya.

Dukkanninsu suka saka ƙara a tare, a dai-dai lokacin da ita ma Atikan jiri ya fara ɗibarta, kasancewar sosai kanta ya fashe sai ambaliyar jini yake.

Bata da zabin da ya wuce ta ta sake su, tare da komawa gefe ta faɗi zaune rikicaa.

Ganin hakan ya saka a rikice tsamurarren mijinta ya je ya tallafo ta suka nufi waje.

Sauƙinta ma gidan nasu kusa da titi ne sosai, duk da sun shiga lungu, hakan yasa ba su sha wahala ba gurin samun Napep.
A nan suka nufi asibiti mafi kusa.

"Allah ya miki albarka Fa'ee! Duk da dai ban so kin saka kanki a wannan rigimar ba." Maman Fa'ee ta faɗa tana kallon 'yar tata.

Murmushin ƙarfin hali Fa'ee ta yi ta ce "kada ki damu Mamana, ni ai bana tsoron rigima komai girmanta. Ba ma yanda za'ayi na zuba ido ina kallo a cutar mun dake."

Ta ji daɗin kalaman 'yar tata sosai don haka ta kuma saka mata albarka tare da janta suka wuce ɗaki don su huce gajiyar da Atika ta tara masu.

Sai a lokacin ne kuma 'yan kallon faɗan suka watse, kowa ya ci gaba da sabgar gabansa. Shamsiyya da Sakina da ta shigo gidan ɗazu don siyen Abinci da Matar Garbe Kanuri ke siyarwa, ta tarar ana rigimar ta tsaya kallo suka ci gaba da tofa albarkacin bakinsu.

Shamsiyya ta kalli Sakina ta ce "Uhmm! Ke ai mu a gidan nan muna shan kallo, kuma mun tara kalolin mutane harda bara gurbi. Ko da yake renon marasa tarbiyya ai ba za a tsammaci ya yi ladabi ba balle kuma biyayya ga na gaba."

"Hmm! Ke dai bari Shamsiyya na so ace nan gidan nake, da kullum zan samu sababbin rahoto a bati ba sai na nemo ba. Allah ya shirya inda rabon shiryuwar, amma kam Allah ya wadaran reno irin wannan." Ta faɗa cikin yanayi na taya ƙawarta neman rigima.

Duk abubuwan da suke faɗa a kan kunnen Fa'ee, domin a saitin ƙofarsu Fa'een suke zaune.

Sai dai a karon farko ta yi masu damo kamar bata ji ba.

WATA UNGUWAWhere stories live. Discover now