P 10

31 2 0
                                    

WATA UNGUWA*
*(Labarin game da wata hargitsattsiyar unguwa mai cike da abubuwan al'ajabi)*

*ALƘALAMIN RUƘAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)*

*AREWA WRITERS ASSOCIATION*

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*


17 June 2021

Free page 10

BABI NA GOMA

Tun kan su ƙarasa Dagarman ta ɗaga waya ta kira gayenta, sai dai yau ma kamar kullum bai ɗaga ba.
A gaggauce ta tura masa saƙo kamar haka "Masoyi ina hanya gani nan zuwa, na kasa juran rashinka a kusa da ni."

Lokacin da sakon ya shiga wayar Ja'afar yana gidan iyayensa dake unguwar Bashal. Hannunsa ɗaya na riƙe da bokitin roba Babba, ya ɗebo ruwa daga famfon unguwar.

Ya zo dai-dai ƙofar gidansu kenan sakon ya shigo, cikin hanzari ya ɗauko wayarsa don ganin ko saƙon da yake ta dakon jira ne.

"Ai kuwa shi ne." Ya faɗa tare da saka ihu kaɗan ya ce "Yes! Yau akwai shagali kenan bari in yi sauri."

Tun kafin ya shiga gidan ya kira Abokinsa Duddoo da suke hayar ɗakin a tare ya ce "Don Allah guy gyara mana ɗaki, ka saka turare gani nan zuwa yanzu."

Ta samu ke nan?" Cewar Duddoo

Yar dariya ya yi sannan ya ce "Kawai ka gyara mun Babyna na hanya so nake na riga ta ƙarasowa."

"Ba dai Mahee ba." cewar Duddoo cikin mamaki.

Dariya sosai Ja'afar ya yi ya ce "An gaya ma ni wasa ne? Ai kai dai yau akwai part........"

Kasa karasa zancen ya yi don ganin tahowar Abbansa daga wajen.

Da sauri ya datse wayar tare da ɗurkusawa "Abba ina wuni?."

"Lafiya lau Jafaru, ruwa ka debowa Umman taka ne?" Ya Amsa da murmushi a fuskarsa.

A kullum yana ƙara godiya ga Allah da ya azurta shi da ɗa mai hankali da nutsuwa, wanda kullum ba ya da burinda ya wuce ya faranta masu rai.

"Eh Abba." Ya faɗa a taƙaice sannan ya ɗauki bokitin ya shige ciki a hanzarce.

"Wai har ka dawo ne Jafaru?" Cewar mahaifiyarsa dake zaune tsakar gidan ta ga shigowarsa.

"Eh Umma na dawo." Ya faɗa yayin da yake zuba ruwan a bokitin wanka.

"Ya kuma na ga kana juye ruwan ne, ba ni ka samowa ba?" Ta faɗa da mamaki.

Murmushin da ya auri fuskarsa muddin yana cikin gidan ya yi sannan ya ce "Wannan Sawu na biyar kenan na ɗebo, to uzurin fita ne ya kama ni da gaggawa shi ne na ke son ki sammun na yi wanka in ba damuwa Ranki ya daɗe."

Yar dariya ta yi "To to to, na gane jeka abinka Allah ya ma Albarka."

Ya amsa da Amin sannan ya shige banɗaki a gaggauce ya yi wanka, tare da canza kaya ya fice daga gidan.

Ita kuwa Mahee ko da ta ƙaraso dai-dai adireshin da ya bata sai ta ja ta yi turus, tana ƙarewa gidan kallo.

Kafin ta gama tantance ko adireshin da ta zo dai-dai ne, ta ga wani matashi ya fito daga gidan ya na shan taba sigari yayin da wasu saurayi da budurwa suka zo suka shige hannunsu na sarƙe da juna.

Shanye mamakin da ya zo mata ta yi tare da ɗauko wayarta ta kuma kiran Ja'afar, sai dai wannan karon ma bai ɗaga ba. Hakan yasa ta shiga zullumi da tashin hankali fiye da farko.

'Tabbas fushin da Ja'afar yake da Ni ya yi tsanani tun da har na zo ya kasa ɗaga kirana.' ta faɗa a ranta.

Tana nan tsaye tana tufka da warwara, ta saƙa wancan zaren ta kunce wannan. Sai ga kiransa ya shigo wayar, sosai ta yi mamaki ta so ta ja aji sai dai a wannan karon ba zata iya ba, domin ba ita kaɗai ba hatta wayarta ta yi kewar kiran Ja'afar. Bata san lokacin da ta kai hannu ta danna malatsin karɓar wayar ba.

WATA UNGUWAWhere stories live. Discover now