JINGA

266 33 7
                                    

JINI YA TSAGA....👭

  ®NWA

©OUM-NASS

  Ina ta son yin magana, ina ta son na yi na gama labarin nan saboda ɗaukar lokacin da ya yi jibge a kaina da kuma jinginar da mutane masu yawa da suke dakon son ganin ƙarshen labarin. Sai dai hakan ya kasa daga gareni. Har na ke tuhumar kaina a kan anya kuwa ba wani abin aka min ba?

Bayan dogon lokaci da kyakkyawan nazari akan neman silar da zan ƙarƙare labarin, sai na gano ashe masu *CI DA GUMIN WASU* ne suka yi ƙaba-ƙaba a tafiyar labarin.
  Tsawon watanni takwas wata ta ɗauki labarin JINI YA TSAGA.. ta ɗora min a Youtube channel ɗinta mai suna *MAMAN KHAIRAT TV*.

Abin sai ya min banbarakwai, kasancewar sanin akwai hakkin mallaka da neman izini ga mamallakin duk wani rubutu.
  Amma ita bata yi hakan ba, dan haka  a ce ta cire min littafina a channel ɗinta, idan bata yi hakan  ba komi zan iya yi marar daɗi wanda na zai yiwa kowa daɗi ba, idan ya kama harsa shari'a.

   Sannan na ajiye rubutun JINI YA TSAGA ɗin gaba ɗaya.. Idan akwai yiyuwar ci gabansa, zan yi tunani akai. Wata ƙila na mayar da shi na kuɗi idan akwai yiyuwar ci gabansa.

Na gode da samun goyon bayan karanta labarina....

Girmamawa.

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Jun 28, 2021 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

JINI YA TSAGAWhere stories live. Discover now